← Book details Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 145

Sashe 56

Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shima Muheed da yaga yanayin kowacce na bazatan da akai musu surprise a fuskansu kamar ba abinda ya kawo su Kenan ba yace.

"Ah da alama muje kawai Asad".

Muheed na rufe baki suka juya cikin taku suna fita a gurin sauke numfashi Yusairat tai tana kallon Clarah tace.

"Tofa lambar mu ta fito tunda nazo ban ta'ba shiga daji da sunan fad'a ba sai yau dole na dage nayi fito na fito da ma'kiyi muje shiri ko" Yusairat na shirin barin gurin Clarah ta dakatar da ita da cewa.

"Amma Yusairat bakiji me Muheed yace ba kenan muma muje mu tunkaresu wanda kwanan sa ya 'kare ya mutu? Tab gaskiya I can't kawai kizo muyi wani gurin bayan tafiyar su ma dawo" ta fad'a tana jan hannun yusairat "taho karki damu nasan mafaka da yawa guraren da zamu kafin su dawo" ta karasa maganar tana janta jin ta'ki biyota yasata kallon ta zatai magana Yusairat ta katse ta.

"Clarah bakiji kunya ba da kika ce muje mu boya? Tome akai kenan wacce asara ce zamu nuna munji tsoro mun gudu ba muna matsayin sojoji masu baiwa 'kasa kariya to inaga mutanen gari suyi yaya da ransu? Kinga Clarah nifa aikina nazoyi ba shirme da kula-kulen samari ba ke kuma naga kamar kin baiwa hakan muhimmanci maganar gaskiya tafiyar mu bazata zo d'aya ba dan haka sai anjima" wucewa Yusairat tai yayin da Clarah ta bita da kallo tana jin takaicin maganar data fad'a mata tsaki taja itama tana barin gurin taje ta shirya amma data fito ma bata ga ko 'kwaro ba domin jirgi🛫🛩️ ya tashi cizon yatsa tai "oh wato Yusairat ni zatai wa haka? Humm inda rai gaba tafi baya yawa" juyawa tai sukai ido hud'u da Asad yana tsaye taji mamaki sosai to meya tsaya yi har suka tafi ko shima ya fasa................muryarsa ce ta katse mata tunani.

"Meye kike kallo na"?.

Baki bud'e ta sake dubansa tana cewa "ya akai na ganka anan bayan kowa ya tafi ko kaima baza kaje ba"?.

Kallonta yayi yana jinjina kai "hum wannan yarinyar is so funny 🤨 da alama taci kai shine zai fasa fuskantar enamies saboda tsoro bai kula taba yana dai inda yake taga Muheed da Yusairat sun fito da sauran wasu sojojin kowa yayi shirin no going back 💣⚔️🔫🔫🔫🙅 babu wanda ya damu da tsaiwarta suna wucewa da sauri ta bisu tana cewa.

"Amma a 'kasa zamu tafi"?.

"Miye damuwarki? Ina tunanin ko da jan gwiwa aka umarce mu zamuje right"? Harara Clarah ta zafgawa Yusairat jin tana neman 'kas'kantar da ita tace "ke kuma ba dake nake ba uwar 'yan shishshigi😠" ta'be baki Yusairat tai bata sake magana ba har sukai nisa sosai suka bar wajen birni sannan suka dakata a gaban wani 'katon jirgin ya'ki dukkan su shiga sukai ba wani jira jirgi yayi sama haka suka shiga wannan ba'kin dajin baka jin komai sai 'karar harbi da bullet abin mamakin baka ganin masu harbin saidai kawai kaga wuta na tashi da 'karar fashewar bom💣 gabadaya haya'ki ya turnu'ke dajin yayi duhu jirgin su na sauka suka fara fiffitowa kamar anyi busa haka sukaga ana jefo musu gawarwaki sun rasa ta ina ne yafi mutum hamsin suna kwance babu mai rai innalillahi wacce irin masifa ce wannan waye yake kashe-kashe a dajin meye dalilin sa kallon Asad daya zuba musu ido suna kwance Muheed yayi yana cewa.

