← Book details Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 145

Sashe 106

Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

washe gari ma saida suka wuni suna shishshirya mata abubuwa da suka gama sukai wanka bayan la'asar Nurain yasa drivern Daddy yazo ya daukesu domin ya mayar dasu gida haka suka bar Nafisa ko d'an irin jin kewar nan babu itadai kawai tazo birni shine abinda ranta ya d'auka kuma idan ta tuna take jin girman Kai ya hauta.🤔

Misalin karfe takwas na dare Nafisa anci wankar taryar ango an bad'a kwalliya a fuska pawder tayi fau kamar biri🐵 an fesa turare anhau gado an lullu'be jiki da mayafi ana jiransa ya shigo tana zaune shiru shiru taji an bud'e kofa an shigo ta d'auka shine harda sake gyara rufe mayafin zuwa fuskarta tana murmushi yau gata ga Nurain sunyi aure a birni wani irin dad'i ne taji yana ratsa ta har tana lumshe ido a ranta tace yanzu lokacina zai fara daga yau zan bud'e sabuwar rayuwa..........................

Katse mata maganar zucin da take akai da cewa "hum'um kan bala'i lallai ya Nurain ya fad'o yanxu mine abun so a village girl harzai aurota yasa a gidansa heyeee ke madam 'kwas-'kwas bud'e wannan banzan mayafin naki ki kallemu sannan ki bud'e kunne ki saurare mu munzo miki da wasu maganganu ne".

Bud'e mayafin Nafisa tayi tana kallon su cike da mamaki tace "su waye ku"?.

Wata iriyar ba'kar harara tai karo da ita daga dukka su hud'un kafin Mimah tace "oh wai kina nufin baki gane muba humm to bari na miki bayani wannan uwarki ce wannan ubankice wannan kanwar ubanki ce ni kuma kanwar uwarki ce yanzu kin gane mu? kiji min shegiyar yarinya fa Meelat wai har tambayar mu take suwaye mu"?.

Tsaki meelat tai tana cewa "ke kika tsaya yi bayanin mu suwaye maiyasa data tambaya baki kifeta da mari ba wanda azaba zata sa ta gane yaren da kike nufi domin wannan akuyar tana bu'katar dusa but not now mubari zuwa gobe zaki bayani barka da shigowa kabarin ki kuma lahirarki ke da'ki'kiya fatan kinzo da likafani? Idan baki zo dashi ba kisa ya Nurain ya sayo miki gobe kuzo mutafi kada yazo ya same mu muna nan kuma tsautsayi yasa ki fad'a masa cewa wasu 'yan mata sun shigo gunki humyim wallahi gobe saimun canza miki halitta".

Kallon Mimih dake tsaye Mimah tai tana cewa "ke baki magana ba ko sai goben"?.

Kai Mimih ta girgiza tana kara dukawa akan Nafisa tare da sake bud'e mata dukkan girman idonta kafin tace.

"Unbelievable sannu amarya ya kike ya gida"?.

Da mamaki sauran suka kalleta Meelat da hartaje bakin kofar fita da sauri ta dawo tana cewa "Mimih me naji kince mata sannu amarya humm tofa ashe zata samu shiga ta bangaren ki ko"¿.

Cizon yatsa Mimih tai tana jin kamar ta d'aga hannu ta kwad'awa Nafisan mari kafin tace "heeeyy tabd'ijan dan'kari anan ake bele'u kuturun ubancan yanzu ya Nurain duk kyansa da jin kansa amma ya haure city ya tafi can wani dabban stupid d'in qauye yaje ya auro wannan ba'kar jahilar yasata a cikin familyn mu ta haifa mana da'ki'kan yara munana irinta hum'um kalleta da Allah wai amarya guda amma babu suturar arziki kalli wani banzan jakin lalle a kafarta wannan tsaya da saltif sukai ne ko kuma tsabar kauyanci haka aka dam'bara lallen? kutumelesi kiji wani wani kafurin d'oyi🙊 babu d'an kamshi da yake tashi na amaren nan sai tsamin kanta ke buguna tayi kitsone ma wannan jakar kauyen"? Ta karasa maganar tana fisge kwalin dake kanta a d'aure kallon 'kyama taiwa kan tana shirin 'ka'karin amai tace.

