← Book details Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 145

Sashe 86

Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Shikenan kada ki damu share hawayen jeki ku sake gaisawa da mahaifiyarki tunda kina shigowa kika tsaya a guna ya kamata kije itama taji dad'i ko" to Amatu tace tana mi'kewa ta shiga d'aki yayin da Malam Habu ya sake binta da kallo yana sauke ajiyar zuciya mai akarfi yadan rufe ido a ransa yana tunani da yace zaiwa Sadi magana su koma Cameroon amma fa yanzu ya fasa babu inda zaije bazai iya tafiya yabar Amatu a gida ba gashi Hassan sai damunsa yake akan dan Allah yaushe ne aurensu bayan kwanan baya Ilyah ya sameshi yamai tas uwa da uba akan wai ya fita hanyar 'ya'yansa dama son zuciya da zilama ce tasa yake kar'be duk abinda suka ba yana musu faran faran idan ba so yake ya hadashi da hukuma ba a musu iyaka to yayi gaggawar hanasu Hassan zuwa gidansa! Bud'e ido Malam Habu yai cike da takaicin dan uwan nasa kafin ya mi'ke yana kallon kofar d'akin Binta iya ganin takalmin Amatu dayai a kofar d'akin ya sanya masa nutsuwa ji yake kamar ya shiga d'akin ya sake ganinta kafin ya fita amma ya danne kawai ya juya yana fita a gidan.

BAYAN SATI BIYU✌️
Malam Habu yana zaune a gida bakin kofar d'akinsa akan tabarma yayi shiru yana kallon iyalansa dake kai komo a tsakar gida kowa da aikin yake sakamakon yanzu ba laifi kowacce tad'an samu jari tana juya Alhaji Bashir ne ya baiwa Amatu dubu hamsin dazata taho shine Binta ta baiwa Saude aron dubu goma tace taci gaba da sana'a inta samu ta biya zama haka babu dad'i sannan ta baiwa A'i ma dashi yanzu suke samu su d'an yi wasu abubuwan.

Kallon Binta dake wanke kwanuka Malam Habu yai zaiyi magana sukaji muryar yaji'kira da lasifika📢📢 yana shela layi layi yana cewa "yekuwa jama'ar gari mai gari ya gaisheku yace a fad'a muku duk wanda yasan ya kar'bi bashin kayan noma yaje gurin sa yanzu ana nemansa kada ka bari sai an kiraka domin masu kawo kayan sunzo yekuwa jama'ar gari............haka san'kira yayi gaba yana shele anguwa anguwa.

Shiru Malam Habu yai yana tunada da ake sauke masa tirela guda yanzu kuwa ko a mashin ba'a kawomasa damai kud'i ake bushasha kila ma sun manta dashi duk da irin dad'ewar dayai yana sayan kaya a gurin su................................

Muryar Binta ce to dawo dashi daga d'an tunanin daya tafi "Malam fatan babu kai a ciki ko tunda naga yanzu ka daina harkarsu kayan kud'i sosai" ta tambaya cike da fargaba tana kallon sa.

Kai Malam Habu ya girgiza yana cewa "a'a babu ni aciki Binta kin manta rabon dana kar'bi kayan aikin gona a gurinsu shekaru nawa harna manta da su malam Balah su Mudi Tanko akewa shelar da yaya Ilyah tunda yanzu dai sune masu abun hannu kuma sune suke da gonaki suke harkokin kayan gona bangaren kayan abinci dana lambu amma nikam babuni a wannan shafin waye zai sako fa'kirai irinmu ana maganar masu shi".

Shiru Binta tai bata sake cewa komai ba taci gaba da aikinta amma haka nan taji zuciyarta na d'ar d'ar da fatan Allah yasa babu Malam Habun a ciki tunda yanzu wannan zamani zalunci yayi yawa dashi ake ado😞.............

Sallama sukaji anayi a kofar gida kuma muryar dai sun santa d'an gidan Mai gari ne Buba wanda ada yaso Asma'u uwarsa ta hana.

