← Book details Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 145

Sashe 11

Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da mamakin ganinta da katon kwano yasa malam Habu cewa "mama na daga ina"? Ya mata tambayar ne duk da shima yasan daga inda take kuma yasan ba kwanon gidan Ilyah bane saukewa tai a gaban sa tana zama kusa dashi tace "baba Rakiya ce ta bani na kawo muku" ta karasa maganar tana bud'e murfin kwanon fuskar malam Habu da fara'a yace "Aiko Allah yaiwa Rakiya albarka ya bata abinda take nema duniya da lahira kamar tasan a yau banci komai ba tun safe haka na wuni"😔 kallon sa Amatu tai jin abinda yace sunkuyar dakai tai saiga hawaye shar yana zuba a idonta da sauri ta mike tana shiga daki ta dauko kwano tazo deba masa tana ajewa gaban sa tace "baba kaci" kallon ta sosai malam Habu keyi cikin tausayawa tare da ri'ko hannunta yace "Mamana ki daina kuka kinji komai yai farko zaiyi karshe insha Allahu bazan tabbata a haka ba" kai ta d'aga tana daukar sauran ta kaiwa umma kafin tadau kofi ta debo ruwa mai sanyi a randa tana ajewa malam Habu daya nade hannun riga yana kai lomar tuwo sai kallon sa kawai take tana share hawaye tuna abubuwan data gani a gidan baba Ilyah ya tanadarwa ba'kin sa ga d'an uwansa jini daya uba daya amma ya'ki taimakon sa............

Muryar A'i ce ta dawo da ita daga d'an gajeran tunanin da take kallonta tai tana zaune kan kujera a bakin kofar d'akin ta sai cewa take "haba da Allah malam kaji fa wani irin tuwo me mugun dadi amma ace kullum daga gero sai gero ni Allah Allah nake ma dawa tazo mu huta da wannan 'kuncin kullum girki iri daya babu canji kaga kaima malam yadda ka karkace hula kana aiki amma ka noma shinkafar a gonar ka ka'ki kodan ina kaga gonar wata miyar sai a ma'kota" ta tafar sauke ko ci kanki malam Habu bai ce ba sai Amatu dai da take ta jin d'acin maganganun A'i.

Fatima na shiga gidan su Dalah tai turus ta tsaya ganin yadda Balarabe ke surfa bala'i ga Indo
a gefe ta kifa kai tana kuka Asabe data fito a d'aki cikin tabe baki tace "yo ai malam wannan kaso kanka iya dan dukan da zakai mata kenan ni na dauka zaka karya mata 'kafar da take zuwa kwartancin da ita ai anzo har gida an fad'a ranar talatar data wuce karfe sha d'aya na dare wani me mota yazo ya sauketa malam idan bakai a hankali ba Indo zata fi karfin ka kawai ka aurar da ita kafin ta jawo maka abin kunya" cikin fad'a Balarabe yace "to wa ma zai sota a haka kalli fa duk kowa yasan tana bin maza nidai ba gado na kikayo ba saidai dangin Dalah kuma wallahi bari kiji duk ranar da tsautsayi yasa kikayo cikin shege saina kashe ki a gidan nan".

Dad'i ne sosai ya kama Asabe tana kallon Dalah datai tagumi tace "ai malam ga shawara kawai yau da asuba bayan anyi sallah a masallaci ka fad'awa liman ya sanar kana da 'ya zaka bada ita sadaka ka wanda keso sadaki kawai zai biya" shiru Balarabe yai a zabure Asabe tace "tunanin me ka tsaya yi ko shawarar tawa batai ba nasan tayi saidai kace baka so" da sauri Balarabe yace "a'a shawarar ki tayi zanyi hakan yanzu bari na fita majalisar mu shima malam Habu muyi wacce zamuyi ya karasa maganar yana yin kofar fita yana tafe yana magana shi kadai kamar ta'babbe la'bewa Fatima tai tana jiran Saida ya wuce sannan ta shigo gidan da sallama hankalin ta nakan indo wacce har lokacin kanta yake duke tana shar'bar kukan damuwa da takaicin 'kuncin rayuwa.

Kanta taje ta tsaya rai 'bace tace "Indo" da sauri Indo ta d'ago ganin Fatima yasa cikin kuka tace "Fatima me naiwa mutane ne meyasa bani da farin jini kamar wacce mujiya ta a ina fatan mutuwa a wannan lokacin da rayuwa ta" kai Fatima ta girgiza cikin tausayawa tace "a'a Indo kada kiyi sa'bo ki dauka hakan kaddararki ce kiyi kokarin cinyewa sai ki samu mafi alkairin sa".............

Asabe ce ta katse su da cewa "ke munafika uban me kika zoyi gidan mutane"? Ko inda take Fatima bata kalla ta d'ago Asma'u y suka shiga d'akin Dalah mikewa Dalah tai tana bin bayan su sakin gud'a da shewa Asabe tai tana rawa "ahayye nanaye ayuriiiiiiiii abun yazo kaga munafikai zaku fito ne kome kuke kitsawa to wallahi nidai nafi karfin ku idan ma ku mayu ne kurwata tai muku nisa nama na yai muku daci kuma Dalah kisa ido ki gani saina hana ki shan ruwa a gidan nan muje zuwa daya Kenan kuma idan akai munafirci na ban yafe ba" d'aki ta juya tana rera wakar munafirci kunun kanwa uwarku ta fara damawa.

