← Book details Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 139 OF 145

Sashe 139

Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwa'be fuska Amatu tai "dan Allah ka barni na tafi gobe wallahi ina son zuwa gida".

"Shine nace ba yanzu ba".

"Please ka barni naje".

D'agowa yai yana kallon ta sai tura baki take tana murd'e murd'e yace "meye ni a gurin ki"?.

Zaro ido tai "kamar ya"?.

"Kamar yadda na tambaye ki waye ni a gurin ki kaka ko uba d'an uwa ko yaya mene ni a cikinsu"?.

Kaita girgiza "babu d'aya".

"Meye matsayi na"?.

"Mijina ne" ta karasa maganar kamar zatai kuka domin ta gano manufar sa tun farko hanata zuwa yake Shirin yi.

"Indai kin tabbata da abinda kika fad'a nace ba yanzu zakije ba".

Bud'e baki tai zatai magana yace "bana son musu keep your mouth shiiittt".

Mami ta kalla tana cewa "dan Allah Mami kisa baki ya barni naje"?.

Kai Mami ta girgiza ''a'a jewel tunda yace ba yanzu ba kiyi ha'kuri".

Shiru Amatu tai bata sake cewa komai ba harya gama abinda zaiyi ya mi'ke zai fita yace.

"Ki sameni a part d'ina yanzu na baki minti sha biyar idan baki zo akan lokaci ba kinsan sauran'' yana fad'in haka yai waje murmushi Mami tai tana girgiza kai tasan yanzu sabuwar takura zata bud'e musamman daya amince da aurensu saidai tasa ha'kuri,,,, mi'kewa Amatu tai tana koma part d'in ta tadauko hijab tasa tana ficewa yanzu kam Amjadd ya rigada ya santa matar uban gidansa cikin girmamawa ya gaisheta kamar wanda yake gaida Mami har Mami Amatu ya bata amma bata ce komai ba data amsa sai kawai ta wuce.

Asad yana zaune a parlor ya d'ora qafa d'aya kan d'aya ta shiga fuskarta ba annuri domin hanata zuwa gidan dayai shima a nasa 'bangaren had'e ran yayi yana cewa.

"Ina wannan nà'urar dana baki"?.

Turo baki tai kamar bazatai masa magana ba saboda haushin kewar gida tace.

"Yanzu bata da amfani".

"Kamar ya"?.

"Ina nufin bazatai aiki ba".

"Eh shine nace kamar ya waye ya lalata ta"?.

"Ba lalatawa nayi ba dama a tsarin qungiyar duk wanda asirin sa ya tonu aka gane shi daga ranar sun fitar dashi a cikinsu yayi expire a wajensu itama Clarah tun daga ranar suka cireta sar'kar ma bata nuna komai camerar jiki tayi damage saidai yanzu na sake gwadawa".

"Ok ga laptop nan" ya fad'a yana nuna mata, zama tayi tana budewa ta fara dubawa amma dai babu komai d'in kamar yadda tace masa d'agowa tai tana kallon sa tace.

"Sunyi delete d'in komai".

"Ok sharesu tunda na bayar da bayanin daya kamata tun a can yanzu a ina zamu samu wata sar'kar"?.

Kai Amatu ta girgiza ''nima ban sani ba dole wannan sar'kar saifa a hannun d'an 'kungiya za'a samu kaga kuwa samunta zaiyi wahala''.

"Eh na sani amma ya zama dole mu samota koma a ina ne inaso muje cikin dajin da suke rayuwarsu shine abinda ya rage min a yanxu na kammala hujjojin dana tara"..

Shiru Amatu tai cikin tunani zuwa wani lokaci tace "yanxu dai bansan inda za'a samu sar'kar ba amma insha Allahu zanyi iya bakin kokari na".

"Ok tnks you sannan abu na gaba dukkan abinda kikasan naki ne a part d'in Mami ki d'auko shi ki dawo dashi nan ki bata part d'inta zama a gurin aron ya isa haka wannan part d'in shi zai zama naki tunda naga yanzu kin daina tsoron zakin nawa".

