Sashe 141
Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Suna kwance abinsu yana daddannawa Amatu bayanta da tace yana mata ciwo😂🤩 zuwa 'kugunta jin ana buga kofa ya suka d'ago a tare suna kallon kofar kafin suka kalli juna shagwa'be fuska Amatu tai tana cewa "ka gani ko" gira ya d'auke "naga me"? Cigaba tai "gashi ana kwankwasa kofa ko sune suka zo" "to miye idan su dinne tashi muyi wanka idan muka shirya basai mu fita ba" zaro ido Amatu tai tana cewa "wanka kuma? Allah zasu gane ka bari sai sun tafi".
"Tab nayi ta zaune da janaba a jikina? A'a wallahi wanka na zanyi wanda bazai iya gani ba ya rufe idonsa 🙈" Amatu zatai magana aka sake kwankwasawa a gigice ta yayimi towel ta d'aura Asad na kallon ta da murmushi a fuskarsa baice mata komai ba tasa hijab da sauri ta fita shikam mi'kewa yai ya shige toilet saida yayi wankansa ya shirya tsaf cikin 'kananun kaya masu kyau 3Quarter da rigar shan iska ko drying kansa baiyi ba ya fita.
Amatu na zaune dama duk kunya ta baibayeta gani take kamar sun san me sukayi kuma saiga uban gayya ya fito zaro ido tai kamar zata fasa ihu take kallonsa murmushin mugunta yayi yana d'auke kai yayin da Amatu tai suman zaune ganin yadda gashin kansa yake ji'ke da girarsa ga gashin idonsa ma babu inda ya goge ruwan duk gashin jikinsa ma yabi ya kwanta innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ta fad'a a ranta cikin kunya tai 'kasa dakai ta kasa motsin kirki sai kakkare jiki take kar suga towel ne a jikinta.
Da nuna farin cikin dake zuciyarsa na ganinsu ya zauna yana gaidasu kallon zarah dake ta faman 'boya yai sai no'kewa a bayan ma'asumah take kuma yasan dan shine yace "ke 'yar Riyadh baki iya gaisuwa ba har yanzu Aunty Fadilaty sei yaushe ne bikin namu ko kin fasa bani"?.
Jin abinda yake cewa a firgice Amatu ta d'ago tana kallon shi da mamaki sannan ta kalli Zarah da take ta 'boyewa a bayan ma'asumah cikin tashin hankali zuciyarta na zugawa da 'karfi kamar ya bikinsu kenan son Zarah yake auren ta zaiyi innalillahi wa inna ilaihi raji'un 😭😭 ji tayi kamar ta d'ora hannu aka ta fara 'kara da ihu ko zataji sassauci a zuciyarta lokaci guda ta d'ago idonta ya fara sauya kala jin Aunty Fadilaty tana cewa.
"A'a Asad yaushe zan hana ka saidai idan kaine kace baka so"?.
"Eh ina so man amma tsoro nafa take kamar mala'ika taya zaman zai yuwu"?.
"Humm ai zata saba, kai dai yanzu kana shiri ne"?.
"A'a".
"Oh baka shirya ba sai yaushe"?.
"Babu rana Aunty Fadilaty zarah na tsoro na taya zata iya zama tare dani ba kwana daya ba ba biyu ba balle ina da mata ta ita kadai ta ishe ni rayuwa jinta nake kamar da dubu" maida hankalin sa kan zarah yai yana cewa "kina da saurayi ne" a firgice Zarah ta kalleshi cike da tsoron kar yace zai aureta ta girgiza masa kai tana shashshe'kar kuka.
"Ok da gaske ne Aunty Fadilaty bata da saurayi"? Kai Aunty Fadilah ta d'aga "eh da gaske ne akwai wani d'an gidan 'kanwar Abi d'inta yana sonta sunansa Haysam tana kiransa Akih tunda yace yana sonta ba sosai take kulashi ba har yayi nacin ya ha'kura".
