Sashe 121
Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Bayan gama d'aurin aure aka yi walima,na maza daban na mata ma haka,da yamma aka kai amarya asalin gidanta dake nan cikin garin Kano,kada kuso ganin yadda y'an uwa suke zuba santin gidan Annien musamman yadda aka tsara komai bisa wayewa da ilimi,komai na ciki an sauya an zuba sabo gwanin burgewa,shi kansa gidan sai ya zama kamar sabo irin wanda ba'a tab'a shigarsa ba,bayan y'an rakiyar amarya sun fara tafiya duka da yake dama ba wasu mutane ne na daban ba,y'an uwane kawai,gida ya rage lolly,Nusrah sai Bareerah kasancewarta y'ar amana,sannan a yanzun su duka suna yi mata kallon wata ta jikinsu saboda halacci,duk inda suke suna tare da ita ba-sa barin wani abu ya sameta ko ta wulak'anta,suna zaune lokacin kafin su tafi Annie ta kallesu ta yi shiru,because har lokacin bata gama yarda wai ita ce tayi aure ba,ta fi ganin abunda yake faruwa irin a mafarki d'in nan,Lolly da suke hira jin shirun na ta ya yi yawa ta kalleta fuskarta da fara'a sosai tace "Adda tunanin me kike yi?" A hankali Annie ta kalleta hawaye suna taruwa a idonta tace "Ina tunanin rayuwar mu ne a baya,yanzun da komai ya zama tarihi sai nake ganin kamar duk wad'annan abubuwan sun faru ne a mafarki!" Lolly tayi murmushi mai cike da nutsuwa tace "Haka ne Annien mu,amfanin bawa ya kasance mai hak'uri,juriya da addu'ah kenan,duk abunda ya same shi idan lokacin ya wuce sai ya dunga ganin kamar ba'ayi ba",Nusrah tayi dariya tace "Laaahh! Aunty kema Annien kika ce?" Duka suka yi murmushi,Annie ma ta yi murmushi mai tafe da hawaye,Lolly tana rik'e da hannunta tana kallonta take bawa Nusrah amsa "Tabbas Angel! Adda maryam ta cancanci na kirata da sunan mahaifiya,kasancewar tun ban gama wayo ba mahaifiyarmu ta rasu,daga wannan lokacin ta sakance ita take yi min komai,bayan ita ban san kowa ba,kasancewarta mutum ta farko da tunda na zo duniya bata tab'a gwada min k'iyayya ba,ta so ni da dukkan zuciyarta,ta zauna da ni a lokacin da na rasa hankali,ta kasance mai sadaukar da farin cikinta akaina,shin idan ban kira wannan matar mahaifiya ba da wane suna ya kamata na kirata?? Matsayinta a gurina ya wuce y'ar uwa kawai,idan har akwai wata mahaifiyar a bayan wacce ta kawo ni izuwa wannan duniyar tabbas zai kasance ita ce,tarbiyyana da komai itace,idan na yi kuka ba ta samun nutsuwa har sai ta ga na yi dariya,idan ina farin ciki tana yin sama da nawa,for nothing other than ban yi kuka ba,itan y'ar baiwa ce kuma abun alfahari a gurin kowane ahali,tabbas da ace ana iya tambayar mutum lokacin da za'a raba shi da wanda yake so,a lokacin da mutuwa ta kusanci d'aya ko a bashi damar musanyawa da wani abu,hak'ik'a da na rok'i a barmin ita,na musanyata da sauran dangina,duk da mun kasance bamu tashi mun san dangin mahaifiyarmu ba a kullum suna nan a cikin zuk'atanmu,muna marmari da begen ganinsu ko da sau d'aya ne a rayuwa kafin mutuwa ta riske mu ko su d'in,sai dai har zuwa yanzun muna k'aunarsa ne kawai amma su d'in babu wanda ya damu da rayuwarmu bare su neme mu,ko su san halin da muke ciki,har yanzun bamu samu wani mutum d'aya wanda a tarihi za mu nuna muce ya fito daga dangin mahaifiyarmu ba,shin a wannan zamanin da muka kasance muna rayuwa mu kad'ai idan bamu so juna ba waye za mu so? Dangin mu basu damu da mu ba,basu san inda muke ba,babu wanda yake kulawa da mu,suna nan a raye ko sun mutu bamu sani ba,amma kasancewata tare da ita yasa a kullum na kasance ina yiwa Allah godiya tare da jin cewa ban rasa ahali ba,ba don komai ba sai saboda itan ta kasance d'aya daga cikin ahalina,tabbas ina alfahari da samunta!" Hawaye su duka suka share saboda yadda maganarta ta tab'a musu zuciya,Annie kuwa gaba d'aya ta kasa samun bakin magana banda hawaye babu abunda take sharewa,Lolly tayi murmushi tace "Saboda haka nake jin idan na kira ta da sunan Mahaifiya ban yi ba dai² ba.." Sun jima sosai a gidan yayin da duka hirar ta su ya kasance kalmomin yabo ga Annie da labarin rashin sanin inda ahalin mahaifiyarsu suke,a nan itama Nusrah zuciyarta ta cika taf da begen nata ahalin mahaifiyar har ta sake k'udurcewa a ranta lallai za ta sake yiwa Abbah magana ko da ace ba zai kaita ba lallai tana buk'atar ya ba ta address,ita da kanta sau