← Book details Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 126 OF 145

Sashe 126

Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bai kar'bi hannunta da sunan su gaisa ba domin ita ba maharramarsa bace kawai ya bata amsa ne a ta'kaice cewa "suna lafiya" sauke ajiyar zuciya Clarah tai tana tunanin wai sai yaushe ne zai sake mata ya daina d'aure masa fuska haka? ta sani da Yusairat ce ba haka yake mata ba amma ita ta rasa hujja meye matsalar ta data gagara shawo kansa ya sota kamar yadda take sonshi batajin zata iya rayuwa idan babu shi a tare da ita rayuwar ta zata shiga wahala wacce take gudun faruwar hakan ta sani without him her life will be difficulty hardly empty and she will be incomplet.........................

Katse mata tunani yai "Clarah kinzo d'auka tane ko kinzo kallona ne"?.

Da sauri ta dawo daga duniyar tunanin data fad'a tana saita kanta tace "sorry muje ko"? Bai sake magana ba ya juya yana kallon Amatu ya mata alamar suje kaita d'aga amma duk da haka Clarah batasan tafiyar su d'aya ba saida aka zo shiga mota taga Asad ya shiga baya sannan ga Amatu ta zagaya tacan 'bangaren ta shiga da mamaki Clarah ta kalli Asad wanda yai picking call d'in Isham yana ce mata.

"Why u stop"? Yana fad'in haka ya d'auke kai daga saitin ta kamar ba da ita yake ba yana amsa wayarshi juyawa tai tana 'kure Amatu da kallo ta kasa magana sai harbawa zuciyarta keyi cikin fad'uwar gaba to waye wannan yarinyar da suke tare da Asad tasan duk rintsi ba 'kanwarsa bace who is she? Ko matarsa ce?🙊 Lokaci gud'a a zabure ta kuma d'ago idonta dayai jaa ya rine saboda kishi tana sake 'karewa Amatu kallo saukar muryar Asad taji.

"Clarah which rubbish is this wai me kikeyi haka kinzo d'auka tane ko kuma kin zo shirme"?.

Kallonsa Clarah tai muryarta na rawa tace "Asad wace wannan ladyn naga ta shigo mota tafiyar ku tare"?.

Wani kallo Asad yai mata yana cewa "A'a ba tafiya na tare da itaba tafiyar ku tare tunda dake na ganta Clarah idan abinda ya kawo ki airport d'in nan kenan ki fad'a min I don't want nonsense 🙄".

Shiru Clarah tai zuciyarta na turiri bata sake cewa komai ba ta shiga tana yiwa motar key suka dau hanya ita kad'ai sai zancen zuci take tana sake kallon Amatu ta mirron motar ko zataga wata 'yar kama dazai nuna itadin 'kanwar Asad ce da zatafi kowa jin dad'i taso share batun amma taji bazata iya ba zata tambaye shi koda bazai ta'ba bata amsa ba zata bi 'kwakkwafi tayi masa naci ko zai fusata saidai bazata iya jurewa ba gyaran murya tai tana dan juyowa ta kalli Asad da hankalinsa bai kanta cije lips tayi ciki takaici tace.

"Asad dan Allah ka fad'a min wacece ita"?.

"Ki tambaye ta".

"Ai baka bani dama ba na tambaye ta ita wacece taka ba"?

Har lokacin bai juyo wajen inda take ba yace "ke meyasa kika damu saikin sani"?.

"Saboda nasan ita d'in meye taka"?.

"Saurin me kike zaki sani".

"Asad hankalina ya'ki kwanciya tunda na ganku tare kishina ya tashi".

"To ai ya miki kyau amma ki rufe min baki bana son sake jin wata magana" numfashin daya tokare mata a kirji da'kyar ta fitar dashi tana karya kwanar inda zatai parking suna fitowa taga yai wajen gidan shi da sauri tabi bayansa tana cewa.

