← Book details Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 145

Sashe 18

Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Fad'i man me kake son cewa"? Malam Habu ya sake tambayar sa cikin gulma Tanko yace "wanne kwarto aka kama"? Mikewa malam Habu yai yana daukar goronsa yace "nima bansan waye ba amma aminin naka Mudi ya sani ka tambaye shi zai fad'a maka domin yana garin lokacin da ake ihun cewa azo an kama kwarto shine yazo ya fesa anan cewa kwarton ma tsoho ne yaje gurin yarinyar da bata fi jikarsa ba ashe ya yaudare ta a kasuwa duk sati yakan sayi lemo da ayaba ya bata ita kuma yarinyar tallar dankali take shiga kasuwar duk sati ya dad'e yana bata kayan kasuwa sai ranar yace mata yana son zasuyi magana tace masa to suka fita daga kasuwa sai yace suyi nesa da mutane yake ta janta har suka wani sabon gida da ake gininsa ba'a karasa ba suka shiga nan ya bata kud'i mai yawa yake ta janta da hira idan tace zata tafi saiya hanata har akai kiran sallar magriba karshe dayaga ta damu ta tafi gida saiya nuna mata abinda yake so nan fa yarinya tai tsalle ta dire tace batasan da wannan maganar ba da yaga tana shirin gudu ya kamata da komawa yarinya d'anya shakaf taga za'ai mata zarrar data zarce ma tunanin ta ta fara zunduma masa ihu tana kururuwa nan mutane suka taro aka tara masa gayya 'kiii aka fito dashi sai kare fuskarsa yake matasa suka d'ebo makamai suna cewa a barsu su kashe shi da'kyar aka tattare su aka hana su aka jashi gaban mai gari nan akaita shari'a akaci tararsa kud'i haka ya tafi garin su jikinsa a sali'be yana d'ari d'arin shiga cikin mutane amma da yake yafi kowa idon akuya ganin anyi burus dashi ba'a nuna masa ansan komai ba saiya ware yaci gaba da fella tsiyar sa kunga wannan shi za'a Kira da yayi new ba malam Habu ba" yana kaiwa nan yai gaba.

Da ido suka bishi cikin mamakin dawa malam Habu yake wannan maganar kafin Tanko yace "kai Mudi kasan da wa Malam Habu yake wannan maganar"? A fusace Mudi yace "ban sani ba meyasa baka tambaye shi ba ka bari ya tafi sannan zaka zo ka dame ni' yana kaiwa nan ya kad'e rigarsa fuuuu yabar gurin da harara Tanko ya bishi yana cewa "jimin tsinanne wato harda ni zakai fushi? Aiko saina nuna maka na fika hauka" kowa na jinsu yai shiru domin sun fi kusa haka Tanko yai ta balbalin bala'i har ya gaji ya 'kyale.

Dutse mopal Base
Satin su Binta biyu take shirin komawa domin ta huta har tayi 'kiba ta murje suna zaune da 'kaninta Bashir ranar da zasu koma gida take ce masa.

"Bashir dan Allah ina da bukata a gurin ka" kai Bashir ya d'aga yana cewa "meya faru fad'a min Allah yasa ina da damar dazan magance miki matsalarki".

Bayani Binta ta fara yi masa "dama matsalar akan malam ne Bashir dan Allah ka taimaka masa da jari wallahi malam yana cikin damuwa da fuskantar 'kalubale a kauyen nan bai isa nuna wani abu da sunan nasa ba komai ya ta'ba a narke ya rasa inda zaisa kansa hatta yarinyar nan Amatullahi tana cikin damuwar mahaifin ta kullum tana cikin kuka da fad'a min cewa taya zata taimaki babanta wannan dalilin yasa nazo dan Allah Bashir ka taimakawa malam".

"Shikenan aunty kada ki damu insha Allahu za'a bashi jari malam Habu mutum ne na 'kwarai lokacin da kukazo banji dad'in yadda na ganku a rame ba saidai wannan bayanin da kikai min na gamsu dashi zan baki dubu d'ari ki tafi masa dashi a cikin kudin da zanyi zakka ba fitar ki bashi dubu hamsin ki dauki dubu talatin ki bawa kishiyoyin ki dubu goma goma zansa a mayar dake gida a mota zan fad'awa Safiyyah zata zuba kayan abinci a motar ki tafi muku dashi nasan zai ishe shi kice zansa a kawo masa kayan da zai ri'ka saidawa daga baya hakan yayi" sosai Binta tai masa godiya cikin tsananin farin ciki harda hawaye Bashir ya nuna mata babu komai.

Harta mike zata tafi sai kuma ta sake zama tana cewa "karka gaji dani dai Bashir ka taimaka kasa Amatu makaranta tayi karatu yarinyar nan nason tayi karatu babanta ma naso amma rashin kud'i ya hana tun daga secondary batai gaba ba ko zata samu"?.

"Ba matsala aunty kada ki damu ina takardun ta"?.

"Suna nan na taho dasu a jakata" "ki kawo min yanzu na duba idan zan fita zanje dasu a yanko mata fom ta fara zuwa wanne bangare take son karanta"? "Ban sani ba saidai na tambaye ta" "ok shikenan babu damuwa ki kawo min takardun yanzu zan fita" to tace tana mikewa ta fita cikin jin dad'i taiwa Amatu albishir din abinda Bashir yai musu da jarin dazai baiwa malam Habu tsaba farin ciki Amatu fashewa tai da kuka tare da kifa kanta akan cinyar Binta.

