← Book details Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 145

Sashe 57

Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

🕚😃🤗
Asad na zaune a wata babbar kafaffiyar rumfa dake cikin 'katon barrack d'in da laptop💻 a gaban shi yana aiki Yusairat da Clarah suka shigo suna zama bai d'ago ba da sukai masa sallama amma ya amsa kallonsa Yusairat tayi tana cewa.

"Asad an ta'ba ce maka kai kyakkyawa ne"?.

Ba Asad ba hatta Clarah saida ta kalleta da mamaki da kuma kishi cikin alamun tambaya yace.

"Kamar ya"?.

Murmushi Yusairat tai "kamar ina nufin wani ya ta'ba ce maka kana da kyau"?🙅.

Kai ya jinjina "eh ba mutum d'aya ko biyu ba mahaifana ne farko sun fi kowa yabo na".

Gyara zama Yusairat tai tana cewa "nima ina son ka saka ni a cikin su Asad kai kyakkyawa ne kuma na fad'i abinda yake 'karkashin zuciya ta sannan ina so idan ka samu lokaci zamuyi magana".

"Ok ina jinki"?.

Kallon Clarah Yusairat tai da kulawa tace "please Clarina dan Allah ki d'an bamu wuri kamar minti biyar" wani irin razanannan kallo Clarah ta mata jin abinda take cewa cikin takaici ta mi'ke tana jin zuciyarta na suya fuuu zatai gaba dakatar da ita Yusairat tai ganin kamar yanayin ta ya sauya tace.

"Am Clarah kiyi hakuri fatan hakan bai 'bata miki rai ba"?.

Jin tambayar data sake jefo mata yasa a fusace ta juyo tana huci ji take kamar ta rufeta da duka muryarta cikin fushi tace.

"Eh".

Tana fad'in haka tayi gaba da kallo Yusairat ta bita kafin ta sauke numfashi tasan Clarah da rashin fahimta maybe yanzu har taji haushin ta share batun tai tana maida hankalin ta kan Asad tace.

"Asad idan baza ka damu ba zance ina sonka"?.

Daina abinda yake yi yayi yana d'agowa ya zuba mata ido na wani lokaci baice komai ba daga baya ya mayar da hankalin sa kan laptop shiru Yusairat tai a ranta tana ayyana Allah yasa ba 'bata masa rai tayi ba saidai ba yadda ta iya dole ta kasa ha'kuri gara ta fad'a masa ta hutar da zuciyarta muryarta da damuwa tace "kayi hakuri nasan zakaji mamaki taya na iya furta maka saidai bazan yi maka 'karya ba na dad'e da kamuwa da ciwon son ka tun ranar dana fara ganinka nayi kokarin dannewa amma na gaza kayi hakuri zuciyata tayi nisa a halin yanzu tana gaf da fashewa bazan iya jurewa ba" tana kaiwa nan ta mi'ke zata bar gurin jiki a sanyaye taji saukar muryarsa.

"Yusairat Bikirah (Abbakar) meyasa kika bari zuciyarki tayi rauni ta kamu da soyayya alhalin kamata yai ace kin ri'ke aikin ki why"?.

Ji tayi hawaye yana zuba mata dama ta sani bazai amince mata ba amma dai duk da haka gara data fad'a masa ya sani.

"Me kike tunani"?.

Kai ta girgiza "babu komai kayi hakuri".

"Ok yayi zaki iya tafiya ki tabbata kin mayar da hankalinki kan aikin ki kada ki sare akwai nasara a gaba".

"Shikenan Asad na gode sai an jima" tana fad'in haka tayi gaba a harabar part dinsu ta samu Clarah zaune ta zuba tagumi zuwa tai tana zama a kusa da ita d'agowa Clarah tai idonta yayi ja kallo d'aya taiwa Yusairat ganin alamar kuka tai yasa tace.

"Meya faru kuka ki kai"?.

Kai Yusairat ta girgiza tana sake goge hawayen fuskarta tace "nayi kuka ne saboda zuciya ta batai min adalci ba taya zata kamu da soyayya bayan ni kuma aiki nazo ba shirme ba".

Zaro ido Clarah tai jin abinda take cewa har 'kwaruwa take wajen cewa "soyayyar wa"😲?.

"Clarah soyayyar Asad ina cikin matsala na shiga rud'u tabbas na mayar da hankalina kan aikina amma yanzu Asad nake so nake mafarkin samu Clarah ke kanki kin sani Asad na dabam ne taya bazan haukace akansa ba in masa son da ban ta'ba yiwa wani mahalu'ki ba kuma aurensa zanyi shine burina".

Tab Yusairat na rufe baki Clarah ta zabura tai cikin tashin hankali tace "what kina sonshi kuma aurensa zaki"?.

Kai Yusairat ta d'aga "eh haka nace masa kuma ina matukar sonsa koda ace shi baya sona indai ya amince zai aure ni a haka zai zauna dani a shirye nake".

Wani ba'kin fitinannan kallo mai ma'anar kin samu ta'bin 'kwa'kwalwata ne? Clarah tai mata tana cewa "amma wallahi Yusairat kin bani mamaki ban ta'ba zaton haka daga gareki ba shin dama soyayya zatai tasiri a kanki ai na dauka jarumtarki bazata bari ba karki manta abinda kika ce shekarun baya aiki ne ya kawo ki ba shirmen soyayya ba mune muka zo soyayya damu ta dace dan haka me zai hana kici gaba da zama a hakan".

