← Book details Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 145

Sashe 90

Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Asad kam yana fitowa mota ya dauka yana fita daga masarautar gabaki d'aya ya d'auki hanya yayita tafiya kawai duka inda ya gani cikin mafarkinsa bai 'bace masa ba direct yake bi kuma yaga dai da gaske ne musamman daya fara shigowa wajajen 'kauyukan sai yake ganin kamar komai daya faru a gasken ne ba a mafarki ba yadda gurin yake mahad'ar da hanya ta rabu a daidai nan inda sukai maganar da ita anan ya tsaya bai fito daga mota ba Saidai ya tabbata ko a mafarkin a daidai nan yake tsaye tazo ta sameshi abu na biyu daya sake bashi mamaki shine gani yake kamar ya ta'ba zuwa nan hakan kamar ya ta'ba ganin nan d'in saidai wannan titin daya bambanta garin Wanda yasan sanda suka zo zai iya tunawa akan konewar wata makaranta ne da wuta ta cinye kauyen harma Mai girma Alhussain yai maganar basu da hanya Mai kyau rairayi ne masu abun hawa suna shan wahala a hanya yafi tunanin ko titin akai musu amma tabbas yasan nan gurin duk da shekarun da aka d'iba yanzun da yazo ya tuna komai "to amma Asad wannan yarinyar fa wacce kayi Mata kyautar rigarka"? Zuciyarsa ta tambaye shi shiru yai ya nutsa cikin tunani gashi bai taho da wannan photon da Mai girma Alhussain yayi musu shi a waya ba shikuma ya mayar dashi wanda za'a sa frame taya zai tambaya a ina wannan yarinyar take wa zai tambaya tunda babu wata alama baisan taya zai kwatancen yadda za'a ganeta cikin sau'ki ba ya manta sunanta saidai koda ace yanzu ya sameta hakan baida wani amfani gareshi tunda ba aurenta zaiyi ba kawai dai yana so ya qara ganinta a rayuwa ko sau d'aya ne........................

'Dagowa yai yana kallon waje ta glass din motar hummm😐 daidai Malam Habu da Amatu sun taho zasu wuce zuwa gida daga kasuwa suke ya sayo d'an kayan miya ita kuma ta sayo musu zararrika domin yanzu d'inkin hula suka ri'ke dashi suke samu su d'an dogara da kansu domin kowa yanzu a gidan ya talauce babu wacce take sana'a sai gari ya waye rana ta fito ta fad'i babu wanda yaga naira biyar😭 saidai idan wannan hular suka d'inka ranar kasuwar wannan 'kauyen idan sun sayar a d'an sayi d'an kayayyakin abinci ai maleji a daddafe zuwa wani satin dayake juma'a-juma'a kasuwar keci.

Yana kallo suka zo suka wuce ta saitinsa yana zaune a cikin motar yana kallon su malam Habu yana rataye da buhu a kafad'arsa Amatu tana ri'ke da ba'kar leda gari yai zafi wani tunani ne ya fad'o masa bayan sun wuce saiya tuna yarinyar itama mahaifin ne zai kaita makaranta kamar haka kodai itace wannan amma taya zan tabbatar? ko tambayar su zaiyi shiru yai kawai ya zuba musu ido suna ta tafiya tun yana ganinsu har suka 'bace masa sau'ke numfashi yai yana sake qarewa gurin kallo yana duban daidai inda tace masa ya kalli wannan kumbon dake rataye zuwa wani lokaci ya tada mota yana barin gurin zuwa gida saidai koda ya koma haka ya kasa nutsuwa yayi nan yayi can sai kaiwa da komowa yake a parlon part dinsa saida akai sallar magriba da isha bayan su fito daga masallacin masarautar sannan ya wuce part d'in Mami tana zaune ita da Ajeeb ya shiga murmushi tai tana binsa da kallo tace.

