← Book details Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 145

Sashe 43

Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Katse shi Ramatu tai da cewa "a gurin kaba sakarai ni a gurina bai cancanta ba bani da had'i da ita" mikewa Ilyah yai takaici ya gama cika shi domin ta gama 'kureshi amma bai nuna mata ba yace "Ki tashi muje dan Allah ki dubota" wani kallo Ramatu tayi masa tana cewa "uban waye zaije dubo Salamatun amma dai bani Ramatun ba wai Ilyah meke damunka ne ka fara haukacewa kome ka manta ita muguntar da tai maka kazo saika wuni a rana tun daga safe zuwa dare biyar bata bata shigo maka ba wallahi Babu inda zanje na dubata Allah yasa ma ta mutu"😲 shiru Ilyah yai yana kallon ta ya kasa magana tsaki tayi "meye ne ka wani tsaye tserere a akai na kamar bishiya ko bakiji yaren da nai maka magana dashi bane? nace bazanje asibitin ba kuma kaima in kaje ban yafe maka ba" zaro ido yai cikin mamaki yana kallon ta zaiyi magana sukaji sallama duk kallon gurin sukai Habu ne ya shigo yana durkusawa a gaban Ramatu yace "babah ina kwana"? Baki da ido Ramatu ta bud'e tana kallon sa tace "tofa jama'a yau za'ai ruwa da 'kan'kara a garin nan Habubakar yaushe rabon duniya da ayyaraye kaine a gaba na kake gaida ni ko kuma mafarki nake"?.

'Dagowa Habu yai cike da mamaki yana kallon ta abinda kullum sai yazo ya gaida ita wata rana harda aje mata kud'in goro yake amma zata ce yaushe rabon duniya da ayyaraye tab lallai Ramatu ta fara gigin tsufa kawai yabar abun a matsayin haka katse masa tunani tai "Habubakar dakai fa nake ko kaima kazo ne ka fad'a min Salamatu na asibiti" kai ya girgiza yana cewa "a'a nazo ne na fad'a miki an samu 'karuwa a gidana yau da asuba Allah ya sauki Binta lafiya mun samu namiji kuma ranar sunan za'a d'aura min aure da A'i" zaro ido Ramatu tai har batasan lokacin da tace "Binta ta haihu namiji na shiga uku na lalace wannan wanne irin bala'i ne da masifa kaji fa Ilyah sai haihuwa suke tayi amma kai ka ma'kalewa waccan mayyar tsinanniyar bunjinjimar matar taka wacce batasan komai ba saici kamar jaka tazo a 'kai'kashe ta samu arziki ta bararraje yanzu gashi ta zama kamar alade ko'ina bulbul ba rama ai wallahi tallahi Ilyah a satin nan saika auri Maimuna na gaji ace har yanzu baka da d'a ko daya Sabi'u 'ya'yansa uku ga Habun ma daka girmeshi gashi shima yayi biyu ehe uban me ka tsaya kallo" ran Ilyah a 'bace yace "to haihuwa ai ba ita bace kuma ba'a girma ko 'kan'kanta bane ina ga makocinmu nan malam na gabas ya tsufa tukuf amma baida d'a ko daya kuma ga d'an uwanki Hashimu inace shima bai ta'ba haihuwa ba saini zaki takurawa".

A masife Ramatu tace "dan gwafar ubanka ni kake cewa ina takura maka saboda bankad'a ta same ka"? Shiru yai yana kallon wani gun daban ganin bai tanka ba tacigaba "kasan Allah wallahi a satin nan saika auri Maimuna babu fashi kaji dai ko na fad'a maka garama ka sani" Ilyah bai sake magana ba yasa kai ya fita a gidan tsaki Ramatu tai tana bin kofar da harara mi'kewa Habu yai ransa babu dad'i da yasan abinda zaizo ya tarar kenan ba baizo ba kallon Ramatu yai yana cewa "shikenan zan tafi sai anjima ni zan koma" binsa da kallo Ramatu tai tana cewa "to ka gaida mejegon Allah ya raya" Amin Habu yace yana fita cizon yatsa Ramatu tai tana mi'kewa ta dauko gyalenta tana yin hanyar fita sai magana take ita kad'ai "wallahi Ilyah baka isa ba hauka ma kenan haka kawai kana zaune kara zube ba tsuntsu ba tarko aradu a kwana bakwai dinan saika yi aure kaga hauka.