"Amma Asad a tunani na ita mace ce ba hostle d'in zallar mata wadanda basu da aure 'bangaren mu zakace na rakata ba sai kuma naga kayo gidanka da ita nasan kai bakasan mace tana ra'barka"?.

Bai dakata da tafiyar saba yace "ni na fad'a miki haka"?.

Kaita girgiza "a'a bakai bane amma naga ni baka ta'ba bari na shigar maka gida ba shiyasa abun ya rud'ani sama da shekara goma muna tare amma baka bani fuska da damar shiga maka ba"?.

"Eh sai kuma yau nazo da wacce ya zama dole ta shiga gidan nawa".

"Dole kuma Asad kamar wata matarka? anan zata zauna tare dakai"? .

"Eh".

Kawai shine abinda yace mata daidai sun isa kofar gate din Clarah da take jin juwa na d'ibanta idonta ya fara ganin duhu a hargitse tace "Asad please wannan yarinyar wace who is she idan matarka ce ka fad'a min na daina wahalar dakai na"?.

"Clarah never mind".

"Meyasa zakace min karna damu da akwai wani abu da kake 'boye min"?.

"A'a ke haka kike tunani"? .

Kai Clarah ta d'aga "eh Asad haka nake tunani ka fad'a min kawai ka barni cikin duhu".

"Clarah ina miki kashedi fa do not put your self into trouble 😠 kin gane? bana son irin wannan tambayar domin baki da wani hakki a kaina keba 'kanwataba ba 'yar uwataba ba matata ba".

"Ok shikenan Asad na fahimta".

"Me kika fahimta".

Baka so nasan wacece ita shine dalili right"?.

"Eh I have confirmed it gara da kika hutar da kanki kika gane thank you zaki iya tafiya" ya fadin haka yasa key ya bud'e gate d'in suka shiga Clarah tana tsaye ta 'kame guri d'aya sai bin kofar take da kallo jitake kamar ta d'ora hannu aka ta rusa kuka ko zataji sassauci a zuciyarta wannan budurwar da yazo da ita barazana ce a rayuwar ta tana so tasan gaskiyar wace ita mene ala'kar dake tsakanin su sake kallon kofar tai tana jan tsaki a fusace ta juya tana d'aukar motar ta tabar gurin direct barrack ta zarce kai tsaye ta shiga bulayin neman Isham amma bayanan hankali tashe ta kira numbar shi yana d'agawa ta saka mai kuka da mamaki Isham yace.

"Clarina meya faru ina Asad d'in ko akwai matsala ne"?.

Cikin kuka Clarah tace "eh Isham da matsala a ina zan sameka yanzu"?.

Tambaya ya jefo mata "ina Asad d'in ko bai sauka ba"?.

"No yana gida isham inason zamuyi magana ne dakai kana ina"?.

"Bana kusa nayi nisa ki bari sai zuwa dare zan dawo" zaro ido tai tare da dafe saitin zuciyarta dake ciwo tace "dare Isham indai ba gawata kake son gani ba please kazo yanzu" ta karasa maganar tana sake fashe masa da sabon kuka.

Da mamaki yace "subahanallahi wai Clarah 'kalau kuwa"?.

"Ba 'kalau ba Isham ka dawo yanzu".

"A'a Clarah akwai uzurin da nake yi bazan samu damar dawowa yanzu ba".

Cikin kalar tausayi tace "dan Allah ka saurare ni".

"Ok ina jinki ya akai"?.

Clarah tana shashshe'kar kuka tace "Isham Asad yana neman 'karasa min zuciya".

"Dayai miki me"?.

"Da yazo da wata budurwa tana nan ya shiga gidan sa da ita na tambaye shi wace ita a gurin shi yace min bai shafe ni ba kasan waye Asad baya bari mace taje masa koda kofar gate balle har ta shiga gidansa amma itafa wannan tare yazo da ita abun yana bani tsoro Isham kar ace matar sa ce zuciyata bazata iya dauka ba please Isham dan girman Allah ka taimaka min".

