Sashe 59
Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tafiya sannu sannu kwana nesa lokaci ya mi'ka shekarun da aka d'ebawa Tanko na zaman gidan yari sun cika ya dawo gida Hummm!!!🤪 Me kuke tunani Tanko ya dawo bayan wadannan shekaru da wani irin turnu'kakken ba'kin dafin d'acin 'bacin rai na daukar fansa da mugun nufi musamman daya tarar babu iyayen sa ko daya sun rasu ga cewa da mahaifin sa yai bai yafe masa ba ya cuceshi Allah ya isa ce tsakanin su nan ba'kin ciki 'kiyayya ta kara d'amfara a zuciyarsa ga rad'ad'i da hassada ganin yadda su Habu suka zama masu arziki matuka wanda kaf garin babu kamarsu musamman Habu shi yafi Sabi'u da Ilyah kud'in ma kamar yayi ga rabon kayan arziki da suke a gari duk an daukake su ganin haka baiyi wata ba wata ba ya samu Mudi suka had'a hannu domin d'aukar fansa gari gari suka rika yawo domin cimma 'kudurinsu a karshe suka sami wani boka sunansa Hambuwa😡😱 yayi musu aiki, aikima kuwa mummuna maici tun daga wannan lokacin Malam Habu ya fara ganin canji a kasuwancinsa da al'amuransa haka ake tafiya har lokacin damuna kamar yadda suka saba ana raba musu kayayyakin amfanin gona kamar su buhunhunan taki dasu shinkafa da Abubuwan feshi daga baya idan kaka tayi sai su biya Malam Habu yana d'aya daga cikin wadanda ake kawowa mota mota saidai a wannan shekarar sakamakon hannu da aka saka masa sai kaf gonakinsa suka 'ki yin abun arziki gonar kowa 'kalau amma tasa hayam yaga tashin hankali ya shiga damuwa a haka dole ya samu ya sassayar da wasu filayensa da gonaki ya biya amma me Tanko bai barshi ba ya sake komawa cewa a rufa masa ba'kin 'kyalle ya zama kasuwancinsa ya dod'e samunsa ya tsaya cak ya ri'ka baya ya talauce ya lalace haka Malam Habu lokaci d'aya abu ya juye ya'ki masa dad'i aka wayi gari bashi da biyar tasa dazai d'aga yayi ikirari da mallakin sace babu abinda ya rage masa daga gona guda d'aya sai gidan da yake ciki Sabi'u ne ya d'auke dukkan d'awainiyarsa da iyalansa komai shine yake masa suna cikin haka me rabawa tazo ta raba ciwon cikin rana d'aya Malam Sabi'u yabar duniya😭 Malam Habu ya shiga tsananin tashin hankali da rud'u yayi kuka yayi ba'kin ciki da rashin d'an uwansa saidai duk da haka matar Malam Sabi'u Rakiya tana kokari wajen d'an taimaka musu iya iyawarta.
(*(*()*)*) (*(*()*)*) (*(*()*)*) (*(*()*)*)
😣👉Wannan shine asalin labarinsu da abinda ya faru a baya👈😔.

💃🍒MUN DAWO CIKIN LABARI🍒💃
Hassan da Hussaini 'ya'yan Ilyah sun dawo daga neman kud'in da suka tafi Cameron bayan shekaru biyar Ilyah yayi farin ciki ya 'kara ji yake kamar ya goyasu a bayansa tsabar so da gata gasu da girman kai na bugawa a jarida Amatu ma tad'an samu hutu tazo ganin gida ta tarar da wadannan samarin sun addabi gari suna fariya sunce babu yarinyar data isa su sota 'yan matan 'kauyen kucakai ne sunyi musu 'kazanta kullum saidai su ci wanka da kwalliya su fantama a gari babu ruwan su suyi shiga kowacce iri ce maimakon Ilyah ko Bara'atu suyi musu fad'a sai hakan ya zama abun burgewa har fasa kai suke yanzu 'ya'yansu ne suke lokaci a garin babu kamarsu hatta Nafisa haka tad'au huma da 'kafafa wai yayyinta sun dawo daga wata 'kasa sun zama 'yan gayu ga yanzu Nurain dinta ya bud'e wuta da kashe mata kud'i ya sai mata waya babba a sati sau biyu yake zuwa ya ganta ya koma su Ilyah anyi hototo ana han'kara ha'kora a gari 'ya zatai aure a binni zata fita zakka a 'kauyen, yana cikin wannan murna ne sabon al'amari ya sameshi wato dai Hassan da Hussaini sun zo masa da zancen sun samu matan aure yayi murna ya hura hanci jin shima lokaci yazo kansa zai d'au surukai🤣🤩 suna zaune bakinsa ya'ki rufuwa kamar gonar audiga yake kallon su da annuwa yace.
