Sashe 127
Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
_Clarah ta shiga matukar damuwa rashin kular da Asad ke bata gabadaya ya tattare hankalinsa kan aikinsa koda yaushe suna bincike wanda ko fuskar gaidashi yanxu bata samu ga ba'kin cikin yadda Amatu tazo sama takai tayi suna cikin shekara biyu kowa ya santa tayi suna manyan mutane suke ji da jarumtarta tasan cewa ta zarce mata sannan har ranta ta yarda bazata iya kasada da ranta kamar yadda Amatun keyi ba domin maganar gaskiya itakam bata so ta mutu😳 badan Asad bama da yanzu ta fice a aikin amma haka zatai ta ha'kura ta lalla'ba shi ya aureta shine burinta da damuwarta tana jin takaici idan ta hango Asad tare da Amatu ji take kamar ta had'iyi zuciya ta mutu tana matukar kishi akan Asad gashi abinda kullum yake sake tarwatsa mata tunani yake firgita mata lissafi shine har yau ta kasa sanin ainishin wacece Amatu meye matsayinta a gurin Asad sister ko wife amma tana so ta sani kuma tana so ta gane saidai ta jarraba su ta wannan hanyar ne kadai zata fahimci komai to amma ta yaya ta tambayi zuciyarta tana cizon yatsa saboda ba'a fi kwana goma ba da sake wayarta Asad ya fad'a mata wata maganar data razanata ta saki wayar ta fashe to ita yanxu ya zatayi wani bangaren a ranta yace.
"Kiyi kiransa a waya tunda yau hutu yake kice masa da yamma yazo kuje shan coffee idan har ya taho da ita budurwar a gurin zakiyi kokari kiyi wani abu da zai fallasa abinda ke tsakanin su harki gane wacece ita" kai ta jinjina cikin gamsuwa kafin ta d'auki waya tana saka kiransa.
A lokacin yana tsaye a bayan Amatu wacce ke zaune gaban laptop tana duba masa wani abu kiran ya shigo wayarsa kamar bazai d'aga ba saida ya bari ta katse yabi bayan kiran.
Jin wayar tayi ringtone harta katse ba'a d'aga ba yasa Clara d'ora hannu aka tana cewa "na shiga uku Asad zai kasheni da wannan shariyar da yake nuna mi............
Kiransa ne ya shigo wayarta da sauri ta d'aga tana cewa "hello Asad kana jina"?.
Asad yana tsaye daidai Amatu tana nuna masa wasu bayanai data binciko ya du'ka yana kallo yace.
"Ina jinki meya faru"?.
Gyara zama Clarah tai tana kashe murya tace "am Asad naga yau ranar hutu ce babu inda za'a fita amma har yanzu shiru kana gida"?.
"Eh wani abu ne"?.
Kaita girgiza kamar yana gabanta tace "a'a yaushe zaka fito ina so muyi magana"? .
"Ke kullum a kina so muyi magana zaki qare kamar mara aikin yi"?.
"Asad please ka bani dama.....................
"Kinga Clarah don't wast my time yanzu nake I don't have a time you".
Jin zai kashe wayar yasa da sauri tace "am dan Allah Asad zuwa yamma ina son zamuje shan coffee".
"Ok"
Kawai yace yana katse kiran sau'ke ajiyar zuciya Clarah tai tana kallon numbern wayarsa kadai tsintar kanta takeyi a cikin farin ciki balle ta zauna guri d'aya gata gashi shiyasa yanzu take shan ba'kin cikin rasa d'an lokacin nasa datai.
Kaita jinjina tana mi'kewa fuskarta da murmushi a ranta fad'i take "wallahi a yau bazan kasa a gwiwa ba koda ace Asad zai kasheni saiya fad'a min wace wannan yarinyar sai nayi abinda dole ya nuna min alamar sister ce gareshi ko mata bari evening d'in tayi" ta fad'a tana qwafa tare da sanya hannu cikin ajihun wandonta taci gaba da zaga gurin ji take kamar ta jawo yamma domin komai ya faru a wuce gurin.
Saida suka gama abinda suke Amatu ta mi'ke tana d'an dafe baya alamar ya ri'ke ciwo yake mata muryar Asad taji yace.
"Meya sameki a baya yana miki ciwo ne"?.
D'an yamutsa fuska tai tana jinjina kai kafin tace "eh amma ba ciwo ne mai yawa ba kad'an kad'an".
"Ok k'arfe biyar zan fita ki shirya muje tare".
To Amatu tace masa tana d'aukar laptop da wayarta ta shiga part d'in daya bata tana zuwa ta kwanta domin ta huta dan a yau inba yanxu ba bata samu hutu ba tun asuba har sha biyu.......kira ne ya shigo wayarta d'agowa tai tana kallon screen d'in ganin mai kiran yasa ta d'aga.
"Me kike so"?.
Numfashi ta sauke dan yadda take jinta a gajiyen nan bata son cin komai hutu take so kawai amma dai sai tace.
"Iya fruits salads yayi".
"Ok give me some minutes".
