← Book details Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 145

Sashe 49

Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kai ya girgiza yana kallon fuskar kyakkyawan matashin saurayin dake hakimce zaune a gefensa ya d'ora 'kafa d'aya kan daya yana sanye da tsadaddun kaya ganin yadda ya had'e girar sama da kasa kamar ba shine ya bukaci su tsaya ba yasa Alhussain yai murmushin rigima irin tasa yana cewa "eh Harun akwai matsala" sake kallon fuskar saurayin yai bazai wuce shekara sha takwas ba amma fa kyakkyawa ne na kwatance kyau kuma irin na larabawa idan ba magana yai ba zaka rantse da Allah baisan meye wani yaren hausa ba.

Mamaki ne ya kama 'kanin mahaifin nasa har yana dafa shi cike da kulawa yace "Asad kana lafiya meke damun ka meyasa kace a tsaya kuma ka "ki magana"? Cikin aji da sarauta ya d'ago yana kallon sa na wani lokaci har Alhussain ya fidda rai bazai ce komai ba sai kuma yaji zazza'kar tsadaddiyar muryarsa mai sauka cikin tsari da dad'in sauraro a hankali yace.

"Ina son magana da wannan".

Inda yake kallo shima Alhussain nan ya kalla su malam Habu ya gani tsaye da mamaki ya kuma kallon Asad domin shi idan ba yanzu ba bai kula dasu ba da har zaice masa me zai masa sai kuma ya ce bari ya 'kyale yaga abinda Asad din zaiyi kallon sauran fadawan dake dur'kushe Alhussain yai yana cewa "ok Harun bud'e masa ya fita" da sauri cikin gaggawa Harun ya mi'ke da gudu ya zagaya 'bangaren ya bud'e masa tabd'i yafi minti goma bai fito ba kafin ya ziro 'kafa a hankali ya fito kai Masha Allah kamar babban saurayi akwai 'kira a tsaye yake zarrr jarumtacce sadauki 'kakkafa yana da manyan ido ga dogon hanci fari irin na larabawa ga pink lips kaiii ya gama had'uwa cikin taku ya fara tafiya cike da nutsuwa zuwa inda malam Habu ke tsaye wanda Alhussain jin hankalin sa bai kwanta ba shima ya fito yana bin bayansa ganin Alhussain ya karaso yasa malam Habu ya saki hannun Amatu yana dur'kusawa cike da girmamawa yace.

"Gaisuwa nake ranka ya dad'e Allah ya baka nasara".

Fadawan dake bayansa ne suka amsa masa "an gaisheka kaima mai nasara ya amsa gaisuwarka" kallon Asad Alhussain yai ganin ya zubawa Amatu ido kuma baiyi magana yasa ya mayar da hankalin sa kan malam Habu yana cewa "tashi" mi'kewa malam yai tsananin mamaki ya kamashi da yake ba iya bambance su ake ba baiyo tunanin ba mai martaba bane 'kaninsa ne lallai ya jinjinawa rashin girman kansu.

Shirun ne yai yawa gajiya Alhussain yai don yaga alama indai ba cewa yai su tafi ba Asad baida niyyar cewa 'kala kuma baida niyyar tafiya yace "Asad kazo mu tafi ko"? 'Dagowa idanonsa yai yana kallon Alhussain kafin ya mayar da hankalin sa kan malam Habu yana cewa "wannan 'yarka ce"? Kai malam Habu ya d'aga "eh 'yata ce" sake jefa masa tambaya yai "mene sunan ta"? "Sunanta Hauwa" d'an rufe ido Asad yai jin sunan mahaifiyarsa kai Alhussain ya jinjina yana cewa "shikenan fad'uwa tazo daidai da zama sunan maminsa ne" fuskar malam Habu da mamaki yace "masha Allah".

Bud'e ido Asad yai yana kallon malam Habu yace "zaka bani ita"? A tare Alhussain da malam Habu suka zaro ido Alhussain na cewa "to fa Asad kamarya zai baka ita matsayin 'kanwa 👫 ko mata 🧕"? Kai Asad ya girgiza yana cewa "mata" a d'ari Alhussain ya sake zaro ido da 'yar dariya yace "to mata kuma Asad? A lallai mun kusa daukar suruka kwana kusa muna komawa zani yiwa yaya albishir" kallon malam Habu Asad yai "zaka bani ita"? Fuskar malam Habu da murmushi yace "eh zan baka ita indai kana son ta"? A hankali Asad ya d'aga kai "eh ina son ta" "to shikenan na baka ita".

"Asad shirmen ya isa haka kazo mu tafi" Alhussain yai maganar kawai da murmushi fal fuskarsa juyawa Asad yai yana kallon sa kafin yace "ina son zamuyi photo" ya fad'a yana mi'ka masa wayar hannunsa "kayi mana" kai Alhussain ya girgiza yana amsar wayar matsawa Asad yai yana sa hannu ya d'aga Amatu sama yasata a kafad'arsa dariya Amatu tayi cike da yarinta daidai za'a d'au photon shi kuma yai murmushi daukarsu yai yana cewa "kunyi kyau kar lokacin shiga ajinta ya wuce ka ajeta mu tafi" ajeta Asad yai yana shirin bin bayan Alhussain wanda sukai sallama da malam Habu sai kuma ya tsaya yana cewa "shekararki nawa"? Cikin za'ki Amatu tace "talatiin da goma da d'ari 😂".

