← Book details Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 145

Sashe 36

Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kai Baffah ya girgiza "a'a Sabi'u bazan gani ba ka barshi a haka" sannan ya mayar da kallonsa kan Habu kafin yaci gaba "na sani kun nuna min fitacciyar 'kauna da kowanne d'a zai nunawa ubansa kuma nayi matukar jin dad'in hakan da godiya ta a gareku duk rintsi kada ku bari a raba kanku ko a shiga tsakanin ku kuzama 'yan uwa na gari ku rufa asirin junanku dan Allah kumin alkawarin haka, shin zaku min wannan alfarmar"?.

Ya fad'a yana ri'ko hannuwansu yasa cikin nasa tab Allah sarki kuka suka saka masa cikin damuwa sosai da tausayawa halin da zasu shiga idan aka wayi gari rana ta fito ace babu Baffah a duniya yabar cikin ta yabar zama tare dasu har abada innalillahi wa inna ilaihi raji'un.

Baffah bai hana su kuka ba domin yasan zai rage musu wani rad'ad'i dake damun ransu da rayuwarsu yace.

"Abubakar Sabi'u dan Allah kuyi shiru haka kuyi hakuri kada kusa naji wani iri nima" kai Habu ya d'aga cikin daurewa da jaruma ya goge hawayen fuskarsa yana daukar kofin da Salamatu ta kawo na kunun safe ya zauna a gefen Baffan ya soma bashi Sabi'u kuma na tsaye.

Dr Usman tare da Dr Lukman suka karaso gurin cike da murmushi Dr Usman yace "alhmdllh gaskiya Baffah kayi dacen 'ya'ya nagari masu so da kaunarka suna kula dakai amma abun haushi yanzun nan daga d'akin masu ciwon ciki muke bakiji yadda wani tsohu yake ambatar suna yaransa ba d'aya bayan d'aya yana tsine musu albarka kuma ba rad'ad'in ciwo bace sai tsabar rashin biyayyar su nayi farin ciki ga kaunarku ga mahaifin ku".

Murmushi Baffah "ai likita wadannan 'ya'yan nawa babu kamar su kuma baza a samu ba tunda sukai wayo suka d'ago suka mallaki hankalin kansu basu sake bari na shiga wata matsala ko 'kuncin rayuwa ba saidai in basu sani ba shiyasa bani da fata sai Allah ya basu 'ya'ya jarumtattu irinsu suma su kula dasu fiye da yadda sukai min".

Kai Dr Lukman ya jinjina "gaskiya ne Baffah irin wannan za'a dad'e ana nema kafin a samu dan wallahi nidai ban ta'ba had'uwa da masu kaunar mahaifi da tattali irin su ba".

Baffah yayi matukar jin dad'in yadda doctors din nan suke bada shedar arziki akan su Sabi'u ya sani albarka zataci ga a da bibiyar su da zuriyar su har abada.

"Baffah bari na sake daura maka sauran ruwanka tunda naka alhmdllh gaskiya jikin naka yayi sauki sosai".

Mi'kewa Sabi'u da Habu sukai yayin da Baffah ya koma ya kwanta Dr Lukman ya matso yana saka masa ruwan kafin ya basu takardar maganin da zasu sayo masa da allurai kar'ba Sabi'u yai yana fita dan ya sayo yayin da yabar Habu shi kadai tsaye a gaban Baffah yana ri'ke da d'ayan hannun da ba'a jiki aka d'aura masa ruwan ba.

Idanuwan Baffah na rufe Habu na kallonsa yana karanta masa addu'a lura dayai kamar ruwan ya daina tafiya ya tsaya yasa da sauri ya sake kallon fuskar Baffan tare da cewa.

"Baffahh".

Jin shiru baiyi masa magana yasa ya d'an ta'ba shi yana sake cewa "Baffah Baffah innalillahi wa inna ilaihi raji'un likita likita kawo mana taimako wayo Allah na Baffah".

