← Book details Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 145

Sashe 88

Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta'be baki Hassan yai shima jin yadda Ilyan ya kamo wani shafin da ba zancen suke ba yace "batun aurena da Amatu nake maka maganaa akai ba gini ba in a ruwana da gida idan zan gina bana bukatar taimakon ka koda bulo daya ne zanyi da kaina nidai damuwata kaje mun ro'kon arziki sonake a had'a bikinmu dana wannan shegiyar 'yar taka Nafisa idan kuma ba haka ba wallahi saidai itama a fasa natan sai lokacin daka amince da namu idan ka'ki zamu Bari sai saurayin nata yazo mu tumurmusa shi agabanka muyi masa tsinannan duka mu faffasa masa glass d'in motarsa sai naga ta tsiya haba idan banda gidadanci anace maka ga gabas kana ga yamma ana ga ruwa kana ga wuta kodan bari na sake maimaita maka watakila kud'i ya fara susutar maka da 'kwa'kwalwa cewa nai magana nake maka akan Amatu yar gidan kawu Habubakar gashi ta dawo so nake na aureta mubar nan garin nan ya isheni kandin kifi zanyi daga ruwa na koma mai Ina aurenta zaka nemi ni ka rasa nayi can zanje na bud'e sabuwar harka da sabuwar duniya yanzu Ina tunanin ka fahimta tunda nayi maka magana da yaren da zaka gane"?.

Takaici ne da ba'kin ciki suka rufe Ilyah yana kallon Hassan zaiyi magana Hussaini yace "yauwa Hassan fad'a masa dai baba Nima dai ta Hassan d'infa Ina maganar auren mu akan Aisha ta kwana domin gaskiya na matsu nayi aure kuma dai rana d'aya zamu bar nan kawai yanzu ka tashi muje tunda ga kud'i nan a gabanka kamar yayi kawai ka mike muje tare guri kawu Habubakar yanzu ayi neman auren nan a gabanmu tunda kawu Habun babanmu ne ba surukin muba".

Mugun had'e rai Ilyah yayi yana kallon su cikin 'bacin rai yace "wallahi babu inda zanje nemawa kowanne shege a cikin ku aure tunda baku da hankali baku mayar dani komai ba ai na dauka zaku iyayin auren batare da neman shawara taba sai kuje kuyi naga da yadda zakuyi d'in shashashun banza mahaukatan wofi wannan ba'kin cikin da kuke sani saikun gani kuma a 'kwaryarku".

Kallon juna sukai suna ta'be baki jin abinda yace kafin Hassan ya jinjina kai yana cewa "Aiko wallahi baba tunda kace haka zakaga yadda akai tijara mun shiga birni mun waye ba wani so'ko'kon dazai fad'a mana wayewa a garin nan banda matata Amatu Dan haka ko alkali sai munje ya d'aura mana aure dasu kuma zaka gani Hussaini zo mu tafi dan idan naci gaba da tsaiwa anan yadda baba yake karanta min wannan gidadancin zan iya wanka masa mari😲😳 mu tafi kawai na daina ganinsa kafin na fusata".

Dariya Hussaini yai ganin yadda Ilyah ya zaro ido sai kawai ya du'ka yana d'aukar d'aurin kud'i guda daya a jikin 'kyaro yace "wannan zaikai dubu hamsin Dan haka mun d'auki kud'in zance nida Hassan yau kaine zaka biya mana kud'in hirar da zamuyo" yana fad'in haka suka wuce muryar illyah na rawa kamar zai fashe da kuka yace.

"Hussaini ka dawo min da kud'in nan Kona tsine maka"?.

Waigowa Hussaini yai yana cewa "tsine min d'in mana idan ka tsine min nabi duniya wayai asara bayan kai ka rasa" yana kaiwa nan ya juya da sauri yaci gaba da tafiya dan Hassan tuni har yayi masa nisa bai tsaya sauraron maganar ilyan ba.