"Asad yau Ina kaje ne ba sanarwa ka barni cikin fargaba na kiran yaronka Amjadd na tambaye shi yace baisan inda ka tafi ba d'azu Ajeeb ya shigo yake cemin kad'au mota amma shima baisan inda zakaje ba fatan lafiya yayi maka magana kace inda ya aikeka zakaje"?.

Zama Asad yai yanaiwa Ajeeb wani kallon zamu had'u ne kafin ya mayar da hankalin sa kan Mamin yana cewa "barka da dare Mami yakike"?.

"Ina lafiya Asad fatan ba wata matsala"?.

Kai ya d'aga "eh Mami babu amma gobe nake so zan koma".

Tun kafin Mami tai magana Ajeeb yace "ka koma ina? Haba Asad ka koma zuwa ina shekarunka nawa baka zo gida ba amma yanzu tsabar jaraba daga zuwa shine zakace wani zaka koma sai ka tafin ai mu gani"?.

Batare da Asad ya kalleshi ba yace "nace komawa zanyi inka Isa ka hana tunda kaine ka haife ni".

"Ba nine na haifeka Asad amma ina da yancin dazan fad'a maka magana kaji ka gane dan haka babu inda zaka saika kara satika kuma abinda na yanke kenan ka gane"?.

"To Ajeeb tunda a ranka kanajin ka isa dani har haka zuwa nan da karfe d'aya na dare jirgi na zai tashi basai gobe ba zan koma Marshall islands yau ka hana ka hana idan ka isa".

Kai Ajeeb ya jinjina yana cewa "Aiko zan hana Asad kuma zaka gani baka isa kabar masarautar nan yau ba kuma abinda na yanke kenan kajini👂".

Tsuka Asad yaja yana mayar da hankalinsa kan Mami dake murmushi yace "zuwa karfe d'aya zan koma Mami".

Kaita d'aga masa tana cewa "ok Asad Allah ya tsare hanya Allah ya saukeka lafiya abinda kake nema Allah ya baka sai yaushe kuma zaka dawo inka tafi"?.

Tun baice komai ba cikin tsokana dason kar a zauna lafiya Ajeeb yace "Mami ai idan kin fahimci Asad sam baya son zaman masarautar nan balle yanzu da yaga Khimiyyah ta dawo tana zirga zirga a cikinta...........

Sha'ka Asad ya kaiwa Ajeeb a fusace jin abinda yake cewa tare da nuna masa tsantsan fushin dake fitowa tun daga karkashin zuciyarsa akan ambaton sunan khimiyyah dayai yace "Ajeeb do not put your self into trouble😠 ka gane banayi dakai ka iya bakin ka a kaina".

Harara Ajeeb ya maka masa yana cewa "Bazan iya bakin nawa a kanka d'inba Asad na fad'i karya ne duk abinda kake Ina lure dakai malam na gama karantar halayyenka batun yauba".

"To ai yayi maka kyau da kafi kowa sanin halin nawa saika sha maganin zama dani babu ruwanka a lamari na..........

Katse su Mami tai ''dan Allah Ajeeb kuyi shiru haka kai miyasa ka fiya shiga safgar Asad ne kullum kuna cikin fad'a kamar wasu Tom and Jerry kuna gani dai Annur da Ameer yan uwan ku ba haka suke ba kai Ajeeb ba dakai nake ba kayi shiru maganata da Asad ne" mayar da hankalinta kan Asad tai tana cewa.

"Yaushe zaka dawo"?.

Tari Ajeeb yai🙊😂 cike da tsokana yana cewa "dan Allah Mami ki bari nace wani abu anan sau d'aya shikenan zanyi muku shiru"

Kallon sa Mami tai ganin shi kuma yana kallon Asad tace "me zaka ce"?.

Gyara zama Ajeeb yai yana cewa "nasan yanxu idan ya tafi maybe sai zamuyi aure zai dawo gidan nan domin banga dalilin dawowar tasa ba koda an kirashi yazo a ganshi zai fad'i uziri acan dan kar yazo d'in tunda naga black habit d'insa ya motsa".