"Buddy wanne irin abu ne wannan wai meke faruwa ne a cikin dajin nan"?.

Kai Asad ya girgiza "I don't know Muheed nima abin yafi 'karfin tunani na".

"To yanzu me zamuyi zamu koma dasu ne ko kawai mu karasa shiga dajin muma"? Jay na rufe baki aka kiransa a irin wayar da sojoji suke amfani da ita akwai Bluetooth a kunnen sa cikin tashi hankali yaji Mayesh na magana da'kyar.

"Jayesh kana ina yanzu"?.

Jin muryarsa a wahale yasa Muheed cewa "kana lafiya Mayesh Boun akwai abinda yake faruwa a yankin ku ne ina aka kai ku"?

Mayesh dake tsaye juyawa yai yana kallon yadda sojojin su suke zuba kamar ana kad'ar ganyen bishiya yace "hello Jay kana jina muna Singapore a wani irin ba'kin daji ni ban ta'ba ganin tashin hankali irin wannan ba Jay baka ganin kowa amma harbi kamar saukar ruwan sama fa".

Sauke numfashi Muheed yai yana cewa "nan ma haka muke kaga gawa nan a gabana takai guda hamsim, to Mayesh abin tambayar anan shine waye mai wannan ta'asar nasan ba iya abokan gaba bane akwai lauje cikin nad'i".

"Tabbas Jay lallai ya kamata ku koma gida a sake sabon shiri domin kawo 'karshen ko ma waye yake mana asarar rayukan sojojin mu".

"ok Mayesh karka damu bari naga abinda zan iya yi ka kula da kanka" yana fad'in haka ya sauke waya yana kallon Asad yace.

"Asad a acan Singapore d'in ma abinda daya faru kenan kamar nan na gaza ganewa yanzu saidai mu koma da baya muyi magana da sir murtih Jonah da general Jalalunddeen gaskiya akwai matsala ba 'karama ba, kamar wanda bakinsu a had'e yake"?.

"Ok mu koma da bayan da ace munyi abu da ka tunda muna da shugabanni".

Yana rufe baki Clarah ta sauke wani daddad'an numfashi cike da jin dad'i domin a da hankalin ta yai matukar tashi cikinta ya kad'u ganin mutanen da suka rasa rayuwar su harta fidda ran sake komawa cikin Marshall islands balle 'kasarta sai yanzu badan ta kamu da ciwon son Asad ba babu abinda zai hana suna komawa ta tattara kayanta ta gudu inda tafi wayo Asad yana lure da ita shikam wannan girl din tana bashi mamaki bazai iya jurar ganin shashancin da take ba matukar aka cigaba da zama a haka baisan kalar matakin dazai dauka ba.

Sunan nan tsaye jirage guda biyu suka sauka d'ayan aka sanya gawarwakin a ciki dayan kuma suka shiga suna barin dajin basu dakata ba da sabon shirin su sukai meeting da manyan shugabanninsu domin su kawo musu ta yadda za'ai su ya'ki wadannan ma'kiyan nasu da suke kokarin ganin bayansu bincike mai tsananin gaske general Jalalunddeen da murtih tare da wadansu hazi'kai masana na'ura suka hau bincike dason gano meye abinda yake 'boye sun shafe tsahon shekaru hud'u da rabi kafin rana daya kamar wal'kiya haka sukaga abun tashin hankali da mamaki wato dai bama ma'kiyan da suke zargi bane wata kalar 'kungiya ce 'boyayyiya suke aikata wannan baka'ken munanan masifun a 'boye suna hallaka al-umma kullum yafi mutum dubu innalillahi abunda suka kasa ganewa dajin na tsafi ne ba damar shigarsa saidai in matsafan ne sukaga dama ka ganshi akwai had'ari basu san ta inda zasu fara ba saidai dole suyi wani abu akai domin datakar dasu dole a samar da wata hanya tsohon shugaba brigadier general safras ya riga ya tsofa zance retire yake kullum zasuyi amfani da wannan damar wajen sanyan gwarazan sojojinsu su dage su 'kara himma su bazu suyi bincike an basu dama su gano asalin wannan 'kazamar azababbiyar 'kungiyar akwai babbar kyauta da girmamawa mai yawa ga wanda yayi nasara zai kasance shine Bgs na gaba tare da taimakon had'in kan 'kungiyoyin duniya na kowacce 'kasa babu gudu babu jada baya dukkan manya manyan shuwagabanin 'kasashe daban dabam sun taro a guri d'aya sunyi meeting domin warware matsalar sun fahimci juna sun kuma amince kowa ya bada sojoji masu matukar yawa daga yankin 'kasarsa sunyi fad'a sunyi ya'ke-ya'ke na al'ajabi da tashin hankali amma maimakon a samu sauki abin sai gaba yake 'karayi babu sauki ta hakan mutane da yawa sun rasa ransu.

