Sashe 10
Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Basu baro asibiti ba sai kusan karfe sha biyu da rabi na dare suka dawo masarautar babu wani labari mai dadi game da Kimiyyah domin likita yace bashi da tabbacin zata sake rayuwa idan kuma ta rayu maybe zata samu tabin kwakwalwa lamarin daya susutar da kowa haka suka dawo jikin su a mace kowa da abin da Zuciyar sa ke fad'a masa tana sa'ka da warwara.
Mu dawo 'kauye tushe da asalin kowa wanda baida 'kauye baida asali tsintaccen kan hanya ne🙄.
Gidan ilyah zaune Bara'atu take a gaban kayayyaki tana ta lissafi da maimwitawa ta kasa total din kudin gashi tasan ba'kin sun kusa karasowa d'aga murya tai ta soma kwalla kira "Maimuna Maimuna kina ina zo dan Allah taho da sauri taki ta sameki" da saurin kuwa Maimuna tayo waje daga d'aki tana gyara daurin zani tace "lafiya Barah irin wannan kira haka duk kin hargitsa min ciki"? Dariya Bara'atu tai tana cewa "ke kam dai wallahi ba wuya kice an d'aga miki hankali dama lissafin kudin wannan shinkafar zaki taya ni da buhun wake biyar ga na gyad'a can Mara 'bawo buhu biyu ga barkono dan Allah muyi sauri da Ilyah ya dawo zai fara fad'a kin sanshi da hararrami" zama Maimuna tai suka soma lissafi har suka gama daidai Ilyah ya shigo yake tambayar nawa ne kudin ta fad'a masa ledar hannunsa ya mika mata yana cewa "na sanki da nawa kiyi sauri ki dafa musu kajin nan sun kira ni a waya yanzu sun kusa isowa" to Bara'atu tace tana karba shigowar Nafisa da markaden kayan miya ta aje tai d'akin su ganin Salmah zaune tana kwalliya yasa cikin mamaki tace "ke kuma ina zakije kike ca'ba wannan adon kamar zaki gasar kyau"? Dariya Salma tai tana cewa.
"To da fa ina zanje amma tun wancan satin nake fad'a miki saurayi na zaizo ko"? Tabe baki Nafisa tai "au kuma shi kikewa wannan kwalliyar lallai kina da aiki karshen ta mummuna ne me tumbi har kika tsaya bata lokacin ki wajen shafe shafe kamar d'an shugaban kasa ne zaizo gurin ki" had'e rai Salma tai "kuma saikin zagar min shi eh naji koma maye ni ina son kaya na in fitsari banza ne kaza ma tayi inta isa" dariya Nafisa tai tana cewa "ai yarinya ni yanzu na wuce tunanin na auri dan kauyen nan na karfi mahaifi na babu mai kudin sa a halin yanzu a garin nan kinga kuwa ai na tserewa sa'a" mikewa Salma tai tana cewa "haka mukam bamu fi karfin auren d'an garin muba kema zaki sauke domin ba d'an birnin da zai soki" zaro ido Nafisa tai "haka kika ce" daidai Salma tadau hijab zata fita tace "eh haka nace" tana fadin haka tai waje zama Nafisa tai ita kadai sai magana take "hum Salma kenan zaki sha mamaki bari Allah ya kaimu lokacin bikin zakiga irin mijin dazan aura nasan har abada babu wacce zata samu kwatankwacin sa a kauyen nan" karasa maganar tana fad'awa kan katifar su.
Haka nan Amatullahi taji son ziyara a ranta dan haka ganin ba abinda take yasa ta mike tana debar ruwa ta shiga wanka shaf shaf a yan mintuna ta kammala shiri ta fito tana shiga d'akin umma tace "umma ina son zanje ziyara gidan baba Ilyah da Baba Rakiya kuma zan d'an biyo ta gidan su Fatima mun dade bamu hadu ba" d'agowa Binta tai tana kallon fuskar Amatullahi saidai tayi murmushi kawai tana mayar da kanta tace "to ki gaishe dasu saikin dawo" to Amatu tace tana fita a zauren gidan ta hadu da malam Habu zai shigo cikin mamaki yace "Mamana ina zuwa" d'an sauke kaitai tana murmushi tace "zanje gidan baba Ilyah da gidan baba Rakiya saina biyo ta gidan su Fatima" shiru yai kamar zaice mata a'a saidai bazai hanata zumunci ba dan haka yace "to shikenan Mamana Allah ya tsare min ke saikin dawo karki dade" "to baba bazan zauna ba yanzu zanje na dawo" kai ya d'aga mata ta juya ta fita a gidan shi kuma ya shiga ciki iya sallama yai tun bai sauke sallamar ba A'i ta dauko kwaryar garin tuwon da aka niko tana direwa gaban sa tace.
"Malam ga garin tuwon ka nan gaskiya na gaji kullum ace kaine da girki bayan kayi casa ka gyara hatsin kayi surfe ka kai ni'ka da kudin ka kayi hadin abin miya wannan wacce irin rayuwa ce"? Wuce ta malam Habu yai yana zama a bakin kofar dakin sa kan tabarma ya kunna radio yana saurara takaici ne ya kama A'i tayi kwafa tana daukar kwarya ta shige d'aki sai balbali take "wai kayi magana kaida gaskiyar ka a mayar ka mahaukaci nikam wannan abu ya na 'kona min rai maigida guda ba sana'a wallahi da sakal dole ka tashi ka nema malam Habu idan ba haka wata rana zaka budi ido kaga gidan ka ya zama kango duk mun watse mun barka wazai iya zama cikin irin wannan ba'kin talauci haka" ita kadai take wannan tace wancan.