Aje wayar Amatu tai tana mi'kewa ta tsaya jikin window tana kallon waje yadda qasar take da kyau ko'ina fas bata ta'ba tunanin zata kawo irin wannan matsayin ba bayan duk abubuwan da suka fuskanta a baya da qalubalen rayuwa amma Allah mai baiwa wanda yaso a sanda yaso shekara da shekaru mahaifin su nashan wahala lokaci guda rayuwar su ta sauya suka taka matakin ba basu ta'ba tunanin takawa ba Jamila tayi aure tana xaune lafiya harda d'anta ga Asma'u irin dad'in da take sha da gata a gurin Alhaji Musa da matarsa Hajiya Aisha sannan gidansu ya daidaita babu abinda suka nema suka rasa duk wata damuwa da wahala ta kare ta sani Aisha ma tana can cikin farin ciki domin mijinta Safwan mutum ne na kwarai kuma yana sonta da dukkan zuciyarsa ga rufin asiri da yake dashi itama babu abinda ta nema ta rasa nata auren ne dai yaxo a juye tunda wanda aka aura mata ba mace a gabansa amma duk da haka alhamdulillah itama babu wani aure yanzu a ranta ya fice Mata akai aikinta tasa gaba tunda ya nuna mata tayi aikinta yanzu ba lokacin wasa bane.
🕔K'arfe biyar da rabi Asad da Amatu suka fito cikin shiri suna sanye da kaya iri daya shi bulun kyakkyawan tsadaddan yadi mai shara-shara mara nauyi yasa farin takalmi da farin agogo kansa babu hula gashin sa ba'ki ya tajeshi ya gyara sai she'ki yake ita kuma tana sanyi da riga da skirt blue and white tasa farin takalmi itama da siririn mayafi fari wow Masha Allah saima ka gansu kamar karka daina kallonsu sunyi matukar dacewa da juna a haka amma a ran kowanne babu wannan maganar musamman ma Asad yafi bada qarfi wajen ri'keta matsayin qanwarsa.
Clarah na tsaye jikin motar Asad dama already ya fita da ita waje saboda fitar da zasuyi tasha riga da wando jeans ba'ki kanta da hula bata daure gashin taba yana sake har bayanta tana waya Mom d'inta fuskarta fal da murmushi da farin cikin yau Asad ya bata time d'insa zata fita tare dashi har wata dariyar annashuwa take yi d'agowa tayi tana magana.
Lokaci zuwa lokaci tana kallon hanya ta kalli agogon dake daure a hannunta tana cikin dariya ta hade rai lokaci guda tana dafe 'kirjinta ba zato ta saki wayarta ta fad'i karas tass jikinta na rawa take kallon Asad da Amatu da suka karaso gurin yanzu daukar wayar Amatu tai tana mi'ka mata kasa kar'ba tai sai kallonta da take kamar idonta zai fito waje tsabar tashin hankali da firgici.
"Malama take ur phone zamu wuce".
Asad yai maganar ganin zata bata musu time a banza da'kyar tasa hannu ta kar'ba tana kallon screen din dayai fatsa fatsa ji tai wani kishi ya taso mata kamar tace ta fasa fita domin batai tunanin harda Amatu ba gashi sun shige gaba sun bar mata baya kamar ta fasa ihu haka taji jikinta sai tsuma yake so take tace bazataje ba ta fasa zuwa amma me Zuciyar ta na gargad'inta tasan waye Asad matukar ta furta wannan kalmar shikenan sun gama fita bazai sake zuwa ko'ina da itaba har abada jin ya tada mota zasu tafi su barta yasa jiki a mace taja kafa kamar me ciwon cinya tana bud'e back seat ta shiga ta zauna tare da d'auke kanta daga saitinsu har sukaje inda zasu idonta na rufe saida taji an tsaya kafin ta bud'e harsun fita sun fara tafiya da sauri itama ta fita da gudu gudu tabi bayansu can gefe nesa da mutane suka samu kujeru suka zauna babu wanda yace 'kala Clarah kam ta cika tayi fam ta kumbura kamar fulawar da yis ya mata yawa kad'an take jira ahau sama a fad'o😠 yau saida ta shawo bala'i tana neman fitina dama ta fito sai an yinta ta qare sai tasan wacece wannan budurwa ayau ko me Asad zaiyi mata zata d'auka indai zai fad'a mata wace itan.
Coffee mai zafi da had'uwa aka kawo musu kofuna uku nanma kamar bazata shaba ko kallon coffee d'in batai ba domin ba shine a gabanta yanzu huci da turiri ne kad'ai ke fita a ranta runtse idon tayi tana tunanin yanzu me zatai wacce hanya zata fara bi dan ta fusata ÀSAD harya fad'a Mata matsayin Amatun a gurin sa to amma taya?.
Wani tunani ne ya fad'o mata cewa ai itama mace ce bari tayi wani bariki man dan burge Asad da jan hankalinsa wanda take so hakan ya ba'kanta ran Amatu itama irin d'acin da take ji murmushi ta saki tare da daidaita fuskarta cikin sassauta fushin dake cin zuciyarta tace.
"Asad nifa bazan sha wannan coffeen ba".
Batare daya kalleta ba yace "what do you mean"?.
Kallon Amatu Clarah tai ganin itama ta d'ago tana kallon ta yasa ta aika mata da wani irin kallon mai ma'ana tana jan tsaki a ranta sannan ta ta'be baki tana sake kashe murya tace.
"Ni hannunka nake so nasan zaifi min dad'in sha zan shanyesa gabadaya batare dana sani ba".
"Meya samu naki dole sai nawa"?.
Saida ta kalli Amatu tana sakar mata harara kafin ta karya kai tana cewa "babu abinda ya samu nawa naka nake so kasan masoyi koda yaushe masoyi ne ina 'kokarin tuna maka matsayina a gurin ka tun shekarun baya ka daukake ni da yawa nagode da kulawa dan haka ni naka coffee d'in nake so nasha ta saitin inda kasha idan kuma bazaka bani ba na ha'kura".
Ta karasa maganar cikin shagwa'ba tana sakin 'boyayyan murmushi ganin Amatu ta zuba mata ido d'agowa Asad yai ya kalleta sai kawai yaga ta kashe masa ido tana cewa cikin shagwa'ba.
"Please my soul ka bani".