"Ah masha Allah Hassan haka nake son ji ko kufa amma da kun tafiyar ku daga neman kud'i kune har shekaru biyar baku dawo ba 'yar gidan wa kake so a ina take fad'a min ko waye ubanta matukar a 'kauyen nan yake dole ya amince ya baka ita kodan kud'i na tunda a yanzu babu kamata".
Hassan yana zaune akan kujerar roba a gefe ya mi'ke yana gyara fosing cap d'in dake kanshi kafin ya kalli Ilyah dayai sa'kwa'kwa yana kallon shi alamar jiran amsa yace "ai baba ada nace nafi 'karfin aure a garin nan amma fa yanzu rana d'aya nayi karo da Amatullahi 'yar gidan kawu Habubakar kaga tuwo na mai na kawai sai kaje gurin sa kuyi magana abinda kuka yanke a shirye nake nan da wata daya ayi mana aure idan na tashi komawa Cameron mu tafi tare da aba ta kome kace"?.
Wata iriyar 'kamewa Ilyah yai yana kallon Hassan jin abinda yake cewa yasa yaji cikin sa yana hautsinawa tari ya d'anyi jin zai 'kwaru kafin ya sake d'agowa yana cewa "mema kace Hassan banjika sosai ba kunne na ya fara samun matsala d'an maimaita kace me"?.
'Kara d'aure fuska Hassan yai domin tunda suka dawo ya samu labarin Ilyah ba ruwansa da Malam Habu kuma wannan tambayar dayai masa yaga take takensa na 'kin amincewa auren abinda bazai yuwu ba kenan me hana shi auren Amatu a yanzu sai mutuwa🤷.
"Hassan nace me kace"? Ilyah ya sake jefa masa tambaya yana karkata kunne yaji me Hassan d'in zaice kauda kai yace "cewa nayi ina son Amatullahi 'yar gidan kawu Habubakar kuma so na aure aurenta zanyi shiyasa nazo na sanar dakai".
Kai Ilyah ya jinjina cikin takaici yace "Au haba auren ta zakai? shiyasa kazo ka kayi min 'kerere akai kana kallona kamar zaka rufeni da duka ka aureta dai? Shiru Hassan yai yana murgina kai Ilyah yaci gaba "lallai Hassan yau na yarda ka fara haukacewa to bari kaji wallahii wallahi tallahi wallahi tallahi kaji rantsuwa uku ko? To wallahi bazaka aure taba ba Amatu ba ko Binta ce uwar data haifeta saika rabu da ita kaji dakyau na fad'a maka shashashan banza sakaran asara wacce Amatun ka rasa inda zakaje kaso 'ya duk girman 'kauyen nan sai yar Habubakar matsiyaci fatararre wanda talauci yaiwa katutu Allah bazaka aureta ba wallahi kaji na fad'a maka".
Ilyah na rufe baki a zabure Hassan yace "wallahi tallahi wallahi tallahi wallahi tallahi na rantse da Allah kaji rantsuwa uku ko? Kallon sa Ilyah ya tsaya yi cike da mamakin abinda yake shirin yi Hassan yaci gaba "wallahi bazan rabu da ita ba saina aureta ko zakai bunga🙊🙊😂" zaro ido Ilyah yai yana sake duban Hassan takaici ya gama cika shi yace.
"Hassan Hassan tabd'ijan amma wallahi baka da hankali kayi hauka ne ni kake fad'awa haka"?.