"Innalillahi malam kaji abinda nake tunani ko gashi ana sallama kuma wannan dai Buba ne"? Shiru Malam Habu yai zuwa wani lokaci kafin ya mi'ke batare da yace komai ba ya fita har kasa Buba ya dur'kusa ya gaidashi sannan ya fad'a masa ana nemansa a gurin babansa kai Malam Habu ya d'aga yana cewa.

"To muje Allah yasa lafiya".

Mi'kewa Buba yai suka tafi fal ya samu gurin mai gari mutane sun cika wasu duk gulma suka zo wadanda dai akazo gurin nasu gasu nan a gefe alhazawan garin su Ilyah Tanko alhaji Gambo Malam Sabo Balah Mudi sai hura masa hanci suke suna bud'e kafad'u😣.

Zama malam Habu yai yana gaida Mai gari sannan suka gaisa da kowa kafin ya juya hankalin sa kan mai garin yana cewa.
"fatan dai lafiya ina gida Buba yaje yana cewa kana nema na"?.

Kai Mai gari ya d'aga "eh nine nasa shi a kiraka amma wadannan ba'kin da kake gani sune suke nemanka sunzo da wata takarda me dauke da sunanka da rubutu ajiki gasu nan".

Mayar da hankalinsa kansu malam Habu yai yana cewa "sannunku da zuwa ina fata lafiya dai ko"?.

Gyara zama daya daga cikin su yana cewa "kaine Alhaji Abubakar wanda ake kawowa kayan aikin gona a tirela🚒 shekarun baya"?.

Kai malam Habu ya d'aga dan yasan dama da haka su suke kiransa Alhaji Abubakar sunan da suka rubuta kenan d'agowa yai yana kallon su yace "eh nine meya faru"?.

Wasu sabin buhuna guda goma😯 yaga an mi'ko masa ga zaren d'inke buhunan da allurar d'inkewar irin bisilan nan suna ce masa.

"Sa'ko ne daga kamfanin mu cewa an biyoka bashin shinkafa buhu biyar alkama buhu uku wake buhu biyu tun wancan lokacin ba'a binciko file d'inka ba sai a wannan satin aka d'auko shi shine akace mu kawo maka ka zuba ka d'inke mu tafi dasu" ya karasa maganar yana aje masa manyan sabin buhuna masu girman gaske a gabansa.

Wata irin daskarewa Malam Habu yai jikinsa yana rawa innalillahi wa Inna ilaihi raji'un😭 tashin hankali kenan wanda ba'a sa masa rana gumi ne kad'ai ke yanko masa ya kasa furta koda kalma d'aya ce dariya Tanko yai yana cewa.

"Tofa Alhaji Abubakar masu ruwan nairori a d'au buhu maza yanzun nan aje a d'ebo musu shinkafar nan da take jibge a d'aki".

Dariya Mudi yai Shima yana karewa yanayin Malam Habun kallo yace "yo wannan talakan talakawan Ina yaga zirin shikafa ko d'aya ce a gidansa saidai in tururuwa ce ta d'auka a waje takai masa da kake cewa yaje ya ciko dame indai bada 'kasa zai ciko musu ba ko ya sayar da yarinyarsa guda d'aya wama take da suna? Ya fad'a yana kallon malam Habu ganin baya tare dasu tsabar tashin hankalin daya shiga baima san me suke ba dariya Tanko yai yana cewa.

"Hauwa'u Amatu ko?? Mamarsa cene ko 'kanwarsa na rasa ma sunan da yake fad'a mata sai ya sayarta tunda wannan masifar ta sameshi ya biya"

Cikin tsokana da isgili Mudi yace "Amma bari muyi shiru kar muji kunya bamu sani ba ko d'an uwansa Alhaji ilyah zai biya masa"?.

