← Book details Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 145

Sashe 66

Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

YUSRAH MUSA ABUBAKAR INA YI MUKU BARKA DA JUMA'A FATAN DUK ALKHAIRIN DA YAKE A CIKIN WANNAN RANA ALLAH YA SADA MU DASHI DOMIN HASKEN MASOYIN MU🙏 ALLAH YA GAFARTAWA MAHAIFAN MU😭😭😭 MUSULMAI MAZA DA MATA WANDA SUKA RASU ALLAH YA MUSU RAHMA YA LULLU'BE ZUNUBAN SU🙏🙏🙏🙏.

👇👇👇
It's Friday don't forget to recite suratul Al-khaf may Allah bless you and your household may Allah open the door of success 4u all Muslims.
Juma'at Mubarak by Yusrah Musa Abubakar maman little Zaran aunty 💃💃💃💃.

47~AL-WADUD
The Loving
48~AL-MAJID
The Glorious

23~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Munzirinah.

🌄 LEAVE TAKING ND WED🌄
Episode 47_48
_____Kwana biyu tsakani kamar yadda Sadi ya fad'awa Malam Habu haka ne ya faru sun tafi Cameron cikin 'kwarin gwiwa da zummar neman kud'i ta hanyar halal basu sare ba musamman Malam Habu tsabar farin ciki kasa ko shan ruwa yai har suka tafi nan labari ya karkad'e gari malam Habu da Sadi sun tafi neman kud'i Cameron kowa da abinda zai tofa wasu na fatan alkhairi wasu na fatan tsiya harda masu cewa kowa yai ta kansa kwanan nan malam Habu arzikin sa zai dawo ya manta da rayuwar 'kunci.

🏙️DUTSE MOPAL-BASE🏙️
Cikin shiri Amatu da Maryam harda Nabilah suka fito harabar gida Maryam na d'auko musu mota zasuje Miyetti kar'bo d'inkin ashobi d'insu idan sun dawo zasuje benin galadima a musu saloon sunsha gyara kamar sune amaren Maryam ce ke driving lokaci zuwa lokaci tana kallon Amatu dake ta faman murmushi cikin mamaki tace.

"Amatullahi na tambaye ki"?.

Juyowa Amatu tai tana kallon ta har lokacin da murmushin ta akan fuskarta tace "eh meya faru"?.

Daidai Maryam zata sha kwanar asibitin police clinic ta shiga takur site zuwa gidan 'kanwar ummansu tace "nifa na kasa ganewa tun d'azu muna breakfast naga sai murmushi kike akwai abinda ya saki farin ciki ne"?.

"Kai Amatu ta d'aga tana cewa "eh akwai kawai na matsu sosai gobe tayi ne".

'Dan zaro ido Maryam tai har tana hadawa da dariya tace "saboda kece Aunty Lailah amarya"?.

Kai Amatu ta girgiza "a'a kawai na tuna gobe umma zata zo zan ganta ta ganni kuma na tabbata babanmu zaizo d'aurin aure Allah yasa domin ambatonsa danai har yasa naji ina kewarsa ke kuma har kikai min wata fassara daban wai amarya rufa min asiri ina zaune lafya amarya a gidan wa".

Le'kowa Nabilah dake baya tai tana cewa "amarya a gidan mijinki koba haka ba"?.

"Eh ba haka ba waye miji na"?.

"Mai sonki mana".

"Waye mai Sona"?.

"Hhhhh ji Amatu da wata tambaya dan Allah taya zan sani abu a duhu kodan banace ba ko wannan zuwa gidan da kikai wani yace yana sonki".

"Oh Nabilah zaki fara ko? Please kiyi shiru".

"Shikenan nayi shiru🤭 Nabilah ta karasa maganar tana rufe bakinta parking Maryam tayi da mota suna fitowa suka shiga gidan da ya kasance gate ne amma ba mai gadi kuma ba laifi gidan Masha Allah ya matukar had'uwa matar gidan tana zaune a parlor tana kallo suka shiga da sallama ganinsu yasa ta d'au remote tana rage 'karar vidion tace.