Ana haka 'kwatsam wannan had'ararriyar shahararriyar matsafiyar ta bayyana musu kowa ya ganta a sarari ta razanasu da kalamanta masu dafi da zafi kamar wuta ta girgiza su ta wahalar dasu kafin daga baya sukai nasara a kanta suka kashe ta mud'us har lahira saidai sunbar baya da 'kura domin ta mutu ne bata mutu ba saboda ta baiwa Prof Jibril da Famous da kuma Danual chai dukkan wani logo da shihirinta bata rage komai ba saida ta koyar dasu zalunci da tsaface tsaface ta gama gur'bata komai tasan tayi nasara ta dulmiyar da mutane cikin baud'dd'iyar hanya kafin ta bayyana tayi fito na fito dasu har sukai nasarar kasheta.

Lokacin da labari ya karad'e ko'ina an cika da farin ciki an yabawa sojojin da sukai wannan aikin wanda a cikinsu harda Asad da Muheed da kuma Isham suna cikin fitattu kuma sanannu 'kwararru jarumtattu an sake za'barsu duba da cewa zasu iya ji da komai aka rabasu zuwa sashi biyu Asad yana 'bangaren wadanda zasu nemo wannan 'kungiyar da mafarinta da kuma wadanda suka kafata a sanadin haka domin kawo 'karshen ta duk wanda yayi nasara tofa zai samu babban matsayi matakin girma na 'karshe a mu'kamin soja sun sake sabon shiri sun lumu cikin 'bangarori na yankin duniya domin aiwatar da haka anan ma sojoji da yawa sun 'bata ciki harda Muheed😥😢 Asad ya shiga tsananin tashin hankali mara misaltuwa yayi ba'kin ciki har bazai kwatantu ba dole haka ya dangana amma yayi sanyi sosai rashin Muheed ba karamin ciwo da d'aci ya haifar masa ba yana iyayin kwana biyu/uku baiyi magana da kowa ba sai Yusairat ce take kula dashi na wani lokaci har ya samu ya warware tun baya sakewa yazo abun ya zame masa jiki haka rayuwa ta mi'ka lokaci mai tsawo.

Kasancewar akwai tsaro mai girma a masarautar mai martaba Alhassan yasa iya samarin ke fita zuwa inda ya kamata suje amma 'ya'yan Alhussain su Shaukiyyah babu inda suke zuwa daga makaranta sai gida kullum suna tsare ata hakane Khimiyyah tayi friend a school nasu sunanta Hudayyah 'yar gidan Prof Jibril ce ta shahara a 'kungiyar ya sanar da ita manyan sirrika tuni ta zama teruwa mai firgitarwa wanda tayi amfani da wannan damar ta koyar da Khimiyyah wasu abubuwa ta nutsar da ita tayi zurfi a ciki, a wannan lokacin sultana Hadizah mahaifiyarsu Khimiyyah ta haifi yara guda biyu cikin rashin tausayi Khimiyyah ta bayar da jininsu rana guda suka mutu a cikin wadannan shekarun sau d'aya Asad yaje gida daga haka bai sake zuwa ba suna tare dasu Isham suna bincike.
Chapter 56 · 0% Book details