'Daga hannunsa yai ganin ya saki yasa ya fasa 'kara da gudu yai waje dan kiran Dr Lukman.

Babu irin magungunan anan cikin asibitin saida Sabi'u ya fita wajen can tsallaken titi ya samo daidai zai shigo gate din hospital d'in yaci karo da wani saurayi wanda shima mahaifin sa room dinsu daya da Baffan tararsa yai murya a sanyaye yace.

"Ka sayo maganin"?.

Jin yadda ya masa magana ga fuskar ba walwala yasa jikin Sabi'u na rawa yace.

"Eh na sayo meya faru? Ko ya rasu ne"?.

'Dan shiru saurayin yai sai kuma ya girgiza kai yana cewa "kawai idan ka sayo mi'ko na mayar".

Sabi'u najin haka baisan lokacin daya jefar da ledar maganin ba aguje yai cikin asibitin yana shiga d'akin yaga Dr Lukman da Usman tsaye a bakin gadon idonsu kowa da ruwa ga Habu ya kifa kai yana kuka karasawa yai da sauri yana bud'e Baffah dake rufe yace.

"Likita meya faru ka rufe shi likita karkace min mahaifi na ya rasu kar kace shikenan Baffah ya tafi ya barmu, likita ka fad'a min cewa lafiyarsa kalau bacci ya samu".

Shiru Dr Lukman yai tare da sunkuyar da kansa kasa ya kasa fuskantar Sabi'un balle ya ce masa 'kala.

Innalillahi wa inna ilaihi raji'un durkusawa a gurin Sabi'u yai yana fashewa da kuka na ban tausayi shikenan Baffah ya musu nisa shikenan Baffah ya rabu dasu har abada shikenan Baffah ya tafi ya barsu da kewarsa.

Kasa basu baki Dr Usman yai sai fita dayai yana sanar da cewa a kira masu motan daukar gawa zuwa kauyen su.

Dama haka rayuwa take yau mune gobe ba mune ba Allah ka bamu cikawa da imani Amin.

Sabi'u ko Habu babu mai karfin gwiwar iya tafiya da 'kafunshi ma balle ya iya wani abu saka Baffah a mota da komai su Dr Lukman ne har lokacin suma basu daina sharar hawaye ba haka suka dauko hanyar kauyen su cikin dagulewar lissafi har kofar gida.

Nan gari ya kaure da salati da koke koke mutane sai tittid'owa suke cikin gida ya cika kofar gida ma har akai masa sutura aka fito waje cikin makara aka sallace shi tare da daukarsa zuwa ma'kabarta.

Hankalin Habu bai sake mugun tashi ba sai lokacin daya d'aga hannu suka fara zubawa Baffah 'kasa wasu zafafan hawaye ne masu tsananin 'kuna suke zuba a idanun sa kansa na juyawa yana ganin duhu da'kyar suka kammala akai masa addu'a suka baro ma'kabartar sun d'an fara tafiya Sabi'u ya farga baiga Habu ba a tare dasu da sauri ya waiga baya can ya gano shi dur'kushe gaban 'kabarin Baffah bai taso ba, da sauri ya koma yana d'ago shi tare da share masa hawayen dake zuba baice komai ba ya ri'ko hannun sa suka fito suna bin bayan sauran mutanen gari har aka dawo kofar gidan tare da shimfida manyan tabarma na zaman kar'bar gaisuwa amma abun mamaki duk abin nan da ake Ilyah kamar bai damu ba haka yake harkokinsa.

A ranar Musbahu da matarsa suka zo suma sunyi kuka sun jinjina mutuwar sun kara saida akai kwana uku suka koma gida yayin da aka bar yan tsirarun mutane wadanda zasu zauna sai anyi bakwai.