Girgiza kai Yusairat tai cikin gazawa tace "bazan iya ba Clarah ina son Asad da dukkan zuciya ta nayi nisa a cikinsa please ke bakya gani ne ki kokari ki fahimce ni man"🤔 had'e rai Clarah tai cikin takaici tace "na fahimce ki shikenan abar maganar ta isa haka" kallonta Yusairat tai kamar zata ce wani abu sai kuma ta fasa kawai ta 'kyale aje a hakan saidai tasha mamaki ganin kamar Clarah ta nuna kishinta a lokacin datace mata ga wanda take so kuma tana fatan Allah yasa Clarah bata fad'a cikin son shi ba inko haka ta faru zata iya bar mata komai batare data damu ba amma banda Asad.

Bayan wani lokaci iya 'kokari Yusairat tayi na ganin ta shawo kan Asad domin ya sota amma abun yaci tura karshe ya bata za'bi ya kuma fad'a mata gaskiya shi baiji sonta a ransa ba idan kuma tana ganin zata iya aurensa a haka ya bata dama ranar tayi farin ciki ta 'kara ta kuma amince koda bazai ta'ba son nata ba zata aure shin jin wannan batu ba 'karamin kad'uwa Clarah tayi saidai ta sami wani wuri ta 'boya tasha kukan ba'kin ciki gabadaya tabi ta lalace ta rasa me yake mata dad'i har ciwon zuciya ya sameta kullum tana hanyar asibiti a haka tafiya taci gaba da mi'kawa har lokacin da Yusairat ta bukaci a d'an bata kwanaki ta jima rabonta da gida zataje bayan ta gama shiri saida taje sukai sallama da Asad kamar ta fasa tafiya saboda dashi haka taji da'kyar tabar gurin sa yana zaune yana aiki ta shiga 'bangaren Clarah amma neman duniya bata ganta ba ta kira wayarta ba'a d'agawa ha'kura tai ta koma tana sanarwa Asad cewa idan Clarah ta dawo ya fad'a mata tafi sati uku zatai ta dawo bata dau wasu kaya masu yawa ba kawai tahau motar dazai kaita airport ta wuce.

Clarah dake gefen titi zaune a cikin mota ganin Yusairat ta fito tana mi'kawa d'an taxi din kud'in sa yasa tayi wani irin murmushi tana jinjina kai tare da kunna motar da mugun gudu ta figeta tayi kan Yusairat data juya ta fara tafiya gadan-gadan ta nufeta cikin tsana da kishi tana zuwa gaf da ita ta sake d'iban motar da gudun gaske ji kake gammmmmm ta sureta ta tafka da kasa tabi ta kanta ta wuce a d'ari tabar gurin tunda dama abunda ta 'kudura kenan kuma burinta ya cika sai datai nisa da gari ta tsaya tana fita a motar ganin yadda jini ya 'bata tayoyin yasa da sauri ta d'auko fetur ta bulbule motar dashi ta 'kyasta ashana faaaa ta kama da wuta cikin azama tabar gurin tana wata irin dariya ta farin ciki ji take kamar ta sauke wani 'katon dutse dake kanta.

A halin data bar Yusairat kuwa cikin jini faca-faca abun babu kyan gani mutane sun taru a kanta babu wanda ya santa a ciki amma anyi dace da akwai wani soja dayazo giftawa ya gani shima da'kyar ya ganeta saboda yadda Clarah ta sauya mata halitta a gigice ya d'aga waya ya kira Isham ya fad'a masa wanda Isham tsabar rud'ewa bayan ya sanar da Asad ko mota basuyi tunanin hawa ba a kafa suka zo an cika guri yayi ma'kil ta tsakanin mutane Asad ya samu ya shiga tana kwance cikin jini sai juya kai take cike da azaba da sauri yayi kneel down a gabanta ya ma kasa magana sai kallonta yake cikin tashin hankali Isham ne yai 'karfin halin cewa.

"Asad meka tsaya kallo ya kamata mu kaita asibiti🏥🚑 yana rufe baki sukaji jiniyar motar asibiti ta karaso gurin shikam ba maharraminta bane shiyasa koda wasa bai ta'ba taba haka aka dauketa zuwa asibiti likitoci sun rufu a kanta sai aiki suke amma basu iya ceto ranta ba ta rasu lokacin da suka sanar da Asad baisan a wanne yanayi yake ba magana ma aiki ta zame masa kawai iya abinda yake gani a idon zuciyar shi shine abinda ya faru a baya rayuwar su irin yadda take da jarumtaka lokaci guda yau an wayi gari rana ta fito babu ita iyacinta kenan Shikenan.

Da Clarah ake komai harda kukan ta na munafirci babu wanda yayi zaton itace silar mutuwar Yusairat haka ta fitittike har Bangkok taje saida aka gama komai suka dawo Marshall islands harda zama wata so silent😔 ta daina wargi duk dan kar a zargeta daga baya irin wai abun nan ya zama jiki sai tazo ta ware ta kama harkokinta kullum ta dage ta kara azama dan Asad ya yabeta kamar yadda yake yabon Yusairat yace ita jaruma ce shishshigi iri iri har ta samu suka 'kulla abota amma baya baya ita kuma abin nata harda za'kewa ta nuna soyayya fili 'karara baiji mamakin ta ba dan yasan dama za'a rina yaga take taken ta tun a wancan lokacin bai nuna bane kawai ya share ta.
Chapter 57 · 0% Book details