Bara'atu na kwance a kofar d'akinsu kandiya tana gefenta ta ji'ka magani sai yi take da bakin ta akan ta tashi tasha ta'ki saboda batasan magani kallonta ta kumayi "wai bara meke damunki ne? dama kina da ciki baki fad'a ba amma meyasa kikai shiru Ilyan ya sani ne? Kai Bara'atu ta girgiza "a'a bai sani nima kaina bansan dashi ba badan kin fad'a ba" zaro ido kandiya tai tana cewa "ah lallai kam sannunki da rashin hankali wato cikin na jikin ki kice bakisan dashi ba nifa abin fitina ne banaso Dan ina tsoron jarabar Ramatu kar tace bata yarda ba bazasu kar'ba ba ya kamata kisan yadda zaku had'u dashi ki fad'a masa gara yasan kina da ciki kinji ko".

Kai ta d'aga "to zan fad'a masa saiyazo" zaro ido kandiya tai "sai yazo kuma? Anya bara kinsan me kike cewa kuwa yanzu zuba ido zaki sai ranar da Ramatu ta barshi yazo inda kike, tabdijan to bari kiji sanki 'kanin kafarki idan kina neman zaman lafiya ki tashi kije ki nemeshi ki fad'a masa inta kama kije har gidan" tashi zaune Bara'atu tai tana kallon kandiya tace "zanje amma yanzu bana jin dad'i saina ji sauki" dauko maganin kandiya tai"shikenan kar'ba kisha" kar'ba tai tasha sannan ta aje kofin tare da komawa ta kwanta.

Kwana biyu likitoci suna aiki akan Salamatu amma shiru sai uban ma'kudan kud'i ta ake ci daga ase wannan sai ase wancan gabadaya Sabi'u da habu sun gigice ciwon nata ba sauki sai gaba yake yau idan anyi gwaji ance ciwo kaza ne gobe wani dabam za'a gani hatta likitocin mamaki suke ba'a ta'ba kawo musu patient irin wannan ba.

Asabe na zaune ta zuba tagumi tai shiru sallama Markah tai amma shiru bata amsa ba mamaki ya kama Markah saida tazo saitin kunnenta ta sake rafka mata sallama a firgice Asabe ta d'ago ganin Markah yasa ta sauke ajiyar zuciya batare da tace komai ba sai kallon bahon dake gaban ta tai waken 'kosai ne data sayo ta zuba masa ruwa harya kumbura ya tsotse tana tunani bata sani ba tsaki tai tana sa 'kafa ta ture bahon tana huci zama Markah tai tana sake karantar yanayin Asaben tace "ya akai ne kawata naga kin zauna shiru ko har yanzu maganin bai ciba Balaraben baizo ba ne"?.