Shafa bayanta Binta keyi cikin lallashi tace "kiyi shiru kinji ai a tunani na farin ciki zaki ba kuka ba"? 'Dagowa Amatu tai tana cewa "umma kukan farin cikin nake nasan cewa yanzu shima baba zai samu abin kansa ya rike mu abar yi masa gori da nunensa" kai Binta ta d'aga "eh haka ne Amatu kuma nayi magana da Bashir akan ci gaba da karatun ki yace na kai masa takardun ki zai fita dasu ya miki rijista ki fara zuwa da haka anan zan barki" da mamaki Amatu tace "yanzu zanyi karatu kenan nima zan samu ilimi gaskiya naji dad'i saidai bazan juri sai anyi hutu na ri'ka zuwa ganin ku ba" "a'a Amatu zaki jura dan Allah ki tsaya ki nutsu kiyi karatun ki" "to shikenan nan umma zanyi" "yauwa Amatu Allah yai miki albarka tashi muje ki masa godiya nima inaso zanje miyatti zuwa la'asar na tafi" mi'kewa tai suna fita a d'akin domin suje tayi masa godiyar.

Yana shirin fitowa daga part din nasa suna shiga dan haka yace su karaso main parlon sunyi maganar zama sukai Amatu na kasan carpet da fara'a Bashir yace "Amatullahi kina son karatu ko"? Kai ta d'aga "eh ina so Abba" "ok kada ki damu insha Allahu yau zan fita da takardar ki basai gobe ba zan yanka miki fom ki fara karatu kinji" "to Abba nagode Allah ya saka da alkairi" Amin yace yana shirin mi'kewa ya kuma jefa mata tambaya "wanne 'bangare kike son karanta likita 'yar jarida lauya teacher ko business zaki karanta sauke ajiyar zuciya Amatu tai tana kara yin kasa da kanta ganin batai magana ba yasa Binta cewa "Amatu dake fa ake me zaki karanta ki za'ba yana sauri zai tafi wajen aiki" d'agowa tayi tana kallon mahaifiyar ta sannan muryarta cikin sanyi dan batasan a yadda zasu dau maganar ba tace "SOJA🙊" "a'a kamar ya soja kuma shine amsar"? Binta ta tambaya tana kallon Amatu kai Amatu ta girgiza tana cewa "karatun bangaren aikin soja zanyi shine buri na" ba Bashir da Binta ba hatta Safiyyah dake gefe kan dinning ita da yaranta sun sha mamaki basuyi tunanin haka ba a d'ari kowa ya zaro ido waje yana kallon ta Nabilah har 'kwaruwa tayi wajen cewa "soja kuma Amatu"? Maryam tace "tabdijan a banza zakije a kashe ki nikwa ko hauka nake ai bazanyi aikin soja ba koni namiji ce balle ina mace" dariya Safiyyah tayi tana kallonsu tace "ra'ayi kenan cin d'an wake da diga kunga laifinta ne abinda ke ranta ta fada" raf raf sukaji ana tafi duk kallon gurin sukai Ahmad ne tsaye da murmushi a fuskarsa yace.

"Haka nake son ji jaruma ta gaskiyar aikin soja babban aiki ne kuma babu wanda zai hana ki cika burinki ni nan da kike gani zan tsaya tsayin daka naga fatan ki ya samu nayi matukar jin dad'in haka Amatullahi kuma na jinjina miki da hannu dubu😅" "uhm haka dai ka iya matsoraci ka refaye baki sai zuba zance kake kamar gaske bayan kai aka fara yiwa tayin aikin sojan ka 'ki wai tsoron mutuwa to yanzu fad'a min bakaji kunya ba ga mace a gaban ka tana cewa ita kuma aikin take so"?.

Cikin fuskewa Ahmad ya maze tare da cewa "mom ai ba tsoro ya hana nayi ba kawai aikin ne bana so kullum mutum yana ciki tashin hankali da aiki kamar wani agogo sannan bana son nayi nisa daku" "humm ba wani ka iya yawan gulma ai ya kunun ni'ka yanzu ba hospital zakaje meyasa ka dau wannan"? Ta fad'a tana nuna jakar matan dake hannunsa d'an hade fuska yayi yana cewa "ai kuma mom baza a duba wannan ba nayi mata alkawari ne kuma idan na karya babu kyau ko a addinance bayan haka zataga kamar ba sonta nake ba kawai ina mata yawo da hankali ne" "ok yayi na gaji da surutun zaka iya fecewa kullum kana sanye da farar riga kamar wani fatalwa" dariya yayi yana kallon farar rigar uniform din doctor din dake jikin shi yace "martaba ta kenan ni shine buri na shiyasa itama nake so ta cika nata burin domin nasan da d'aci ka nemi abu baka samu ba" yana kai nan yai waje yana sake cewa "Amatu karki damu in Allah ya yarda zaki cika burinki zaki zama soja wata rana" ita dai Amatu shiru tayi tana jiran hukuncin da Bashir zai yanke mata saidai tana fatan ya amince idan kuma yace a'a dole zatai hakuri tabi son ransa.
Chapter 18 · 0% Book details