Ran Hassan a had'e zaiyi magana Hussaini dake gefe yana cin abinci yace "ai bakai ba Hassan koni akwai wacce na hasko a cikinsu Aisha 'yar gidan Saude kuma babu wani so'ko'kon dazai hana na aure ta ban ganshi ba😲😁😳" 😂tabd'i tashin hankali wanda ba'a sa masa rana Ilyah kallon su yake a fusace ji yake kamar yayi hauka tsabar ba'kin cikin da suke cusa masa yama kasa magana sai sunkuyar dakai yayi yana shiru kallon juna sukai suna dariya Hassan yace.
"Baba karfa ka zauna 'bata lokacin ka wajen tunani da nazarin ya zaka 'bullowa al'amarin bari na baka shawara wallahi gara ka koma gefe ka zuba mana ido dan aure kamar munyi inace 'karfin zumunci zamu ninka ka manta me yanke zumunci babu shi ba rahmar Allah kai kuma kake kokarin rabawa tab kaji fa Hussaini meye makomar baba"?.
Batare da Hussaini ya d'ago yace "makomar sa suya da babbaka wuta ce idan aka wullashi saiya 'kone ya toye ya dangwalo 'kasan bakwai😲" had'a ido sukai suna fashewa da dariya Ilyah tsabar takaicin da suka 'kunsa masa ji yake kamar ya zubar da hawaye Bara'atu ce ta karaso gurin ranta a 'bace saboda tana jin komai dukkan su biyun ta kalla tana cewa "wai shin kun gamu da ciwon hauka ne a garin da kukaje kome? Uban daya haife ku kukewa dariya😡 gaskiya tunda har yanzu bakuyi hankali ba bansan yaushe zakuyi ba gani kuke riba zakuci ku tsaya ku gyara halinku wannan d'abi'ar da kuka d'auka bazai kai kuba".
"Yo umma ai kina jin fa abinda yake cewa miye a ciki🤷 dan kawai muce yan matan kawu Habubakar muke so ba abin farin ciki bane yana matsayin yayan sa amma harda wani wallahi tallahi wallahi tallahi wallahi tallahi kaji rantsuwa uku ko 😂😂 baza ku aure suba mu kuma wallahi tallahi saimun auresu ko mutum zaiyi bunga🙊🤩😂😂😂🤣 Hassan ya karasa maganar yana tsayar da idonsa tarr cikin na Bara'atu.
Kae Bara'atu ta jinjina tana cewa "tabdijam babbar magana kenan d'an sanda yaga gawar soja Hassan Hussaini yaushe kuka zama haka har ana fad'a muku magana kuna mayarwa dan raini to bari kuji maganar gaskiya koni ban amince muku ku auresu ba kun dai ji dakyau na fad'a muku inba shashancin kuba ai da gaske yake fatararran ne uwar me yake dashi yanzu wanda lomar abinci take masa wuya kowa yana gudun auren 'ya'yansa saboda kar talauci ya shafe shi ku kuma tsabar 'batan basira kuna cusa kai zakuje ku yayo mana masifa ku kawo mana gida lokacin da suke matasa kamar ku wanne irin wulakancin ne Habubakar baiwa ubanku ba har sha'ke masa wuya ya ta'ba yi ya hankad'a shi gaban Baffah duk wannan cin mutumcin dayai masa amma tsabar sakarci harku so 'ya'yansa uwar me zakuyi dasu meye abin so a jikinsu gayyar talauci da 'kas'kanci yanzu kaf garin nan ba wanda yakai gidan Habubakar fatara da shan wuyar rayuwa to wallahi baku isa ba kuji dakyau na fad'a muku".
Ta'be baki Hussaini yai yana kallon Bara'atu yace "wallahi umma saimun aure su ko mutum zaiyi bunga😬 garama kiyi shiru ki daina 'bata bakinki akan mu ba wani so'ko'kon dazai rabani da Aisha saiya shirya duk wanda yai yunkurin shiga tsakanin mu saina jajjaga shi nayi 'kuli 'kulin kubura dashi😲😂".