Kai asad ya jinjina yana kallon Zarah da take kallon sa itama da hawaye ya fara taruwa a idonta yace "ke kalle ni nan" yai maganar babu wargi 'kara 'kan'kame jikinta zarah tai ganin ya fito mata da dukkan girma idonshi murya ba wasa yace "d'an uwan naki ne bakya so? Haysam Abraham ai na sanshi ki za'ba koni koshi kuma basai kinje ko'ina ba yanzu nake son jin amsa anan gurin idan kuma ba haka ba gobe sai an d'aura mana aure".
Kuka Zarah keyi cikin tashin hankali yayin da Amatu ma taji kamar ta d'ora hannu aka itama ta fara kukan ba'kin ciki ko zai fahimta ya daina wannan maganar da yake wacce take shirin tarwatsa mata zuciya tasan gobe daurin auren Ajeeb Annur ba karamin aikinsa bane yayi abinda yace itakam Aunty Fadilah dad'i taji domin dama dangin baban Zaran suna ganin laifinta wai data yarda ai Zaran bazata 'kishi ba tace "yauwa Asad dan Allah ka taimaka kaje Riyadh idan mun koma dama yarinyar nan ana ganin kamar nice na hana ta taso Haysam ni kuma ina bakin kokari na".
Asad har lokacin idonsa nakan zarah yace "yanzu komai yazo karshe na gama magana wa zaki d'auka ni ko shi ki bani amsa da wuri tun kafin ki fusata ni"? Zarah na shashshe'kar kuka😭 tace "wallahi ni ina son Haysam bance bana son shi dan Allah kayi hakuri".
"Ok yayi amma ki tabbata abinda ke ranki kika fad'a min dan bana son karya zanzo Bahrain zan biyo ta Riyadh zanyi bincike tashi kiba mutane guri 'yar 'kauye kawai" da gudu Zarah ta fice daga part d'in tana kuka dama neman hanyar guduwa take sukam cigaba sukai da hirarasu har wani lokaci kafin sukai musu sallama suna tafiya.
Amatu ta tashi da sauri fiiiiii ta shige bedroom da kallo Asad ya bita da d'an surprise a face nasa ita kuma wannan yarinyar lafiyar ta? mi'kewa yai yana bin bayanta a tsaye ya sameta ta jingina da bango tare da rufe ido tsayawa yai ta gaban ta yana 'kare mata kallo kafin yace.
"Kina lafiya"?.
Bud'e ido tayi tana kallon sa kamar zatai magana sai kuma ta fasa tana shagwa'be fuska kamar zatai kuka ta cire hijab d'in tana jira dashi zata bar gurin batare data bashi amsa ba ri'kota yayi yana dawo da ita da baya da baya ya mannata da jikinshi cikin kunnen ta yace.
"Fushin me kike"?.
Har lokacin ta'ki bashi amsa kuma ta cika tayi fam hannunsa naka 'kirjinta shiru yai yana sauraron yadda zuciyarta take bugawa da 'karfi da sauri har gudun yayi yawa jan towel d'in yayi 'kar dashi da sauri ta ri'ke tana 'kara kumbura juyo da ita yayi suna fuskantar juna ya ri'ke kafad'unta ita kuma kanta yana sunkuye ta'ki d'agowa ta kalleshi saukar muryarsa taji yace.
"Hauwa'u Abubakar"🤩🙉.
Tab a d'ari ta d'ago idonta dayai jaa tana kallon shi jin sunan da bai ta'ba kiranta dashi ba yasa ta 'kureshi da kallo shima ita yake kallo yana karantar yanayin ta dama yayi hakan da niyya ne dan kawai ta d'ago kallon da take masa ne ya fallasa asirin abinda data 'boye a zuciyarta kamar idan ya fahimta akan Zarah ne tai fushi girgiza ta yai yana sake dubanta yayi murmushi yana cewa.
"Mrs ASAD da gaske ne?.