'Yar dariya tayi tana kallon photon zaki na roba qato dake tsaye kamar na gaske tace.

"Wancan zakin a haka yayi kama da me rai sannan na tambaye ka meyasa ka d'auko wild animals (dabbobin daji) ka kawo su"?.

"Saboda ra'ayi".

"Amma naga daga zaki sai giwa da tiger da manyan dokuna meyasa baka d'auko biri da kura ba".

"Me zanyi dasu"?.

"Kiwo".

"No".

"Meyasa banda su"?.

"Because ko ganin su bana so"?.

"Ni kuma akwai abinda nake so".

"Mene"?.

"Zomo".

"Kike so

"Eh da kiwon kifi🐬🦈".

"Zomo dai"?.

"Eh ko kana dashi"?.

"No saidai na samo miki tunda kina so".

"A ina zaka samo min"?.

"A tambayau surutun ya isheni haka keep quiet".

Shiru Amatu tai tana kallon sa shikam hankalin sa nakan waya can taji yace.

"Why are you looking at me"?.

D'an zaro ido tai tana kau dakai batare datai magana ba mi'kewa yai yana cewa "zo nan" tashi tayi tana bin bayansa suka shiga cikin stockyard d'in can qarshe ya kaina yana nuna mata wani d'an madaidaicin d'aki wanda aka yishi da qarafa yayi kyau bud'e mata windown d'akin yai yana cewa".

"Duba cikin nan".

Matsawa tai tana le'kawa ga mamakin ta fararen zomaye ta gani manya da qanana sunata guje-guje wasu kuma rabinsu fari rabinsu ba'ki, zaro ido tai tana kallon su cikin sha'awa tace.

"Wowww ashe kana dasu sunyi kyau musamman yaran sunfi d'aukar hankali".

Bud'e kofar d'akin yai yana d'auko guda d'aya wani d'an qarami🐇 ya mi'ko mata da sauri ta kar'ba tana murmushi tace "suna da kyau sosai na tafi da wannan"? Batare daya juyo ba yace "eh amma zaki bashi abinci ne? uwarsa bata yayeshi ba".

Jin haka yasa Amatu ta mi'ka masa tana cewa "to sauya min wani wanda aka yayeshi zan tafi dashi".

"Me zaki bashi"?.

Amatu tana kallon d'an zomon daya kar'ba ya mayar dashi taga ya tafi gurin uwarsa ya kwanta yana shan nono d'an murmushi tai tana cewa "Ba ganye suke ci ba"?.

"Eh suna ci".

"Nima shi zan bashi ka d'auko min na tafi dashi".

D'auko mata wani yai wanda already shikam an yayeshi ya bata yana rufe kofar suka bar gurin inda suka qara shiga daga nan ne ya bata mamaki gurin nan kamar shine ta gani a mafarki shekarun baya tabbas yayi kama danan kuma wancan na mafarkin ma d'an sarki ne, kodai mafarkin tane ya zama gaskiya? Subahanallahi tabbas babu tantama haka ne rud'ewa tayi tana sake kallon Asad da shikam baisan me take ba daidai sunje gurin wani dutse da yake zubar ruwa zaro ido tayi domin bata manta ba a mafarkin yana tsaye anan tazo ta bayansa bai sani ba ta rufe masa ido to amma ina dutsen data taka a lokacin waige waige ta fara can ta hangoshi a d'ayan site d'in innalillahi wallahi komai kamar a gaske ya faru ba'a mafarki ba ana cewa mafarki ba gaskiya ba wataran yana kama da gaskiya to yaukam ta gasgata..............

Katse mata tunani yayi dacewa "idan kifi kike so a cikin wannan ruwan kowanne kala akwai".

Kallon ruwa tai tana cewa "akwai shark a ciki"?.

"Eh harda starfish da kuma shi yana had'iyar mutum".

Zaro ido tai "mutum kuma kai gaskiya mubar nan kar yayo tsaye ya fito waje".

"Baya fitowa saidai in cikin ruwan zaki shiga ki ganoshi ina jiranki".

Kaita girgiza "a'a bazan iya shiga kifi su cinye niba".