Ba'kin Ilyah sun sauka lafiya kuma yai musu kyakkyawar tarba jiki na rawa daga shi harsu Bara'atu sai son yin gwaninta suke wannan karon Kam Nafisa kwalliya aka yi aka sa kayan 'kure ajiya itace mai kai musu komai idan ta ajiye saita kalli fuskar saurayin dake gefe amma shi ya'ki d'agowa ya kalleta sai zuwan karshe ta mike zata tafi gyalen ta ya zame ya hango breast dinta Dan lumshe ido yai ya sake budewa akan fuskarta daidai ta d'ago suka hada ido ya sakar mata murmushi mamaki ne ya kamata da sauri ta fita yayin daya cire lips dinsa yana sake bin kofar da kallo.
Nafisa kam na fita da gudu ta karasa d'akin su tare dayin tsalle ta haye katifa tana fasa ihu a firgice Salma dake bacci ta farka tana kallon ta tace "lafiya meya faru kike ihu"? Dariya Nafisa tai tana cewa "ke Salma albishir dinki wannan zuwan anzo da wani saurayi naga sai kallo na yake yana murmushi watakila Sona yake kai wayyo Allah, Allah yasa da gaske ne dan ina matukar son zaman binni kinsan da dad'i kalli fa su yaya Hassan tunda suka tafi kin jisu shiru suna can suna jin dad'in su" tabe baki Salma tai tana cewa "umh umh fa kinga Nafisa ki kiyayi kanki yan binni wayo garesu wallahi kada ki saki jiki dashi ya saki kuka wata rana nidai na fad'a miki" had'e rai Nafisa tai tana hararar Salma tace "kinga goggo Salma idan bazaki bani karfin gwiwa ba kada ki karya min zuciya mu tsaya iya haka nikan yayi min ina son shi" cikin haushi Salma tace ai saiki je ki fad'awa baba ya aura miki shi inga karshe rashin kunya" gyara zama Nafisa tai tana cewa "meye abun rashin kunya bayan na gani ina so kinga kema ta dalili na zaki shiga binni kiga yadda yake" mikewa Salma tai zata fita a d'akin tace "Allah ya kiyaye kema dan bakisan ciwon kanki bane ina fata ki gane da wuri" shiru Nafisa tai tare da bin kofar da Salma ta fita da kallo saidai tafi tunanin ko Salma kishi da hassada take mata.

Tana nan zaune har Salma tayo alwala tazo zatai sallah ita kuma sai powder data kara daukowa tana sake fante fuskarta Salma na shigowa Bara'atu tai sallama tana cewa "ke Nafisa kizo baban ki na Kira baki zasu tafi an gama loda kaya daya daga cikin yace yana son zakuyi magana Allah yasa yace yana sonki ki fita zakka a kauyen nan ki auri dan binni mai kud'i" jiki na rawa Nafisa ta mike tana fita cikin zumudi bayan Salma ta shafa addu'a ta juyo tana kallon Bara'atu tace "amma umma wannan fa kuskure ne take aikatawa ya daga ganin mutun ba sanin sa akai ba kawai tace zata aure shi tasan halinsa ko baba nasan baisan komai game dasu ba iya kaci suzo da kud'i ya siyar musu Kaya su tafi dan Allah umma ku tsaya ku duba" wani kallo Bara'atu tai mata tanacewa "ke jimin yarinya da shishshigi me kike nufi dan kawai yazo daga binni kuma yace yana son ta saimu 'ki amincewa dashi"? "Eh ina tunanin abinda zaije ya dawo ne kuma ku idan yace zai aureta zaku bashi ne"? "maizai hana zai kashe tane"? Kai Salma ta girgiza "Amma umma a tsaya ai bincike kafin a amince masa" kallon ta Bara'atu tai "kinga Salma saurara meye damuwar ki ke ba kince kinfi son zaman kauye ba to saiki kyaleta itakam sai rayuwa a maraya" shiru Salma tai bata sake cewa komai ba itama Bara'atun haka.

Da sallama Nafisa ta shiga d'akin ba kowa shiru saishi zama tai dan nesa dashi yana kallon ta yace "barka da wannan lokaci kyakkyawa a gaskiya kin iya kwalliya kallon ki yasa na kasa furta kalma daya amma dai zanyi miki tambayoyi uku ki bani amsa, na farko mene sunan ki"? Ya fad'a yana kafeta da ido duk jitai ta takura da'kyar tace "Nafisa" a bakin shi kamar shine ya rad'a sunan ya maimaita "oh Nafisat nice ne, tambaya ta biyu kinji nai miki kina sona? tambaya ta uku zaki aure ni"? Ina jiran ki amsa hajiya Nafisa kece mace ta farko da naiwa kallo d'aya naji na kamu da cutar sonta kuma ina fatan kema zaki amince min"?.

Zaro ido tai tana kallon sa tace "da gaske sona kake"? Kai ya d'aga mata "eh sonki nake irin ainun dinan fatan kema haka kina yina"? Cikin wawanci ta fara dariya wanda shi mamaki ma yasa ya tsaya kawai yana kallonta saida ta gama yace "yadai kiban amsa zamu tafi jira na suke" ko kunya balle kara haka Nafisa tana kallon idanuwan shi tace "eh ina sonka kuma zan aureka domin ba abinda nake so kamar zaman binni" wani kallo ya mata to maye abin son zama a birnin ko'ina ba gurin rayuwa bane gira ya dage tare da mikewa yace "shikenan to nagode da so zamu tafi" itanma mikewa tai suna fita tare saida tai masa rakiya har waje ya shiga mota suka wuce Ilyah sai yan'kare baki yake yana annaahuwa ganin dayai Nurain ya nuna yana son Nafisa yasan yanzu zai sake zama me dukiya fiye da da idan ya samu ta aure shi.
Chapter 11 · 0% Book details