← Book details Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 152

Sashe 38

Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Yana kallon sanda motarsu ta bar gurin but ya kasa motsawa,almost 30 minutes ya d'iba a gurin yana tunanin anya itace ko kuwa mai kama da ita ya gani.!? Wata zuciyar tayi saurin fad'a masa
"Wannan fa ba kama bane kawai,ita ce da gaske.."
Saurin katse tunaninsa yayi ya juya ya fara bin inda suka yi da kallo,but ko alamar su bai gani ba,da sauri ya juya ya nufi inda driver'nsa yake,tun kafin ya k'araso cikin hayaniya da wannan tsadadden turancin nasa yace "Hey.! tada mota muje.."
A rikice baturen ya juya ya yi tunanin ko wani abu ke shirin faruwa a arean da suken,ya bud'e masa mota Rafeek na shigewa ya rufe yayi saurin fad'awa shima ya tada mota ya juya ya d'auki hanyar da zata mayar da su gida da mugun gudu.

RAFEEK dake zaune a baya ya zuba idanunsa kan wayarsa yana kallo da tunani mai zurfi not knowing where they were going sai da suka shigo carport drivern ya gyara parking ya fita ya bud'e masa yaji yana fad'a masa sun iso,,ya d'ago zai yi magana ya gansu a cikin mansion,a fusace bakinsa har wani kyarma yake ya taune lips yana matse forehead d'insa,yana d'agowa ya kwashe shi da wani irin gigitaccen mari,cikin hayaniya yace "Here i insisted u to brought me.!?"

Baturen yana dafe da cheeks d'insa ya furta "Sorry sir"

Cikin hayaniya Rafeek yace "Ka ci ubanka kai da sorry d'in"

Duka maidservant dake harabar mansion d'in suka fara sauke kawunansu k'asa bcos sun san masifar sa babu wanda ba zata shafa ba musamman idan yaga wani yana kallonsa,a zafafe ya koma mota cikin masifa yace "bring me back to where u take me.. Quickly.!"
Saurin fad'awa mota drivern yayi yaja a 360,guard d'insa suka dafo musu baya,da mugun gudu suka d'auki hanyar komawa 9 Albert street,a bakin Store na Ali Jerich suka yi parking,tun kafin motar ta gama tsayawa Rafeek ya fice yana dube²,guards d'insa suka dafo masa baya suma suna tayasa duk da basu san mene ne actual abunda ya kawo su ba,ya koma dai² inda ya tsaya d'azun yana dubawa,yaga babu alamun su,a hankali ya lumshe idanunsa yana juya kansa kad'an²,Clark ya matso kusa da shi yace "Sir.!"
Da sauri ya bud'e rinannun idanunsa ya watsa masa wani irin kallo,a masife yace "Who told u to came.!?"

Clark yana raba ido yace "Sorry sir"

A masife Rafeek yace "Sorry for ur self."