"Amma ke kina iya cinsu"?.

"Eh Ina so yanzu ma d'auko min wani na tafi dashi gurin Mami".

"No bana so hannu na ko jikina yayi qarni me zaki dashi"?.

"Farfesu".

"Da gaske"?.

"Eh''.

"Ok kisa a d'auko miki acan kitchen d'in masarauta man".

"Um uhm ni wannan nake so".

"Amma saidai ki kama da kanki"? Ya tambaye ta yana nuna mata wata raga mai dogon qarfen ri'kewa bata da girma sosai d'auka tai tana sakawa a ciki ta d'ago aiko taga ta d'ebo kifaye da yawa fitowa tai da abar tana ajewa taga sai tsalle suke suna fita daga cikin ragar wasu ma idan sunyi tsallan dakyau har ruwa suke komawa d'agowa tai tana kallon Asad tace.

"A ina zan juye su suna guduwa fa"?.

"Saidai kije kitchen d'in part d'inki ki d'auko abun zubawa" yana fad'in haka ya fara tafiya da sauri tabi bayansa a parlor ya zauna ita kuma ta wuce tana d'aukowa tazo ta koma manyan ta za'be ta mayar da qananan sannan ta sake tsamo wasu saida ta cika robar ta d'auka tana fita a gurin Asad yana kallonta ta shiga part d'in da yace nata ne daga yau.

Kai tsaye kitchen ta wuce ta ajiye kafin ta fito parlor ta cire hijab d'in ta koma saidai da yake ba amfani ake da kitchen d'in ba babu komai na bangaren daya shafi kayan miya kayan abinci maggi da spices dan haka fitowa tai tana d'aukar hijab ta fice a part d'in gurin Mami taje bata nuna wani abu zatai ba tace dai ta had'ata da baiwa guda d'aya zatai Mata rakiya zuwa kitchen bata tambaye ta mexatayo ba ta kira wata budurwa ta had'ata da ita tace daga yau itace zata ri'ka yi mata hidima godiya Amatu tai suna fita daga gurin Mami ta rakata kitchen Amatu ta d'ebo duk abinda take so sannan tasa wasu bayin tare da wannan budurwar suka d'auko mata suka rakota dashi sannan Asad yabar parlon suna aje mata suka fita tadai tambayi budurwar sunan ta saboda idan ta tashi nemanta wa zatace tace mata sunanta Tasnim.

"Ok Tasnim na gode jeki saina nemeki".

"To shugaba ta ki huta lafiya" ta karasa maganar da risnawa cikin ladabi sannan ta fita tabar Amatu na aikinta kamar yadda tace haka tayi farfesun kifin ta soya wasu da ginger kad'an da garlic ga spices tayi farar shinkafa da peppered soup na kaza😋😂 saida ta kammala komai ta fito a kitchen tana shiga bedroom d'in tayi wanka amma bata da kaya anan part tunda bata d'auko ba da iya towel d'in jikinta ta saka dogon hijab d'inta data cire har qasa tana fita ta koma part d'in Mami da tayi sa'a babu kowa ta d'auko iya abinda taga zata d'auka ta dawo har lokacin ba Asad ba labarin sa dan haka tasa akai mata kiran Tasnim ta had'a kayayyakin datai a manyan basket's guda biyu tasa ta d'auka mata d'aya itama ta d'auki d'aya suka tafi part d'in Mami tana zaune tare da samarin 'ya'yants.

Da mamaki Mami take kallonta bayan Tasnim ta tafi tace "jewel daga Ina haka"?.

Zama Amatu tai tana kallon Asad wanda yadan girgiza kai kafin tace "Mami girki na fara daga yau shine na kawo kisa mun albarka".

"Girki dai jewel"?.

"Eh Mami d'azu ne muka shiga stockyard naga manyan kifaye a ruwa shine na kamosu nayi miki farfesu".

Murmushi Mami tai tana cewa "to amma fa nagode jewel irin wannan kulawa haka Allah yayi miki albarka darajar mijinki ta shafe ki".
Chapter 139 · 0% Book details