ta neme su,wajen misalin k'arfe 9:00pm suna kan yin hiran Nuraz ya kira ta,tana d'auka bayan ta yi sallama,maganarsa a low tone yace "Madam kin manta da ni gaba d'ayan" tayi murmushi da sauri ta tashi ta haura sama,tana cewa "ta yaya zan mantawa da rayuwata? Idan na manta da kai ashe zan manta da kaina" yayi murmushi yace "kawai kince haka ne Madam,but na san hidima yasa an manta da ni,tunda ga shi daga zuwa rakiya ank'i a dawo" tana kwanciya a saman bed d'inta na gidan tace "No! Ba haka bane fa,kawai dai babu dad'i mu taho mu barta ita kad'ai ne,su Abbah muke jira har yanzun su zo,uhn! Sai nake jin ma kamar na kwana a nan" yayi murmushi yana cewa "to ko za ki gwada?" Tana dariya tace "Idan ka fad'a ba zan k'i ba" ya jinjina kai yace "Wai sai yaushe za ku taho?" Tace "Muna jiran su Abbah su zo" ya tab'e baki yana adjusting kwanciyarsa yace "Ni dai a dawo da wuri a san yadda za'ayi da ni" murmushi tayi muryarta a low tone tace "Me zan yi?" Yace "Ohooo! Kin fi kowa sani" ta shagwab'e tace "well,kawai ka zo mu tafi" yace "Ke kina wasa ko? A hakan zan wani biyo ki? Ko so kike na yi miki ciki a gabansu?" Kyalkyalewa tayi da dariya tana rufe baki tace "Allah yasa ban ji abunda kace ba" shi kansa sai da ta fad'i hakan ya tuna me yace,yayi dariya yace "idan kuma kina so nazo shi kenan dama ai muna da d'aki a nan right?" Ta kad'a kai tace "Ehh muna da shi" yace "Shi kenan ga ni nan,yau a nan za mu kwana",tayi sauri ta katse shi "wai da gaske kake yi?" Yayi dariya yace "absolutely sure" tace "Ka rufa min asiri kayi zamanka,yanzun za mu dawo" cikin zolaya yace "A'aahh! Dama ai asirinka a rufe yake" Tace "Pleasee!" Tana shagwab'ewa,da kyar yace mata ya yarda but tayi sauri,idan ba haka ba zai biyo sahunta,ta amsa tana dariya,tana gama wayar ta fito tana murmushi ta jiyo maganar Father In-law d'inta yana tsokanar Lolly,tayi dariya a fili tace "hali zanen dutse!" Ta sauko k'asa lokacin ta tarar da su har sun mik'e za su tafi,ta kalli lokaci taga 10pm yayi,here tayi realizing sun b'ata almost one hour suna magana,a gurguje taje ta d'auki kayanta suka yiwa su Annie fatan alkhairi had'e da sallama,kamar kada su tafi haka suka dunga ji sai da Rafeek yayi da gaske yasa su gaba yana zolayarsu sannan suka fita suna waiwayen Annie kamar wanda ba za su sake had'uwa ba,a mota suna tafiya kasancewar Lolly ce a front seat kusa da Yallab'ai dake jin tuk'i da kansa,Nusrah ta zauna kusa da Bareerah a back seat,da yake mota d'aya suka zo da shi babu security,Rafeek sai tsokanar Lollyn yake yi ganin tunda suka taho tayi shiru ta kasa cewa komai,fuskarta duk ta nuna damuwa,lokacin kuyinas their car parked tun da bikin ya matso yadda take shige da fice ya sake mata suna yake kiranta da *KIN FI AMARYA*,duk lokacin da yaji tsokana da hakan yake kiranta,basu yi nisa ba ta biye masa lamari ya canja salo,kunyar tafiyar nasu tare yasa gaba d'aya Nusrah ta kasa motsawa tana jin kamar ta shige cikin seat d'in,har suka iso gida tunda ta rufe idanunta sai da taji sunyi parking sannan ta bud'esu a hankali ta kalli harabar gidan,as their car parked guards suka bud'e ta fito da sauri cikin jin kunya,duk gaisuwar da suke yi mata bata tsaya amsawa ba ta shige ciki da sauri,tana shigowa bata jita ba direct ta nufi bedroom d'in da suka sauka,a nan ta tarar da Nuraz kwance daga shi sai nickers yana waya,tana shigowa yayi mata alamar barka da zuwa,ta kalleshi tana yin murmushi da sauri ta ajiye jakarta ta wuce bathroom,lokacin da ta fito ya gama wayar yana dai kwance har lokacin,yana ganin ta fito ya sakko daga saman bed d'in yana yi mata wani irin kallon dake narkar mata da zuciya,tayi baya a hankali tana sakin murmushi,yace "ina za ki je kuma?" Ta kad'a masa kai,abunda ya faru a mota ya dawo mata a rai ita kad'ai ta kyalkyale da dariya,ya rik'o ta yana cewa "What are u laughing?" She nodded again tana b'oye d'uriyarta,ya rik'o waist d'inta yana cusa kansa tsakanin neck d'inta yace "Ba ni labarin naji" Tayi ajiyar zuciya tana sake yin murmushi tace "nothing" yace "anya zan yarda babu komai?" Tace "why not?" Because da kunya ta iya fad'a masa abunda ta gani,daga nan ya d'aga ta yace "ok! Muje a ba ni kulawa" tayi dariya tana kai hannunta saman beard d'insa.
*****
*****