GIDAN BALARABE
Asabe dai fatan ta baici ba yadda take so bai samu ba da fari boka yace mata aiki zaici harta kwantar da hankalinta akan wannan batun ta manta ma da wani ilu sai gashi kwatsam rana tsaka taga su Inna sun sauka a gidanta da asubar fari😂 da Dan d'aurin kayansu kamar yadda suka zo a lokacin Indo tashin hankali ne 'karara ya bayyana a fuskar asabe wanda batasan sanda tad'au tabarya ta bisu da ita ba tana surutai a layi tayiwa su Innah korar kare fata-fata ta'ki kar'bar ro'kon arzikin Iluh kuwa daya fita tantiranci suka had'a baki shida Bahijjah ya rakasu gidan Markah yace Asabe ce tarosu wai ta kar'bi ro'kon arziki domin tana jin kunyar Bahijjah 'yarta ce ta fari Markah kuwa tayi kiran Mairo suka kar'bi komai tare Asabe batasan komai ba sai kusan kwanan ashirin da biyar a jita-jita taji wai-wai ana tayata murna a anguwa wai ashe auren Bahijjah zatai zata bata Iluh d'an garuwa jin abinda aka cewa yasa a hargitse tayi gidan Markah kamar zata tashi sama taje tana kwala mata kira tun daga layi harta shiga gidan ta ri'ka Danna mata zagi da masifa iri iri akan me zatai Mata haka dama tace ta kar'bi kayan wadancan tsinanun mutanen Markah kuwa ta nuna Mata ai itace ta turosu nan din dan Bahijjan ma haka tace ita da Iluh Asabe tayi kuka tayi ba'kin ciki da kiran ta shiga uku ta lalace Markah tace Mata kawai tayi ha'kuri tunda har anyi haka ta dangana ta ha'kura karta hana auren ba'a san me yake 'boye ba jinya kam Asabe tasha kamar bazata kai labari ba kuma dole ta warke saidai fa damuwa ta dama Mata 'kwa'kwalwa ga kuma hawan jini da ciwon zuciya rai da rai tana tare da magani a kusa da ita😣😞.

Allah sarki Malam Habu masu kar'bar kaya sunzo babu komai a gurin sa haka dole yasa hannu a takarda akan cewa gonarsa 'yar guda d'ayar da yake nomawa yanzu babu ta zama tasu yayi juyayi yayi bakin ciki ya kara dole ya dangana ya ha'kura yasan Allah ne ke bada komai kuma shizai bashi wata.

Hassan da Hussaini suna zaune a irin dabar samarin gari hangowa Ilyah sukai yana ta sauri yayi layin wajen gidan malam Habu yana tafe kamar zai kifa hada ido sukai da sauri suma suka mi'ke suna bin bayansa da gudu ba zato yaga sun sha gabansa cikin haki Hassan yace.

"Baba Ina zakaje haka kake sauri kamar zaka tashi sama"?.

A fusace ilyah yace "ban sani ba bani hanya".

Gira Hussaini ya d'age yana cewa gidan kawu Habubakar zakaje ko wato har wani ba'kin tsinannan munafikin yaje ya fad'a maka munyo masa cefane da kayan abinci a kasuwa ko shine kai kuma ka d'ebo qafa saboda baka juri zuga ba kayo gidansa da ba'kin ido so'ko so'ko🙊 ka taho gurin sa kazo ka tada masa hankali ko? to wallahi baza kaje ka tada masa hankali ba dan nasan akam wannan kayan abincin ne saboda bamu saya mun kai maka ba kana ubanmu mun kaiwa surikin mu shine zakaje ka tada qayar baya haka ne"?.

Cikin takaici Ilyah yace "inji ubanka nace maka haka Ina ruwana da wani shege abinci da kuka kai masa shine mitsiyaci mayunwaci😣 amma bani ba shine fa'kiri talakan talakawa shi yake bu'katar abinci bani ba".

Kai Hassan ya jinjina yana "To indai kasan ba abinda zai kaika ba kenan ka koma gida yanzu".

Muryar Ilyah da fushi da yadda suke bashi umarni a fusace yace "Bazan koma ba dan uwarka ka komar dani idan ka isa yau sainaga wanda ya tsayawa Habubakar a garin nan" ya fad'a yana shirin wucewa had'a ido sukai suna jinjina kai tare da tareshi suna d'aukarsa sukai hanyar gida dashi yana wutsul wutsul basu damu da yadda mutane suke kallonsu ba haka suka wuce dashi ana binsu da kallo ana gulma saida suka kaishi har kofar d'akinsa sannan suka direshi suna huci shima yana yi.

