← Book details Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 120 OF 145

Sashe 120

Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Eh Mami sunan mu Aliyu, to amma ai itama sunanta Hauwa'u ake ce mata Amatullahi Kinga an raba ba wata jewel da zakice mata gaskiya idan ba haka ba nima saidai ki dawo ce min diamond😀"?.

Dariya Mami tai tana cewa "waye zan cewa diamond tab amma dai bakai ba saidai ka bari idan kayi aure kaima taka matar sai nace mata diamond tunda naga kishi kake da Asad ko"?.

''A'a niba kishi nake dashi ba Mami".

"To me kake inba kishin ba"?.

"Tsokana nake".

"Uhm ai a irin wannan tsokanar taka kake tsokano Asad d'in kazo kuyi tayiwa mutane hauka a gida kamar qananun yara Allah ya shirye ku dai".

"Amin Mami bari naje ina so Annur zai rakani wani wuri kar lokaci ya 'kure" ya karasa maganar yana mi'kewa tsaye.

"Ok sai kun dawo".

Fita yai yabar Mami da Amatu suna zaune su kad'ai Mami tana sake yi Mata bayani sosai tana qara bata qwarin gwiwa kada ta yarda ta nuna tsoron ta a gaban Asad idan ba haka ba zata sha wahala koda ace tana jin tsoron tafi bayyana jarumtarta wannan zai taimaka mata kuma zai ceceta zama da Asad sai jarumtacce balle ita da zatai rayuwar aure dashi ba zaman wuni d'aya ko kwana d'aya ba.

B'angaren Shaukiyyah amare a gidan Aliyu Ameer tana zaune Khaldiyyah da Khimiyyah sunzo mata amma banda Makiyyah domin dama kwana tayi tana kuka batai barci ba da gari ya waye ta tashi da zazza'bi mai zafin gaske ma kuwa ko ruwa ta kasa had'iya balle taje ga breakfast.

Cike da tsokana Khaldiyyah ta kalli Shaukiyyah tana cewa "a'a Shauki amarya a gidan prince Ameer yau ya naga babu shauki a fuskarki sai wani jaa d'auu datai ga idonta a kumbure miya faru ne ko duk kewar mu kike ai gamu munzo ko? sai abar kuka" ta karasa maganar tana kunshe dariyarta.

Harararta Shaukiyyah tai cike da takaici tace "ban sani ba idan ma isgili kike min kema ai baki haure ba abinda ya sameni yana nan zuwa kanki gara nima iya kuka nai ke wayasan me zakiyi"?.

Rufe baki Khaldiyyah tai tana dariya tace "au sorry ayya aina manta ashe fa ke d'in amarya ce dan anga kinyi kuka ma bai kamata a tambaye ki kukan meye ba bayan kowa yasan keda ango ne tab uhm Shaukiyyah ina kallonki haka ashe dama ke raguwa ce"?..

Cikin haushi Shaukiyyah tace "raguwar uban me? Kinga Khaldiyyah bana son rashin mutunci idan dama abinda ya kawoki gurina kenan sa ido tashi ki tafi".

Zaro ido Khaldiyyah tai tana cewa "to haba amaryar prince Ameer yada korata dan kawai nazo gaida dake nifa zuwa nayi na taya ki wuri wato daga kwana d'aya har kinsan dad'in miji shine zaki min gori"?...

Had'e rai Shaukiyyah tai tana cewa "uban nasan dad'in miji indai abinda yayi min jiya shine abun dad'i to kema ina miki fata Allah ya kawo miki miji ko yaune a d'aura miki aure kema ki d'and'ana abinda na d'and'ana ba isgili kike min"?.

Dariya Khaldiyyah tai tana kallon yadda Shaukiyyah tai da fuska kafin tace "ba Amin ba daina min fata tunda kinsan wanda nake so Annur ne kuma nasa a raina matukar bai amince ya aureni ba bazanyi aure ba gara na qare rayuwata a haka sannan shi prince Annur gentle Man ne".

"Au haba taya kika sani haka shi ya fad'a miki"?.

Kai Khaldiyyah ta d'aga ''kwarai ma kuwa na sani domin alamar qarfi tanaga mai 'kiba a iya yanayin sa kinsan nutsattse ne bazai bazai gigita mutum ba".

Kai Shaukiyyah ta jinjina tana kallon ta tace " to shi kuma Ameer burkitaccen mutum ne shiyasa ni yaci ubana kike nufi kome"?.

"No ba haka nake nufi kawai dai komai a sannu yake yinsa cikin sanyi kin gane"?.

"Uhmm" kawai shine abinda Shaukiyyah tace domin Khaldiyyah batasan komai ba ita kuma yanzun data sani batasan ta yadda zataiwa Khaldiyyan bayani ta fahimta ba sai kawai ta kyaleta suje a hakan zata tuna mata sai ranar datai aure washe gari itama zataje ta rama Khimiyyah kam tana gefe komai suke tana jinsu ko tari batai ba hankalinta yana kan wayar dake hannunta tana chatting da Hudayyah.

*** ** ***. ** *** ** ***
Nurain ne a zaune yana kallon Nafisa wacce idonta ya cika fal da hawaye yanata zuba ransa a mugun 'bace yace.

"Nafisat da izinin wa kika je kika zubar da ciki batare da sani naba dama nace miki bana son haihuwa ne ko kuma rainin wayo ne yasa kika aikata min haka"?.