Isham dake sauraron ta shima mamaki ya gama cikashi da tarin tambaya a ransa to dawa Asad yazo har Clarah ta susuce haka a iya saninsa Asad baida 'kanwa mace indai ba cousin d'insa ba, dawo dashi daga tunani Clarah tai da cewa.

"hello Isham kayi shiru ko kaima bakasan wace ita ba"?.

"Eh Clarah maganar gaskiya bansan wacce yazo da ita ba domin da mukai waya dashi bai fada min zai taho da kowa ba Kinga nima bansan da zuwanta ba bansan wace ita ba amma ina da tabbacin Asad baida mata taya zaiyi aure ban sani ba kawai kece kika rud'e maybe ma a cikin sisters d'insa ne d'aya ta biyo shi zatai karatu ko kuma wani abu dabam ke kuma har kika damu kanki haba da Allah ki ri'ka sassautawa zuciyarki wannan ba'kin kishin idan ba haka ba wata rana zakisa ta buga".

"Ok thank you na gode Isham zan kula sai anjima".

"Ok ba matsala".

Kashe wayar Clarah tai tare da runtse ido da 'karfi ta sau'ke ajiyar zuciya tana cewa "kai sai yanzu naji dad'i har zuciyata ta samu nutsuwa Allah yasa maganar Isham ta tabbata ace cousin d'in tasace da zanfi kowa farin ciki but hakan ma bawai na 'kyale bane zanci gaba da bincike harsai na gano wacece ita koda ace bai sani bane" ta karasa maganar tana shiga mota tabar anguwar.

Kwanansu biyu da zuwa Asad yaci gaba da koyar da Amatu sauran abubuwan da suka rage sannan ya bata wani littafi tana karanta shi a ciki ma dukka bayani ne akan lamarin abinda ya shafi 'bangaren aikin sojan sai taga wuyar da tasha a Nigeria nafila ne akan tanan wancan somin ta'bi ne yanzu yake bata cikakken horo acan d'in ma saboda su Mami yasa yake d'aga kafa kar suga kamar zaluntar ta zaiyi.

Cikin nasara ta fara aiki da qwarin gwiwa da qarfin zuciya new comer ce ita amma fa tafi wasu tsofin kan nuna jarumtaka da rashin tsoro ba Asad da yazo da ita ba hatta Isham da sauran wasu sojojin sun yana mata ganin irin 'kwazon da take nunawa da bajinta idan aka zo yin wani abu daya shige duhu takan bada solution kuma idan akai a dace tuni ta d'aukaka tayi suna tauraronta ya haska ta samu lambar yabo.

Zuwa wani lokaci mai tsawo ta samu 'karin girma wanda kowa yayi mamaki mace a cikin maza ta d'aura rank itama Asad yafi kowa yabon jarumtarta ya sake janta jikinsa sosai sukai sabo kuma tamkar 'kanwa ya ri'keta kamar yadda itama ta d'aukeshi yayanta 'bangare guda kuma ga binciken da take taya shi sun tara bayanai masu tarin yawa suna aje 'kwararan hujjoji akan 'kungiyar overcrowded potency association wanda babu wanda suka bari ya san sunsan komai sai iya Isham da Sir murtih Jonah sun fad'a masa wani abu daga abinda sukai binciko kuma ya yarda ya gamsu ya nemi wasu qarin bayanin Amatu tayi masa sannan ta fad'a masa suna kan hanyar kawo sauran bayani akan opa da inda suke rayuwa koda cikin rami ne zasu 'kwa'kulo su dan haka Sir murtih da Sir Jalalunddeen sukai na'am domin sunyi farin ciki da zuwan Amatu lallai ita alkairi ce a tare dasu domin kawo karshen zalunci kodan 'barnan da kungiyar keyi.
Chapter 126 · 0% Book details