Had'e rai tai muryarta a hankali tace "da gaske ne me"? Ta fad'a tana d'auke idonta a kansa dan karma ya gane cewa kishinsa take.
"Da gaske ne kishi ne ya kama ki akan Zarah"?.
Jin tambayar dayai mata yasa ta sake had'e girar sama da ta 'kasa tana cewa "a'a" shine kawai abinda tace tana san zamewa ta wuce turata baya ya 'karayi yana matseta sosai a jikin bango har saida ta runtse ido yana kallon ta bai sassauta mata ba saboda hukunci yake bata yace.
"Da gaske kina kishin tane"?.
Haushi tambayar ta bata ga ciwon da jikinta keyi cikin son abar maganar tace "a'a akan me zanyi kishi da ita dan kawai kana son ta sannan 'yar uwarka ce ta jini tun kafin ka sanni ka santa kake sonta akan me zanyi kishi indai ba son wahalar da kaina nake ba"?.
Zuba mata ido yayi yana cije lips yace "oh really? Da gaske kike bakya kishi akaina"? "Eh" ta fad'a tana kallon sa murmushi yayi yana cewa "amma taya zan yarda bayan ga kishin nawa nan ina gani cikin wadannan kyawawan idon da suke nuna son abin abin kaunar su suna taya ki kishin mijinki🤗 right"? Kin fad'i abinda ba haka yake a zuciyarki ba, sannan son Zarah da kike magana akai eh da gaske ne ina sonta kinsan tun yaushe nake sonta? Ya tsaya anan yana ri'ke hannuwanta duka biyun yaci gaba "tun tana shekara biyar saidai dama ban zurfafa sonta akan dole zan aureta ba ban ta'ba kawo haka a raina ba ko a mafarki domin tun tuni ina da wacce nake so a waccan lokacin itace first love d'ina saidai na manta sunanta da inda take da kuma inda muka had'u amma ban gogeta a zuciyata ba kuma ko yau na ganta zan aureta na zauna da ita na bata gata but hakan ba yana nufin shikenan na daina sonki ba a'a kema jaruma tace kuma ina matukar sonki da dukkan zuciyata dan haka karki damu akan Zarah nayi mata barazana ne kawai d'azu niba aurenta zanyi ba never mind bayan ina da ke jewel inji Mami farin cikin Asad mother of my kids🤼 baiwar Allah Amatur-rahman zance ko Amatul-azeez wanne kike so😇"?.
Yana rufe baki ta saka mai kuka tana rungumeshi murmushi yai wato dai da gaske kishin ne ya rufe mata ido hartai fushi tab anya zata yarda idan ya samu yarinyar da yake nema ta bari ya aureta ya hasko wani irin damuwa dashi da Amatu tayi tana masa tsaftaceccan so wanda batai wa kowa tayi nisa a cikinsa kuma yana girmama hakan a nasa 'bangaren ma ji yake kamar ya fita damuwa da ita datayi dashi.
Zamewa tai daga jikinsa tana tafiya ta zauna a bakin gado taci gaba da kukanta tsayawa yai guri daya yana mata kallon mamaki cikin tsokana yace.
"Mrs Asad dama ke raguwa ce"?.
Wani kallo Amatu ta masa ji take kamar ta tashi ta rufeshi da duka😳 wato abinda zaice kenan maimakon ya lallameta lallai ta yarda da gaske Asad baisan yadda ake lallashin mace ba.
"Me kike tunani? Na miki tambaya baki bani amsa ba ada ke jaruma ce but yau d'aya kin gaza kinyi rauni naga kin zama raguwa why"?.
Goge hawayen fuskarta tai tana tamke gira tace "kamar ya"?.
"Kamar yadda kika ji nace haba Mrs ni😂 kamar ba kece wannan jarumar da take tarwatsa taron maza ba ina kika bar 'karfin zuciyarki kamar ba soja ba an sanmu da juriya🤷😎"?.