Yana rufe baki ganin Nafisa ta kallo su Mimih tana shirin magana da sauri a gaggauce Zainab ta hana Nafisan dake shirin cewa wani abu ta zafga mata wata uwar ba'kar harara tana cewa "ke kinga ki rufawa mutane baki banza kawai jaka 'yar qauye wacce batai karatun addini ba jahila tsabar ke da'ki'kiya ce zakije ki xubar mana da babynmu yau saikin gane gaskiya kin cuce mu" ta karasa maganar tana kallon Nurain daya sake fusata kamar zata she'ke da dariya tace.

"Kuma abun haushin my choice nima har ina murna da farin cikin Auta ta kusa samun qani sai kuma na dawo aiki naji su Mimih suna cewa wai sunga Nafisa ta dawo daga asibiti da takarda a hannunta tana kuka da suka tambaye ta tace ciki gareta bata so ka sani dan Allah su rufa mata asiri tsabar gidadanci da qauyanci batasan cewa in ciki ya fita dole sai an gane ba humm gaskiya Nafisa baki kyauta mana ba kinyi mana asarar babyn mu" ta karasa maganar tana kau dakai gefe sakamakon dariyar dake ciciyarta ganin yadda maganar data fad'a ta sake sanya Nurain zabura ji yake kamar ya d'aga hannu ya sharara mata mari kasa-kasa Zainab take dariyar mugunta ganin yadda Nafisan tayi shiru ta kasa magana sai hawaye dake zuba tace.

"Kayi hakuri my choice tunda cikin dai ya riga ya fita shikenan saidai ai mata uziri kasan mutum idan bai karatu ba matsalar auren jahila kenan batasan doka ba inaga saidai ka sata a makarantan islamiyyah amma dai yanzun kayi hakuri idan ta sake ka d'au mataki me tsauri a kanta dan gaskiya babu wanda za'aiwa irin wannan abun bai d'auki hukunci ba".

Shiru Nurain yai ya kasa furta koda kalma d'aya tsabar ba'kin cikin da Nafisa ta cusa masa Mimih data d'auko littafi kamar gaske dan taji abinda suke tazo wucewa da sauri ta tsaya tana cewa.

"Ai yaya idan baka sani d'auko tan dakai daga wannan mummunan qauyen ka kawota tsakiyar birni baiyi mata amfani tunda gashi ba'aje ko'ina ba ta fara nuna maka ta waye ta hanyar zubar da ciki kayi tunanin gaba me zata aikata humm ba'a sani ba kawai yaya ka saketa yau ta koma karkararsu"?.

Mimih na rufe baki Nafisa ta d'ago a firgice tana kallon Nurain wanda shima ita yake kallo kai ta soma girgizawa cikin kuka tace.

"Dan girman Allah kayi dan Allah wallahi ba laifi na bane"?.

Zare mata ido Mimih tai tana cewa ''ba laifin ki bane laifin uban kine"?.

"Ke Mimih kada ki sake zaginta duk da kin fita koma dai yaya ne matar yayanki ce ita ya kamata ki bata girmanta".

Zainab tai maganar tana kashe mata ido murmushi Mimih tai kamar gaske harda d'an risnawa tace.

"Oh sorry na manta ne 'bacin ran rashin babyn mune yasa nace Mata haka kiyi hakuri Aunty Nafisa na😂" ta karasa maganar tana sakar mata zazzafar harara ganin ta d'ago tana kallon ta kafin ta kad'a kai tayi gaba Mimih na wucewa Zainab tace.

"My choice kayi hakuri kar kasa damuwa a ranka komai ya wuce".

Tsaki Nurain yai batare daya kalli inda Nafisan take ba dan ko ganinta yanxu bai son yi muryarsa da alamar fushi yace.

"Get to the point".

Tsiru-tsiru Nafisa tai domin batasan me yace ba kuma bata kawo da ita yake ta d'auka ko tsakaninsa ne da Zainab saida taji cikin tsawa yace.

"Ki 6ace min da gani kafin na 6allaki" jin abinda yace yasa da gudu Nafisa ta mi'ke tana kuka tabar falon tsaki ya sake ja a karo na babu adadi yana cizon yatsa Zainab kam tana gefe sai murmushi take tana rausaya kai mi'kewa yai zai fice yace.

"Ina da tafiya zuwa Singapore ranar Monday ki kira Mimih yanzu su d'auko Auta zamuyi sallama dasu"?.

Kai Zainab ta d'aga "ok my choice amma idan babu damuwa ka biya min kud'in jirgi na zuwa sai nayi na dawowa ina son zanga qasar please" ta fad'a a marairaice.

"Ok shikenan" shine kawai abinda yace mata kafin ya fice tsalle Zainab tayi cike da murna domin tasan tunda ransa ya 'baci indai baiyi nesa da Nafisa ya huce ba tofa akwai matsala shiyasa take so ta bishi su tafi tare taje ta d'auke masa hankali su dad'e basu dawo yadda Nafisan zata gaji ta gudu qauye koda tasan ma bazata iya zama ba domin su Mimih bazasu barta Tasha koda ruwa ba tsabar wuyar da zasu d'an'dana mata.

🌑🌚INSIDER🌚🌑
BAYAN WATA HUD'U
_____Khimiyyah ce zaune tare da Hudayyah a gurin Muheed dake d'aure Hudayyah na sake jaddada masa cewa har yanzu yana da damar cewa yana sonta zai aureta shima yana fad'a Mata kalma d'aya bazai ta'ba auren taba koda ace zai rasa rayuwarsa ne.

Gurin Prof Jibril da Mr Famous dake gefe Khimiyyah tayi ga kuma Danual Chai daya koma wata kalar siffa a gabansu yana fad'a musu sirrin daya sake binciko musu ta yadda mutum zai iya zaka kowacce halitta yake son komawa karaawa tai tana cewa.
Chapter 120 · 0% Book details