*KAI 🙆 AMATU SHEKARA 'DARI DA ARBA'IN 🤭😲TAB AIKO BAFFAH BAIKAI HAKA BA🤩😋*.

Dariyar da ba shiri malam Habu yai yana cewa "shekararta shida" "shekararki shida ni kuma sha takwas idan kika hada da nawa kina da shekara ashirin da hudu kenan" ya karasa maganar yana cire kyakkyawar rigar sanyin dake jikinsa da photon zaki kwance a jiki a 'kasan zakin an rubuta ALIYU ASAD da manyan ba'ki bata yai batare da ya sake magana ba ya juya ya soma tafiya da kallo suka bishi har ya shiga mota aka rufe suka bar gurin tun suna iya hangosu har suka 'bacewa ganinsu.

Sauke ajiyar zuciya malam Habu yai yana kallon rigar dake ri'ke a hannun Amatu sai tashin 'kamshi take yace "Mamana muje ko? Lokaci ma ya matukar 'kurewa da yake yau Juma'a gashi yara har sun fito inaga baifi nan da awa a tashi ba kawai ki barshi mu koma gida yau din kya zo ranar litinin muje a kasuwa na sai kayan miya mu tafi gida" kar'bar rigar yai ya zuge jakar goyon dake bayanta yasaka a ciki ya zuge kafin ya kama hannunta suka wuce.

Kamar yadda malam Habu ya baiwa Dauda kud'in gudun karya sake zubarwa sai kawai ya sayi goribar ya koma kai mata daga baya ya dawo yai hayar da mamaki babarsa ke kallon shi tace "sannu sarki shiririta na baka kud'in goriba saika tafi ka barshi anan ina shara na ganshi a inda ka zauna kuma da ya ka sayo goribar bayan kace baka da kud'i ko bashi ya baka"? Kai Dauda ya girgiza yana zama yace "aini babah na dauka a hanya a jefar kud'in ashe tun a gida ne kuma wallahi kinga muka had'u da malam Habu zai kai 'yarsa makaranta shine ya bani kud'in yace na sai miki" d'an zaro ido tai tana ri'ke baki tace "oh Allah mai baiwa kai malam Habubakar baya gajiya da alkairi Allah ka bud'a arzikin sa ka tsole idon ma'kiya gaskiya Habubakar mutum ne na 'kwarai Allah ya biyashi da mafificin alkairi" Amin Dauda yace harya mike zai tafi yace "am babah tunda an samu kud'in inaga ki bayar a mayar masa abinsa ko" kallon sa tai tana cewa "eh kayi gaskiya kar'bi wannan din kace masa a gida a manta" kar'ba Dauda yai yana fita ya hau mashin d'in ya hango malam Habu ya sauka da jibgin kaya yasa da sauri ya karasa yana cewa "ashe kaga kud'in a gida na barshi ban sani ba na jefarshi" kallon sa malam Habu yai "haba Dauda kuma dan ka gani saika dawo min da kud'ina mayar mata dan Allah ta 'kara jari" cike da jin dad'i Dauda yace "to an gode Allah ya kara arziki" "Amin kai kam karka damu mayar mata" malam Habu ya karasa maganar yana fara d'iban kaya yana shiga gida dasu Saida gama sannan ya zauna kan tabarma a kofar mashigar d'akinsa cikin gajiya ya ce "Binta Kai min ruwa nai wanka a d'an fad'a yau garin da sanyi" to Binta tace tana mi'kewa cikin mamakin labarin abinda ya fad'a mata na had'uwar da sukai da mai girma Alhussain ya nuna mata rigar da Asad d'in ya baiwa Amatu saida ta gama komai ta dawo daidai zai tafi wanka tace.

"Malam amma dagaske ka bashi ita da aure kuma idan ya dawo fa yace yazo kar'bar ta"? Murmushi malam Habu ya "idan ya dawo yace yazo ne dan cika alkawarin sa wallahi Binta zan bashi" 'yar dariya Binta tai tana cewa "tab saidai a mafarki mezai dawo yayi yanzun ma sila ta kawoshi balle ya auri d'iyar talaka" "oh kina mamaki ne"? Kai Binta ta d'aga "eh 'kwarai ina mamaki sosai ma abin da kamar wuya" juyawa yai yana tafiya tare da cewa "ki daina jin mamaki babu abinda gagari mahalicci" da kallo Binta ta bishi harya 'kule sannan ta sauke ajiyar zuciya tana sake zubawa Amatu ido wacce gabadaya ta tattare hankalin ta ga wasan da take da 'kyar karamar Teddyn ta.
Chapter 49 · 0% Book details