Ya juya ya ci gaba da dubawa,almost 2 hours suna wajen mall d'in yana duba ta inda zai ganta but shiru,tun daga kan motocin dake parke a gefe har wad'anda suke wucewa amma ko mai kama da ita bai gani ba,again Clark bai yarda ba ya matso kusa da shi da niyyar ya tambaye shi ko zai fad'a musu abunda yake so sai a duba musu record na CCTV cameran mall d'in,Rafeek ya juyo da sauri ya kalleshi,duka shi ba don Clark d'in yayi maganar ba ya manta ma da akwai wani CCTV a gurin,ya girgiza kansa da sauri ya wuce yayi gaba,Clark yace ko zai bari suje su control room,yace A'a basu san me yake nema ba,suka wuce yana gaba har cikin mall d'in,basu jima ba sosai bayan sun samu yin magana da Manager mall d'in aka kai su control room,gaba d'aya Operators d'in aka tara masa su,daga shi sai su a cikin room d'in sai Clark sauran duk ya kora su waje ya fad'a musu abunda ya kawo shi,vedio recording surveillance footage na last 2 hours and half aka fara search,babu jimawa aka masa playing,ya zuba idanunsa a saman screen yana watching,bayan wucewar wasu seconds cam1 ya nuna dai² zuwansu da shigarsu gurin,da aka ci gaba da tafiya cam2 ya sake nuna ainihin shigowarsu mall d'in,duk abunda suka yi da inda suka shiga a hankali cameras suka yi finding out,suna fita camera1 ya sake nuna inda suka tsayar da cab Nusrah na rik'e da ita,abunda ya basu wahala kad'ai shine number cab da suka shiga,duk iya k'ok'arin su na son su gano lamarin ya rikitar da su,hankalin Rafeek a tashe yasa suka fita daga mall d'in,a hakan bai hak'ura ba yasa suka bi hanyar da suka nufa,guards d'insa suka fara k'ok'arin binsa yace su koma gida,ba dan sun so ba haka suka tafi suka kyale su su 3,wasa² tun ana batun counting hour daga 1,abu ya fara tafiya up to 5 hours,sun zagaye duk inda suke tunanin cab d'in sun ta bi,but ko irin colour d'in cab da suka shiga bai gani ba,kan dole ya hak'ura yasa drivern ya juya suka nufi mansion,,suna tsayawa a harabar gidan security'nsa suka bud'e masa ya fice idanunsa sun sauya launi,veins d'in kansa sun fito rad'a² a waje kana kallonsu,bai kula kowa ba duk yadda suke welcoming nasa,ya wuce inda entrance yake,wani irin security door ne na dim glass na ciki zai iya ganin na waje,palm d'insa kad'ai yayi shone daga gefe,door d'in yayi welcoming nasa kafin ya bud'e ya wuce ciki Clark ya biyo shi rik'e da phone da suit d'insa,"Subhanallah..!" Shi ne kad'ai abunda na iya fad'a a lokacin da nayi arba da cikin mansion d'in,fan's duk yadda zan fad'a muku tsarin sa ba lallai ku fahimta ba,but ku hasko kawunanku a ciki,k'arshen had'uwa iya tsari da duk wasu alatun more rayuwa babu wanda idanunku ba zasu hasko muku ba,tun daga kan parlor gidan ya kasance wani irin aljannar duniya ne,chairs kad'ai da aka zuba aka yi decorating sun kai five set a first floor kad'ai,parlor guda d'aya ne amma yadda aka yi ginin da wasu irin pillars da fitilu ke zagaye da shi sai ku yi tunanin sun kai hud'u,ko wanne an masa decoration da different colours,wannan yana wane wannan saboda tsaruwarsa,na tsakiyar shi ne yake d'auke da two set kuma duk ciki ya fi girma,sauran dake zagaye da shi an baza musu wasu irin rantsatstsun royals,dai fitowar wata y'ar dattijuwa data had'e cikin wani rantsatstsen super jikinta sai haske yake gold ta ko ina ga sanyayyan k'amshi da take bazawa ta nufo inda yake k'ok'arin zama saman wasu lafiyayyun armchairs tana tafiya tana kallonsa har ta karaso inda yake "Rafeek.!" Tayi calling nasa out,bai iya d'agowa ba sai da ya kwanta yana sakin wasu irin ajiyar zuciya masu nauyi,ta zauna kusa da kansa tana lumshe ido da bud'ewa ta shafa kansa,saurin juyawa yayi ya rungume ta with his coloured eyes yake kallonta ya kasa magana,hankalinta a tashe tace "Rafeek.! Mene ne yake damunka haka.!? Ka kalli yanayin da kake ciki kuwa.!?"
Yaci gaba da sauke ajiyar zuciya da k'arfi,ta rik'o fuskarsa slowly ta zuba masa idanu,a tsorace ya d'ago idanunsa da suka fara tara hawaye yace "Hajiya.! I've seen it not for awhile" ta tsaya kallonsa kafin ta samu courage na tambayarsa "Wace ce ka gani Rafeek.!?"

Yace "Ita.!" Hajiya da bata fahimci inda zancen sa ya nufa ba tace "Lydia.!?"

Yayi saurin girgiza mata kai,tayi squeezing face tace "Wace ce ka gani d'in Rafeek.!?" Bud'e bakinsa yayi da kyar yace "Hauwa.!"
Wata irin mik'ewa tsaye Hajiyar tayi tana kallonsa da mamaki tace "Rafeek.! Anya kuwa ita ka gani.!?" Ya girgiza kai yana matse kansa da runtse idanunsa,Hajiya ta koma ta zauna tace "Me ya kawo su UK to idan su d'in ne.!?" Da kyar yace "Ban sani ba Hajiya,but am scared don't know ko ta yi aure yanzun.."

Ya k'arasa yana yana had'awa da dafe saitin zuciyarsa,Hajiya ta kalleshi da tausayawa tace "Zai iya kasancewa hakan ne,zai kuma iya kasancewa ba haka ba,amma ni dai abunda nake son fad'a maka kada kasa damuwa a ranka,ka san condition da kake ciki,idan kace za ka sawa ranka damuwa komai zai iya faruwa da kai,ka san kuma abunda bana so kenan,kayi addu'ah in sha Allah idan Hauwa'u rabonka ce zata dawo.." (Hhhh.! Lallai kun makaro)
Ya lumshe idanunsa hawaye suka sauko daga idanunsa,Hajiya tana kallonsa tace "Cry Son.! Cry as if it will make u feel better,cry alot until u feel like ur tears come to an end,ba zan hana ka kayi ba,na san rad'ad'in da kake ji a yanzun bai kai kwatankwacin irin wanda kasa taji a shekarun baya ba" a hankali Rafeek ya zame ya kwanta a jikin Hajiya yaci gaba da kuka sosai kamar k'aramin yaro,Hajiya tana hawaye take ci gaba da shafa kansa,sai da yayi mai isar sa sannan yayi shiru ya ci gaba da sauke ajiyar zuciya,Hajiya ta ci gaba da masa nasiha cikin sanyayyan kalamanta sai da ta tabbatar ya fara samun nutsuwa sannan ta barshi.

*A month leave...*
Al'amari ya tsananta a b'angaren Rafeek,tun daga ranar da yaga Lolly a Ali Jericho Store cikin ikon ubangiji sai bai sake ganin ko da shade d'inta ba bare itan kanta,even though ya saka masu kawo masa report ya baza su a duk inda yake tunanin zai ji wani abu apart of her life,and a kullum cikin jiran tsammanin jin labarin an ganta yake amma shiru duk tsayin lokacin nan.
Chapter 38 · 0% Book details