Kai Asabe ta d'aga tana cewa "ina yazo kuwa dama yanzu gurin ki nake shirin zuwa Markah na gaji har yau ba wani labari gaskiya muje ki kara rakani gurin bokan nan kila ma baiyi aikin ba kawai kud'i na ya cimin wallahi bazan ta'ba yarda ba saiya biyani tashi muje" katseta Markah tai "a'a Asabe dan Allah ki saurara kiji na tabbata bazai cinye miki kud'i ba 'kadaga aikinsa mai kyau ne" mikewa Asabe tai "a'a nifa banason dad'in baki kawai in zakije ki tashi muje" markah zatai magana yaro yai sallama yana cewa "wai inji wani mutumi wai yana sallama da Asabe" da sauri asabe tace "wani kuma ya sunansa"? "Nima ban sani ba amma yace Balah" da mamaki Asabe tace "Balah kuma wanne balan kenan? Shikenan dai jeka kace ina zuwa" fita yaron yai daidai Asabe ta dauki gyale tace "ni waye Balah a garin nan Markah"? Kai Markah ta girgiza "nima ban sani ba Balah dai daya ne baban Tanko kuma ya mutu saboda ba'kin cikin abin da d'an sa ya aikata bayansa bansan wani ba amma kije ki gano ko Balarabe ne" zaro ido Asabe tai "Balarabe kuma anya? Gaskiya da kamar wuya" "to kije ki gano man ina jiran ki" shikenan bari na dawo Asabe ta fad'a tana fita kamar a mafarki ta ganshi tsaye a jikin bishiyar kofar gidan tabbas Balarabe ne amma anya ita yake nema amma bari ta jarraba 'karasawa tai tana masa sallama ga mamakin ta sai taga ya washe baki yana amsawa "am kaine kake nema na"? "Eh nine fa Asabe kinji mamaki ko kiyi hakuri dan Allah abinda ya faru ranar da kikaje gidana nazo ne muyi magana" numfashi Asabe ta sauke tare da sakin murmushi abun yazo kwarai aiki yaci kallon tai tana cewa "to ina jinka Allah yasa lafiya ina d'iyata Indo"? Da sauri ya amsa "d'iyar ki tana gida lafiya da'kyar ma ta barni na fito sai rigima take wai sai ta biyoni" kai Asabe ta jinjina a ranta tace "humm da dukkan alamu akwai sha'kuwa da so mai karfi tsakanin ka da 'yarka kuma saina rabata.

Abu fa yayi nisa tun Markah tana zaune har ta gaji ta fara gyangyad'i a kan kujera karshe ta kwanta ta kama barci ta dauka abun na wasane taga har ta tashi a barci Asabe shiru to kodai tayi wani wurin ta barta ne tashi tai tana le'ka kofar gida hangosu tai suna tsaye suna hira 'kara murtsuke ido tai ganin da gaske Balarabe ne yasa ta koma tana dariya tace "kai Masha Allah kawar burin ki ya cika saura nawa azo aban alkawarin dubu hamsin cascas nima naje na shana wallahi yau kaza ce abincin darena" tana rufe baki Asabe ta shigo bakinta kamar zai 'bare tana jefar da gyale ya yarfa gud'a tare da tafi tai tsalle ta dire tana rawa tace "ke Markah albishirinki wallahi da gaske Balarabe ne yazo kinsan abun mamaki yadda ya sake yana zuba min zance harda ban hakurin wulakancin da yai min a gidan sa kinsan yana jana da zance karshe sai cewa yai yana sona dan Allah na amince ya aureni kinji wani irin sanyi da naji yana ratsani kai gaskiya na gode Markah aikin bokan nan me kyau ne"

Dariya Markah "aha kin gani ko? Ai dama na fad'a miki karki gaggawa kice aiki baiyi kyau nasan waye bokana shiyasa na kaiki gurin sa dan nasan bazai saki 'kasa a gwiwa ba wannan somin ta'bi ne kika gani Asabe wallahi nan gaba idan kika aje kara Balarabe bai isa ya tsallaka ba muna nan dake zakice na fad'a miki" sauke ajiyar zuciya Asabe tai farin ciki ya gama cikata jiki na 'bari ta shiga d'aki sai gata da dubu hamsin kamar yadda taiwa Markah alkawari ta bata tana cewa "to ko yanzu nasan burina zai cika naga alama ga alkawarin danai miki nan" bakin Markah 'kin rufuwa yai godiya kuwa kamar wanda tayi mata kyautar miliyon ranar wuni tai a gidan sai bayan sallar magriba Asabe tayi mata Rakiya ta tafi gida.
Chapter 43 · 0% Book details