Jin abinda Mudi yace yasa kowa ya mayar da hankalinsa kan Ilyan suji Mai zaice bud'ar bakinsa ba kunya ko kara sai cewa yai "tabd'ijan wanne Ilyan kuke magana amma dai baniba wanine dabam ko? Allah ya sauwake na biyawa Habubakar bashi wallahi yadda nake jin haushinsa akan su Hassan da yakewa wayo fatara tasa yana kar'be musu kud'i Aiko kashesa zasuyi su d'ora masa bindiga a ka dai ina kallo ace inban biya ba zasu harbe shi wallahi saidai yai bunga uban waya hanashi tashi ya nemi kud'in"? Ilyah na rufe baki guri ya d'auki sowa hhhhh suka kuma fashewa da dariyar mugunta har hawaye ne yake zuba a idanun Tanko yana kallon malam Habu yace.

"A'a malam Habu yadai ka zama mujiya mai ba'kin jini kana jin abinda d'an uwanka yace inaga mu iye mukuma muce maka me yanzu fad'a min Ina gasa maganar daka saba idan anyi maka magana yau bakin ya mutu ko umhum uwar bari ba shegiya bace da ubanta kaima yau ka shiga uku taka ta sameka".

Tari da bai kama malam Habu ba baiyi ba kawai kuma badan bazai iya mayar musu da martani ba a'a sai tsabar takaicin maganar da Ilyah ya fad'a a gaban mutane akansa wai uba d'aya? Amma yake tozarta shi haka a gaban mutane jin hawaye na neman zubo masa yasa cikin jarumta da sauri yayi kokarin mayar dasu ba tare daya d'ago kansa ba.

Ganin da me gari yayi kamar Malam Habu baya cikin nutsuwar shi yasa yace "wa kake da suna Alhaji Mansur kace ko? To dan Allah kuyi masa ha'kurin yau ku d'aga masa kafa zuwa nan da sati biyu sannan ya gama had'a muku saiku dawo ku d'auka na roka masa wannan alfarmar".

Kai Mansur ya girgiza yana cewa "ai ba'ace mana mu taho batare da wannan kayan nasa ba sakamakon ya dad'e da fa cewa akai a taho tare da 'yan sanda su tafi dashi saboda yasan ana binsa tsawon shekaru yai shiru bai nemi company ya mayar musu ba da'kyar wasu suka sa baki cewa tsohon costumer d'insu ne amma badan haka saidai yau ya kwana acan".

Kai Mai gari ya jinjina yana kallon malam Habu kafin yace "shikenan amma dan Allah kuyi masa uzirin nan zuwa sati biyun kawai saiku dawo insha Allahu zasu samu kayanku dan Allah kunji dole rayuwa saida uziri balle shi ba kamar yadda suka sanshi da yanzu ba haka yake ba ku masa afuwa"..

"Ok to shikenan ba matsala zamu dawo nan da sati biyun Amma kafin nan ya bada kayan a gurin ka kawai da munzo da mota sai mu d'auka"? Jin sun amince yasa Mai gari yace "eh ya amince zuwa sati biyun".

Bayan sun gama magana da sauran sun kar'bi kayan da zasu kar'ba komai ya shiga manyan motocin da sukazo dasu sannan sukaiwa Mai gari sallama suka tafi daga nan kowa ya fara bajewa sai gulmar malam Habu ake wai yanxu ya zaiyi mutumin da bashi da ko naira biyar akawo masa buhu ba d'aya ba har goma ya cikasu da kayan abinci tabbbb zasuga yadda wannan cakwakiyar zata kare.

Saida Mai gari ya bari kowa yabar gurin daga shi sai malam Habu da sauran wasu yan majalisarsa mutum biyu ya kalli malam Habu yana gyaran murya yace.

"Am nikuwa malam Habu idan bazaka damu ga wata shawara dazan baka ko Allah zaisa ka amince ta yadda zaka biyasu kayan nan batare da tashin hankali ba"..

Kallonsa malam Habu yai yana cewa "amma me gari taya kenan wannan kayan da suke bukata a gurina bana karamin kud'i bane dame zan biyasu na tabbata ko yar gonata guda daya da nake nomawa na sayar kud'in bazai isa Wanda zan basuba"?.
Chapter 86 · 0% Book details