"Tofa Antin gida (Maryam haka take kiranta saboda sunan yayar mijinta ce) yau kune a cikin namu sannunku da zuwa bismilllah ku shigo man kuke ra'bewa kamar wasu ba'ki" zama sukai suna gaishe da ita ta amsa da fara'a taba kallon Amatu tace "wannan yarinyar ce 'yar gidan Binta yayar Bashir ko"? Kai Maryam ta d'aga "eh itace Aunty Umma munzo kar'bar ankon mu a gurin telan momy shine nace bari mu karaso mu gaisa ke"

"Aiko kun kyauta Maryam nagode muku kunfi Ahmad zumunci gashi a kwanakin nan kusan zuwanku hudu amma yaron nan shiru kamar baya gari rabo dana ganshi harna manta sai yanzu da bikinsa ya tashi zanje mu had'u ai sai naci 'kaniyarsa".

'Yar dariya Maryam tana mi'kewa tace "ina Ikram ko bata nan banji motsinta ba"?.

"Oh Ikram tana kitchen wai saurayinta nefa zai zo daga nan-nan Yadi shine take masa iyayi tun d'azu a kitchen ko uwar me take girka masa oho shima da bajajjan hancinsa a gurin".

Murmushi Maryam tai tana cewa "bari na gano abinda take yi ku jira ni" Maryam na rufe Nabilah tace "ai gara kizo mu tafi dan Allah wallhi yanzu idan kika shiga gurin Aunty Ikram sai mun 'bata lokaci muzo munata jiranki baki fito bakuma kin manta zamuje saloon"?.

Wucewa Maryam tai tana cewa "a'a ban manta ba ku jirani minti daya shigewa hanyar da zata kitchen tai tun kafin ta karasa taji Ikram na sakin ashar loya-loya a waya da sauri ta karasa tana cewa.

"Iki miya faru kike zagi"?.

Da sauri Ikram ta rungume Maryam cikin murna tace "ke sis yaushe kika zo kullum ina kiran wayar ki amma ta'ki shiga"?.

Had'e rai Maryam tai "humm ban yarda ba Ikram ganin idona yasa kika ce haka"?.

"Ke wallahi da gaske bata shiga but idan kin koma ki tambayi ya Ahmad zai fad'a miki ai shi muna waya dashi".

"Na'ki na tambaye shi idan da gaske ne ki bari saina koma zan tambaye shi domin daga nan Miyetti muka nufa bari na tafi dama Nabilah tana can a falon Aunty umma tana min 'korafi".

"Oh harda Nabilah kika taho"? Ikram tai maganar tana d'auko abinda data dafa masa da wanda ta soya dukka ta d'ebo musu shi zuwa falor amma Maryam tace bazasu zauna ba kar lokaci ya kure a yau zasuje saloon da lalle gashi yaune farin biki yace sai anyi 'kauyawa party suna shirin tafiya Ikram tace.

"Ku jirani kawai bari na dauko kayana mu tafi nima tunda nasan umma zuwa jimawa zaki le'ka kema ko"?.

Kaita d'aga mata "eh zanje mana zamuje mu gano 'kauyawa party dole" wucewa Ikram tai tana d'auko kayanta a jaka zasu tafi sukaiwa Aunty umma sallama .

Saida suka gama safgoginsu sannan suka kar'bi ashobin suna komawa gida ko zama basuyi ba iya kayan suka aje cikin sauri ganin lokacin yana neman fita musu suka tafi saloon basu suka dawo ba sai la'asar sosai a harabar gida suka ga Ahmad da wasu abokansa suna magana ganinsu yasa yace.

"Amatu dama ke nake nema dan Allah ki fad'a min ya shigar 'kauyawa take mun rasa yadda zamuyi"?.

'Dan harararsa Amatu tai tana had'e rai tace "ai nima ban sani ba saidai kayi sacin a gogul zaka gani" dariya Ahmad yai "haba ke kuwa sorry gani nayi ke kin sani shiyasa Allah kuwa serious nake tambayarki ki fad'a min yadda zanyi"? "Shikenan zan fad'a maka sai zuwa jimawa dan wallhi yanzu a gajiye nake" .