"Subahanallahi kai ku muje wayyo zan mutu da wari" ta karasa maganar tana fifita hancinta da hannu.

Ri'ke kunnenta Meenah tai cike da kishi da tsana tace "oh wai dama akan wannan ya Nurain ya rud'e ya mayar da hankalinsa qauye har saida ya aureta ya samu nutsuwa tabbb na rantse da Allah wannan kazamar yarinyar ko 'yar aikin gida bazan yarda a gidanmu a d'auke taba balle wai mata matar ma ta ya Nurain anya ya Nurain kansa d'aya kwakwalwar sa bata fara ta'buwa ba gaskiya ya kamata ya je hospital a duba shi domin wannan tsinanniyar ko 'yar goge takalminsa bata kai ba" ta karasa maganar tana hankad'a Nafisa baya ta fad'a saman gado.

Tsaki Meelat tana cewa "Humm kema dai kya fad'a Meenah gadaita nan a gashe ba mai'ko a dafe ba moro zataci ubanta ne damu take wasan badai kin aureshi ba? zaki bayani" Mimah kuzo mu tafi dan idan naci gaba da tsaiwa wannan tinkiyar ba'kauyiyar zatasa nayi aman fruit salad🥗 dinan da muka ci yanzu" tana rufe baki ta dunguwa Nafisa goshi kafin suka fice daga bedroom d'in.

Tsumu-tsumu Nafisa tai tana zaro ido waje kamar zata fashe da kuka ta shiga uku🙆 daga dirowarta garin tazo da farin ciki wadannan kuma su waye zasuzo su d'aga mata hankali daga ina suke waye ya turosu? Wannan tambayoyin sune fal ranta ta rasa yadda zatai gashi harsun hautsina mata ciki rasa inda zata sa kanta taji dad'i tayi saidai ta juya can ta kalli nan har Nurain ya shigo sai sannan ta d'an samu nutsuwa shikam baisan meke faruwa ba sai baje mata baki yake yana kallonta itakam saidai tayi masa murmushin ya'ke gashi sun gargad'eta akan kada ta kuskura ya sani duk wani farin ciki da take ji ya koma ciki haka dai kamar mara lafiya sukai abubuwa.

Washe gari sai wajen karfe d'aya Nurain ya fita shima a bisa dole Yazid ne ya kirashi yace masa yana so dan su had'u yanzu a ina zai sameshi ganin Nafisan barcin safe take yasa bai tasheta ba kawai yayi wanka ya shirya ya fice duk abinda yake su Mimah suna ankare dashi suna jin tashin mota da qarar bud'e gate da rufewa sunsan ya fita kuma Zainab ma tuni ta wuce hospital iya sune a gidan har karo suke da juna sukai part d'inta tana kwance tayi d'ai d'ai akan gado ta bararraje tana she'ka barci harda munshari saboda bata samu tayi da daren ba😉.

Fridge Meenah ta bud'e tana d'auko robar ruwa mai sanyi har ra'ba take ta juyeshi a cup ta d'aga ta watsa mata jiki tana cewa.

"Ke jaka tashi a kwanciyar nan dama barci kika zo dan uwarki harda bajewa kinai mutane gwarci kamar rago" ta karasa maganar tana kware mata sauran ruwan.

A firgice Nafisa ta farka jikinta na kakkarwa tsabar sanyin ruwar kamar mai zazza'bi sai makyarkyata take bakinta na rawa ta kasa magana tana kallon su cikin tsoro.

"Keee uwarki kike kallo a jikin mu"? Meelat ta fad'a tana fisgota daga kan gado ta fad'o kasa Mimah tasa kafa ta take ta tana cewa.