Abinda ya baiwa kowa mamaki tun ranar sadakar uku Ramatu ta soma maganar rabon gado da farko kowa yayi tunanin ko mutuwar Baffah ce tasa mata ta'bin kwakwalwa ta zare sai aka barta a haka amma me ranar sadakar bakwai ma Saida tai batun a gaban liman cewa a raba gado tunda yanzu babu Baffah idan ba'a raba kowa yasan matsayin sa ba baza ai zaman lafiya ba dole tasa Saida liman ya amsa mata dan haka ta dameshi zuwanta gidansa uku cikin wata daya da rasuwar Baffah cewa har yanzu taji shiru dan haka yace ta jira zai magana da manyan gari da shedu zasu zo sannan fa ya samu ta 'kyale shi liman kuma akwai abinda yake dubawa musamman 'ya'yansa Sabi'u da Habu yana jin kunyar tararasu daga rasuwar ubansu ko zafin mutuwar bai gama barin jikin su ba a tsiro musu da zancen wani rabon gado.

MRS AL'AMEEN AHMAD CE😘.

MAMAN LITTLE ZARAN AUNTY 💃🎶🎵🎻.

Sai mun sake had'uwa gobe masoya idan me duka ya kaimu da nisan kwana godiya 💖 nake sosai da nuna kaunarku gareni Allah ya kara barin mu tare Amin.

YUSRAHMS ABUBAKAR TA KOWA CE🤗🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹.

TYPING 📲 {Tue, Apr2/24 8:00} ¥usrah Musa Abubakar.

💎ME KAMAR SARKI 💎

Story and written by
✍️YUSRAH MUSA ABUBAKAR Mrs Al'ameen Ahmad ce.

Wannan page din naku ne iyaye masu girma daraja da kima Allah ya kara tsawon rai da shekaru irin dad'ewar dabino👏🌴.
Maman mu
Maman Huzaif
Umman Basiru
Umman Suraj
Umman Fati
Umman Usman
Maman baby
Maman Fadilah
Maman Maryam
Maman Hafeezah
Maman Feedow
Maman Shamsuddeen.

🥀 Always be watchful don't take risk don't try to get lost try to protect your life always.

13~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Qaiminah.

25~AL-MUDHILL
The giver of dishonour
26~AS-SAMII
The All hearing

🌄BEWITCH ND BADLY🌄
No 25_26.
Yau da gobe a kwana a tashi babu wuya rasuwar Baffah har yayi wata uku gashi abubuwan kadarorin Baffah da yawa an rasa su wai sun 'bata harda dabbobi da kud'ad'e.

Haka lokaci yaja rayuwa tana ta tafiya har Baffah yakai wata takwas da rasuwa sannan tabi jiki Ramatu ta tada 'kayar baya sai an raba gado kowa yasan matsayin sa a baiwa kowa hakkin sa yaci gashin kansa ba iya ahlin gidan ba hatta na waje da sukaji wannan maganar saida sukai tirrrr da Ramatu domin ta nuna 'kiri 'kiri gado ne damuwarta hartayi wa manyan gari maganar azo a raba kowa ya kama gaban sa.

Jin haka yasa Salamatu samunta tace "Ramatu naji kina maganar a raba gado a bawa kowa kason sa ko"? "Eh haka nace nan da gobe kowa zai san matsayin sa" kai Salamatu ta jinjina taci gaba "ina fata kinsan cewa gonaki biyun nan da malam yake nomawa na d'ana Sabi'u ne ko? Domin a gaban ki a gaba na da Hauwa duk muna gurin tare da yaran ya tara mu yace kada muji ance ya sayi gona ba tasa bace ta Sabi'u ce kar bai fad'a ba tarai ta kasance a samu sa'bani yace lokacin da aka kai su Sabi'u makaranta yake baiwa malaminsu ajiyar kud'i shi kuma dayaga kud'in ya taru da yawa da Baffah yaje saiyai masa bayani ya bashi yace ko gona ce ya saya masa kafin ya d'ago yai hankali.......................
Chapter 36 · 0% Book details