← Book details Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 152

Sashe 87

Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

"In Allah ya yarda,muna fatan haka" is what everyone saying,zuk'atan su Annie taf² da farin ciki suke as they see the matter come to light har ji suke yi kamar za su cire zuciyoyinsu suyi kyauta da su (lolz),Abbah yayi murmushi yana kallon yadda Nusrah ta sunkuyar da kai ta kasa d'agowa ta kalli kowa k'asa² yace "Baby da gaske yanzun ma sake tafiya za kiyi ki barni.?" She smiled and hid her face in his arm tace "Abbah ai kaima za ka sake yin aure",Baba yana kallonsu cike da sha'awa yace "Well,shin yanzun ina ne za muje neman auren? Ya kamata mu sani da wuri" Abbah yana sakin murmushi ya d'ago ya kalli Rafeek yana fad'in "Here is her father,since he is a relative of mine ina ganin ba sai anja da tsayi ba" saurin kallonsa Rafeek yayi da mamakin furucin Abba'n yana fad'in "Ni kuma.?" Abbah ya girgiza masa kai yace "Sure kai ne waliyyanta,saboda haka kai za ka bada aurenta" lumshe ido Rafeek yayi a hankali bcos bai tab'a zaton wannan karramawar da gaggawa ba,ya bud'e idanunsa a hankali yana kallon mutanen parlor'n d'aya bayan d'aya,after a while he swallowed some of the tears of joy da suke son zubo masa,Baba ma da kansa sai da yayi murmushi yana jinjina karamci irin na Abbah yace "is this ur decision.?" Abbah ya gyad'a kai alamun haka ne,Baba ya sake yin murmushin jin dad'i ya furta "Ina tunanin ya kamata ku matan ku bamu guri,u should go inside and wait for us to decide.. Kai kuma Abdullahi sai kaje ka samo shaidu yanzun ba da b'ata lokaci ba saboda ayi komai akan idanunsu" With a happy look on their faces suka amsa sannan duka suka mik'e suka nufi ciki,Yaya Abdullahi kuma yayi waje domin neman wasu daga cikin dattawan unguwar,bayan fitarsa nan ya bar Baba yana waya da wasu daga cikin amintattun abokansa na kusa,kafin wani lokaci parlor'n har ya sake cika da sababbin fuska,a nan Baba ya maimaita musu dalilin kiran na su da niyyar yaji shawaran da za su bayar,kusan duk bakinsu a had'e yake kowa ya tashi magana sai dai kaji ya bada shawaran abunda side d'in su Yaya Abdullahi suka fad'a shi yafi cancanta a bi saboda samun masalaha,cikin k'ank'anin lokaci sai duk ga shi an tafi akan wancan maganar kuma ko da akayi k'uri'a sunfi yawa,dole Baba ya hak'ura ya sakko daga kan nasa ra'ayin ya bi wancan,karo na farko kenan a tarihi da Baba yayi magana ya canja,bayan wasu y'an mintuna duka aka ware waliyyan ango da amarya a nan Baba ya bada sanarwa ga limamin unguwar bayan sallar isha'a za ayi d'aurin auren bcos yana son auren yayi albarka duk da ya so ace an bari sai washe gari Sunday,but the divine plan for the wedding was to be on that day.

Lokacin da aka idar da sallar maghreb aka yi sanarwar d'aurin aure a unguwar kowa mamakinsa da tambayar da yake yi shi ne auren waye za ayi a gidan *ALHAJI BABA MUHAMMAD* former parliament yake,bcos zuwa lokacin duk wasu y'ay'ansa na cikinsa maza da mata duk ya gama aurar da su,,kamar yadda aka tsara bayan an fito daga sallar isha'a aka d'aura auren *NURAAZ BIN HAUWA* and his bride *NUSRAH ABUBAKAR KUMO* auren da ya tara d'umbin jama'a,ka-ma daga kan y'an siyasa har zuwa manyan y'an kasuwa,yadda k'ofar gidan ya cika mak'il da mutane u wouldn't think a yau kad'ai ne aka yi sanarwar d'aurin auren ba,sai dai bayan gama d'aurin auren ne kuma wasu k'ananun maganganu began to arise as a result of a change in the name of the groom,instead of his surname ya sakasance sunan mahaifi sai aka ji sunan mahaifiya,nan take wad'anda basu san badak'alar da ta faru ba suka fara cece kuce,while those who are well versed kasuwarsu ta bud'e they begin to recount what happened since then,kafin lokaci mai tsayi labarin ya baza ko ina,abunku da maganar ya shafi manya kuma y'an siyasa.

A ranar su Annie didn't get a chance to go back to Sardauna crescent a nan k'ofar Na'isa suka kwana kasancewar yadda mak'ota suke shigowa yi musu Allah ya sanya alkhairi so they decided to spend the next day,misalin k'arfe goma na daren suna zaune cikin bedroom Annie ta shigo lokacin dawowarta kenan daga kiran da Yaya Abdullahi yayi mata ta nemi guri ta zauna tana kallon Lolly dake cike da fargaba,yadda Lollyn tayi zugum tana tunani sai ka rantse da Allah tana da masaniyar abunda yake faruwa a can waje,ajiyar zuciya ta sauke da fad'in "Allah ya kyauta",dai² nan Nuraz yayi sallama a bakin bedroom d'in tare da Bareerah wacce Annie tace ya taho da ita lokacin da ta aike sa can gidan bayan an gama d'aurin auren because she felt that if they had left her alone there kamar basu kyauta mata ba,saurin d'agowa Nusrah tayi jin muryarsa a daf da k'ofar d'akin cikin kame² bcos a time d'in daga ita sai wani women sleeveless kanta ko d'an kwali babu,before she made any attempt ya shigo ciki,a daburce ta bisa da kallo,suna had'a ido taji gabanta ya yi wani mugun fad'uwa saboda kyau da yayi a cikin kayan da ko a mafarki bata tab'a tunanin yana sawa ba,milk color shadda ne a jikinsa babban riga da y'ar ciki banda kyalli da haske babu abunda yake yi uwa uba kuma k'amshin scent's d'insa da suka cika d'akin,har ya gama yiwa Annie bayanin aiken da tayi masa zai fita yana ankare da yadda take kallonsa,cikin zolaya yana daf da k'ofa zai fita he look back at her had'e da mata winking then ya fita,tana ganin ya fice ta had'iye saliva's da kyar tana sakin nauyayyun ajiyar zuciya,Annie ta kalleta tana tambaya "Daughter lafiyarki k'alau kuwa?" A d'an tsorace ta kalli Annien tana son tambayarta but she could not speak,ganin haka yasa Annie girgiza kai tana b'ata rai tace "Tashi ni ki ba ni guri tunda wankan yana miki wahala" sumi-sumi ta mik'e ta nufi bathroom,bayan shigarta Annie tana kallon Lolly and exclaims "Wai yau lafiyarki k'alau kuwa?" D'agowa tayi ta zubawa Annie ido ba tare da ta ce komai ba,Annien ta harareta tace "kin zuba min ido and u didn't even talk to me,i said are u okay?" Lolly gives her a kind of smile but kallo d'aya za kayi masa ka gane irin a babu yadda mutum zai yi ne ya yisa,Annie ta tab'e baki trying to talk to Bareera ta ji Lollyn ta furta "I just don't know what's wrong with me,but haka nan yau duka nake jin fad'uwar gaba" Bareerah tayi mata sannu,Annie kuma was advising her to pray,if something was about to get out of her window it will come to her with ease.
Chapter 87 · 0% Book details