"ok ba damuwa ki huta zamuyi magana an jima kafin lokacin shiri yayi" to kawai Amatu tace masa tana wucewa ciki domin ita yau bata jin dad'i sosai zazza'bi ne yake neman rufeta tana shiga bedroom kwanciya tai taja bargo dan har taji sanyi ya mata kad'ata kallonta Maryam tai "Amatu yada kwanciya"? Kaita d'aga "eh bana jin dad'i ne".

"Ok Allah ya sauwake amma da kin tashi kinga la'asar fa tayi idan an Kira sallah saiki kwanta" "eh zam tashi wanda nake son maybe hakan zaisa naji d'an dama dama zazza'bi keson kamani".

"Subahanallahi Amatu zazza'bi kuma Bari naiwa ya Ahmad magana yazo ya duba ki".

"A'a karki kira shi ban tabbatar ba tukuna sanyin da nakeji ne ga jikina yai zafi" tun kafin Maryam tayi maja Ikram taja tsaki tana jan hannun Maryam tace.

"Ke dan Allah zo mu tafi yar rainin hankali wai tazo birni ta waye sai wani wahalar dake take wai ita ga maamaa kema kina biye mata muje share ta" murmushi Maryam tai tana dafa goshin Amatu da gaske jikinta d'au yake da zafi kamar wuta kai ta jinjina tana cewa.

"Amatu zazza'bi man kike bari na kirashi" fita sukai Ikram sai harararta take tabe baki Amatu tai tana gyara kwanciyar ta tace "wannan budurwar akwai yar jin kai amma babu komai ina daidai da zamaninki wallhi ba kyaleki zanyi naga take-takenki nima zan fito miki cikin kalata idan ba haka nayi miki baza mu zauna lafiya ba baki isa raina niba dan daga 'kauye nazo".

Bayan sallar magriba suka fara taruwa a harabar gidan inda zasuyi 'kauyawa kowa yayi shiga kayayyaki komai daban-dabam harda amarya Lailah tasha had'in gambiza da tawagarta daga gida dubu ba shigar wanda tafi hargitsa ba'a ci dariya an more har ciki yai ciwo ba saida ango yazo da abokansa riga daban wando daban takalmin 'kafarsa d'aya fari d'aya ba'ki silifas da combus😂😂 ga d'aurin kara a wuya🤣🤣innalillahi wai maimakon a d'aure a d'auko aka shine suka d'add'auro shi a wuya sun datsa shi 'kanana yadda zai dadi daurewa ansha dariya fuskar amarya Lailah tasha kwalliya da bakin kwalli idan ka ganka birad'al kamar ka gudu ga takalma an zurasu a jikin gyale kowa ta d'aure a kugu ga kuma sandunan rake ana sha 'kawayen amarya kuma sunyi d'an malele yasha manja da yajin maggi😋😃 sun yanka albarka da cocumber abun dai sai wanda ya gani 'kauyawa party yayi kyau ansha dije sosai an girgije dama Ahmad yace kunyarsa galan d'aya ce kuma ranar aurensa zai tintsirar dashi haka ne kuwa ya faru ya gyagiye ba laifi kalangu ya daku a gurin makad'i sai kusan karfe goma ta dare suka koma gida sannan Amatu ta dad'e dayin barci domin bataje ba zazza'bi ya hanata zuwa.

Washe gari tun wuri gida ya sake cika Binta ma tazo tare dasu Aisha harda Saude da A'i Amatu tayi farin ciki ta 'kara ganin ahlinta anan Binta take fad'a mata malam Habu ya tashi sun tafi neman kud'i tare da Sadi tuni murna ta sake lullu'be ta harda hawayenta ta d'aga hannu tana rokar nasa samun abinda yaje nema duk sai taji zazza'bin nata ya warke da Binta ta mata wannan albishir mai dad'i.

'Karfe hudu aka d'aura auren Ahmad da Lailah a babban masallacin sallar idi da yake wajen gida dubu bakin Ahmad kamar zai yage😂 tsabar murna bayan an gama daurin abokan sa sai taya farin ciki suke suna bashi hannu haka da suka shiga gaisuwar iyaye Ahmad ba kunya harda 'kara jawo Lailah jikinsa a gaban mutane sukai photuna kafin zuwa yace ta sanar da 'kawayen ta dinner nan da 'karfe biyar a moderling event center🌆.
Chapter 66 · 0% Book details