Kai Mami ta girgiza domin tsaf ta fahimci Ajeeb tsokana kawai yakeso ya tuzura Asad d'in suzo suna caskalen nasu da suka saba dan haka tace "eh sai lokacin zai dawo abar maganar Allah ya tsare min kai Asad shine fatana amma Asad yaushe zakai aure kai ko tare dasu Ajeeb d'in zakai"?.

Kai Asad ya girgiza da sauri kamar wanda ta fad'i wani abu mai firgitarwa yace "Noo Mami sai nayi ritaya".

Zaro ido Mami tai tana shirin yin magana Ajeeb dake dariya yace "uhum uhum Mami kinji irin rashin hankalin nasa ko kinga d'anyan kan nasa da nake fad'a miki yau yana nuna miki ko kiji wani hauka wai sai yayi ritaya dayai aure sannan ya tsufa a yanxu ma shekarun mu talatiin da takwas kuma shi yanzu shekararsa sha biyar da fara aikin soja nan gaba sai yayi wata shekara sha biyar d'in kafin ritaya sannan yana da shakara hamsim da uku tab tsofile sannan ka dudduge ubanwa zai aureka wacce yarinyar ce zata yarda ta zauna da tsoho Asad gaskiya Wallahi baka isa ba dole kayi aure tun wuri ka gane"?.

Ko inda yaje Asad bai kalla ba baice masa 'kala ba saida ya sake magana sannan yace "sai kasani dole tunda kai ka haife ni".

Murmushi Mami tai tana cewa "ai Ajeeb ba komai aure lokaci ne bakai ka haifeshi ba kuma shima ya fad'a ne kawai wuya ya had'u da wacce yake so saidai kuji muna shirin kai masa ro'kon arziki".

Dariya Ajeeb yai yana kallon Asad yace "tab Asad da mata wai za'aga hauka anya zai iya ri'keta ma🙊"?.

Da mamaki Mami tace "meyasa kace haka kamar ya zai iya ri'keta"?.

Dariya Ajeeb yai daidai Asad ya d'ago suka had'a had'e rai yai kamar bashine yai dariya yanzu ba yace "meye kake wani kallona ko baka ta'ba ganina bane"?.

Banza Asad yai dashi bai ko nuna alamar dashi yake ba mayar da kallon sa kan Mami Ajeeb yai yana cewa "dalilin daya sa nace haka Mami naga wannan d'an naki d'anye ne nifa harna fara tunani daya zaiyi auren a ina zai samu matar babu wanda zai yarda ya d'auki 'yarsa da hankalin sa ya baiwa Asad yadda yake qasurgumin shashashan nan indai uban ba..................shiru yai tare da rufe baki bai karasa ba ya kama dariya🤭.

"Me kake son cewa karasa man muji indai uban bame ba wai Ajeeb meka mayar min da Asad d'ina ne"? Mami tai maganar tana kallon Asad daya mi'ke yana cewa.

"Ki huta lafiya Mami maybe kafin na wuce zan sake shigo miki idan ban samu dama ba zamuyi waya".

Kai ta d'aga ''to Asad Allah ya tsare hanya saika dawo" Amin yace yana nufar kofa zai fita Ajeeb yace.

"Asad ni kuma me nayi maka da baza kai min ban kwanar ba tsabar ba'kin hali kodan idan baka bukata bama niba irinka bane farin hali kar gareni kamar ruwa zanyi maka addu'a Allah ya dawo dakai lafiya kuma da kake maganar idan baka samu damar dawowa gurin Mami ba ka wuce daga can kwayi waya humm lallai ma yaron nan ka fito fili kayi bayani malam dama dai baka da niyyar dawowar ko"?.

Asad bai bashi amsa ba bai kuma tsaya ba ya bud'e kofa ya fita murmushi Mami tai tana kallon Ajeeb tace "Kai gaskiya Ajeeb ka kyautawa kanka kullum kana kan tsokanar d'an uwanka kuna fad'a kamar wasu kaji"?.
Chapter 90 · 0% Book details