Yadda zata jiyo shi ya d'aga murya yana cewa "aike A'i tun ba yauba na fahimci kin samu matsala a kwakwalwarki shiyasa nake miki usuri dan da kinsan abinda kike baza ki rika kallon cikin idanu na kina iya fad'a min dukkan maganar data zo bakin ki ba" fitowa A'i tai tana cewa "yo malam tsakani da Allah inda talauci ma fa da laifin ka ka mike ka nema inace ko majalisar zaman taku kowa da abin sana'arsa kai kadai ne kake zaman kashe wando labarin rariyar hannu ce dakai ya zaga ko'ina har wajajen kauyen nan gashi ko samari babu wacce yarka take dashi mutane suna cewa kada su aure su suna debe kayan abinci suna kawowa gida....................
"A'i ya isa haka" malam Habu ya fad'a yana nuna ta da yatsa shiru A'i tai domin ganin ta fusata shi yasa ta debi 'yan siraran kafafunta tabar gurin tana cewa "kai kuma malam akwai son yiwa mutum tsawa har kasa naji shakkar ka" ko kula ta baiyi ba ya cigaba dajin rediyon sa.
Gidan ilyah Amatu ta fara zuwa amma dai kamar kullum ba maraba ba 'karaso balle a nuna anji dadin zuwanta tana ta tsaye kamar kafaffiyar bishiya har Nafisa ta fito tana cewa "umma nifa gaskiya yunwa nake ji wai har yanzu ba'a sauke ba" kallon ta Bara'atu tai "eh ya kusa kidan kara hakuri juyawa Nafisa tai tana komawa bayan ta gasawa Amatu harara tace "wai nikam dama har yanzu ana maula ne lallai kud'i sunyi" Bara'atu batai magana ba domin haka nan taji tana kunyar Amatu.
Itakam Amatu maganar da Nafisa tai ko kadan bata ta'ba taba saima d'an kyakkyawan murmushi data saki tana cewa "sai anjima" a yangace Bara'atu tace "a'a bazaki shiga ku gaisa ba yana ciki fa" bata ce komai ba ta juya da sallama ta shiga d'akin sa yana zaune gaban sa fal da kayan marmari ga wani yana sha gefe gashashshan naman balangu ga kwaryar kindirmo dukka anyiwa yan birni tanadi durkusawa Amatu tai tana gaida shi a ciki ya amsa yana hade rai tare da zaro d'ari biyu ya mi'ko mata kaita girgiza tana mikewa tace "a'a dama kawai nazo gaida ku ne sai anjima" mayar kudin sa yai da sauri yana cewa "to to sannun ki da kokari tun kina yarinya kinsan zumunci ki gaida yan gidan naku" to tace tana fita Bara'atu ta tsayar da ita da cewa "Amatu har kin fito ki tsaya na sauke miya kici abinci ga kaji nasan kila yau bakici komai ba tun dumamen safe" juyowa Amatu tai da sauri ta na kallon Bara'atu da mamaki saidai batace komai ba kuma bata nuna ta damu ba tace "a'a nagode sai anjima" ko magana bata bari Bara'atu ta sake yi ba tai waje tana mamaki wato haka baba Ilyah ya koma amma ya taimaki mahaifin ta koda jari ne ya'ki.
Jitai zuwa gidan baba Sabi'un ma ya gundureta ya fita a ranta amma haka ta daure tabi ta gidan su Fatima domin ta rakata duk da gaban ta na fad'uwa batasan me zata tarar ba acan tunda shikam ya riga ya rasu sai matar sa da 'ya'yansa a gidan biyu sunyi aure da daya mara aure da mata uku a d'aki Kowacce da yaranta da sallama suka shiga Innah Rakiya tana zaune gaban murhu tana aikin girki da mamaki tace "a'a mamar kowa da gaske kece kamar a mafarki kai maraba lale sannunku da zuwa keda Fatima ne yar gidan malam Mato can kusa da dandali" tabarma ta dauko ta shimfida musu tana cewa ku zauna zama sukai suna gaida ita cikin fara'a ta amsa musu tana tambayar su can wajen anguwar har ta 'kare tuwan shinkafar da take tai kunu suna zaune domin sunyi yunkurin tafiya itace ta hana su saida suka ci suka koshi ta zuba musu wani tace Amatu taje gida dashi godiya sosai Amatu tai mata cikin jin dad'i da karramawar datai mata domin ta matukar burgeta shimfidar fuska akace ta wuce ta tabarma.
Daidai zasuyi sallama manya manyan motoci guda biyu sukai parking a kofar gidan Ilyah yana tsaye ya fito taryar su sai kancara ha'kora yake dan tabe baki Amatu tai tana kallon Fatima tace "amma ba anan zamu rabu ba zaki karasa gidan mu ko"? Kai Fatima ta girgiza tana cewa "a'a anan zamu rabu zanje gidan baba dala ne" kai Amatu ta d'aga "to shikenan Fatima na gode" sallama sukai ta shiga gida Fatima kuma ta wuce.