Ganin Ilyah d'auke a hannunsu sun shigo gida yasa daga manyan har 'ya'yan kowa ya fito jin Bara'atu tana salati sun d'auka ba lafiya ba.

Cikin alamun tambaya Maimuna tace innalillahi meya sameshi haka Hassan ko fad'uwa yayi a waje naganku kun rirri'koshi daga Ina dama baida lafiya ne"?.

Kad'a kai Hassan yai yana cewa "kalau umma Maimuh d'auko shi mukai a hanyar gidan kawun mu Habubakar wai saiyaje ya gargad'e shi akan dan muna son 'ya'yansa".

Jin haka yasa maimuna taja bakinta tai shiru ko tari bata 'kara ba duk da tana mamakin meyasa Ilyan baya so su Hassan su auri 'ya'yan 'kanin nasa kodan ya furta cewa talaka ne fa'kiri......

Kai Bara'atu ta jinjina cike da takaicin halayensu tace "anya ku mutane ne Hassan Hussaini Ina gargad'inku fa ubanku shine abun wulakancin ku kubi duniya a hankali".

Kau dakai Hassan yai yana cewa "wallahi umma nikam yanzu na fara tara tsinken tsikarar duniyar ma🙊 kinga ko taya zan bita a hankali gara na bita da gudu zamufi daidaitawa da kowanne so'ko'ko😳" A'A AN SHIGA 'DAKA JAMA'A ILYAH FA YA HAIFO RUWAN DUHUWAR KANSA😭.

Wani irin Sar'kekken numfashi wanda ya kusa tafiya da bugun zuciyarta Bara'atu ta sauke tana kallon su kamar ta d'ora hannu aka ta fasa ihun damuwa ko zasu fahimci halin da take ciki zatai magana Hussaini yace.

"Ai Hassan 'kyale ta na rasa wacce irin 'kwa'kwalwa gareta data kasa fahimtar inda muka dosa amma zamu ganar dasu dan wallahi ko hannu bamu saba a fara tara tsinken tsikarar duniyar ba saima nan gaba sannan munyi aure suna kallo zamu shiga duniyar nishad'i kuma mu d'ebi nishad'i yadda ya kamata a gabansu da 'ya'yan kawu Habubakar babu ruwanmu da mutum yana gurin saidai ya rufe idonsa ko yai bunga🤥 wannan matsalar sace muje kawai Hassan sharesu" ficewa sukai a gidan suka bar Bara'atu a tsaye ta qame guri daya kamar sanda ta rasa meyake damun wadannan yaran ace sam bakinsu bai mutuwa idan ka fad'a musu cuta sai sun fad'a maka mutuwa haka Ilyah ya shiga d'aki yanata share hawayen ba'kin ciki shima.

MRS AL'AMEEN AHMAD CE😘.

Yusrah Musa Abubakar YUSEEN AL-AMEEN🏖️.

Much appreciated masoya💕tnks for ur supports💃 Allah ya barmu tare amin.

Nagode a bisa nuna kulawa da qaunarku ga littafin nan da kuma lambar yabo da kuka bashi Allah ya saka da alkhairi 🙏🤝.

YÚSRÃH MÛSÃ ABUBAKAR💋
[email protected]

TYPING 📲 wed Aug28/24 YUSRAH MUSA ABUBAKAR🤝.

💦🤟ME KAMAR SÄRKÌ💦🤟

________________________________
________________________________
________________________________
___________________
💫 ANNUR WRITER'S ASSOCIATION💫
Home of hospitality and harmony 🤙gidan karbar mutane hannu biyu da zaman lafiya🙅 ÀÑÑÙRÌ haske le'ka gidan kowa koda ma'kiya na kallon ka ramin kura sai'ya'yan ta.

FATIMA SHAMSUDDEEN
RAMLAT IBRAHEEM
RU'KAYYAH KABEER.
👇Wannan 📝page d'in naku ne duka mallakin ku 'ya'yana🍎 na kaina kuna farin cikin Yusrah ababen son Najaat muradin Zarah d'an Adam🤟.

59~AL-MU'IDU
The Reinstater Who Brings Back All
60~AL-MUHYI
The Giver of life.
Chapter 88 · 0% Book details