"Ke jiya me muka ce miki dama kinzo hutu ne tabd'i humm aiko yau saikin gwammace baki ta'ba sanin waye ya Nurain ba a rayuwarki".

Dam'ko ta Mimih tai tana mi'kar da ita tsaye tana kare mata kallo kafin tace "kai ku duba min na shiga uku me nake gani yarinyar nan kamar kuka tayi kodai ya Nurain yayi first night da ita😳 "?.

Mimih na rufe baki duk suka zuba mata ido suna qare mata kallo zaro ido Meenah tai tana cewa "kuturun ubancan lallai kam wallahi maganar ki nakan hanya Mimih wannan tsinanniyar ta shigo familyn gaskiya ya Nurain ya qasqantar da ahlinmu yanzu tsakani da Allah matsayin mata yad'au wannan kucakar yarinyar"? Mtswww.

Ta'be baki Meenah tai tana hararar Nafisa tace "hum kema dai kya fad'a Mimih wannan bala'in har ina na rasa me ya gani a jikinta abinso ita ba kyau ba itaba dirarran jiki ba kalleta fa kamar ta'barya ko'ina kai d'aya babu shape saikace gongonin peak milk haba wallahi ya Nurain yana da abun mamaki".

Qwafa Meelat tai tana cewa "kunga karmu tsaya surutai harya dawo bamuyi abinda ya kawo muba ta wuce muje ta fara bautar daya kawota gidan ta wanke mana toilet ta gyara mata bedroom da part d'in Aunty Zainab sannan tayi mana abun breakfast muna tsaye a kanta kuma bata isa ta shiga kitchen ba a garden zatai da gawayi zaki bayani wallahi sai munci uban daya kawoki duniya da kafafunki zaki gudu karkara kuma zaki gani muje dalla gafara akuya kawai" ta karasa maganar tana hankad'a ta da gudu Nafisa tai waje su kuma suka bi bayanta.

MALAM HABU.
________Kamar yadda Hajiya Aisha ta shawarci Alhaji Musa ya samu malam Habu ya fad'a masa bu'katar sa kasawa yai idan sun had'un ma baya iya fad'a masa harsu rabu sai daga baya abin yake damunsa musamman yanzu da suke zuwa kallon Asma'un ta kile sosai ta kara wayewa an zama 'yan birni tuni yaji hankalin sa ya tashi dan haka daya kasa tunkarar Malam Habun sai kawai ya tura abokinsa Alhaji Aminu yayi masa bayanin komai yadda zai fad'awa Malam Habu din sannan duk yadda sukai yana jiransa ya dawo ya sanar masa.

Alhaji Aminu baiyi kasa a gwiwa ba yaje har kofar gidan malam Habu da dare ya zayyane masa komai abinda yake faruwa ya kara masa da cewa Alhaji Musan yace ya tsaya yayi tunani tukuna idan yaga takura dan Allah kada ya 6oye masa ya fad'a zai fahimce shi babu wanda ya'ki shawara dan haka malam Habu yace zaiyi magana da iyayansu mata kome suka yanke zai sanar masa duk da yaji matukar mamaki kuma zuciyarsa ta girgiza dajin batun baya jin zai iya hanawa Alhaji Musa yayi masa komai a rayuwa domin shine ya bashi magani a lokacin da yake tsananin bu'kata ana barin halak dan kunya.

Saboda haka yana shiga gida yayi kiran duk su ukun d'akinsa dansu samu damar tattaunawa yadda ya kamata kuma ya fad'a musu ga abinda yake faruwa sa'kon Alhaji Musa zuwa garesu duk basu goyi baya ba domin maganar gaskiya gani suke idan sunyi haka sunci dinduniyar Hajiya Aisha wacce ta mayar da Asma'un kamar 'yar data haifa babu wanda ya gamsu a cikinsu Shima kuma Malam Habun dama yacewa Alhaji Aminun hakane saboda kada ya yanke hukunci ba neman shawara komai yana bu'katar nutsuwa.
Chapter 106 · 0% Book details