← Book details Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 152

Sashe 45

Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

***
Da safen bayan tashin Nusrah daga bacci kafin ta sauka daga saman bed she began to check her phone to see whether Aatif had called tana bacci,ta cire lock taga babu miss call bare text,ta ajiye jikinta a sanyaye ta wuce bathroom tayi wanka,duka jikinta a sanyaye tayi shirin tafiya skul,ko breakfast bata jira ta yi ba tayi sallama da su Lolly ta tafi,she said she had morning lecture and the teacher was so hot that she didn't want to miss out,da Annie tace ta kira Yayantan ya kaita,she smiled softly tace ta san bacci yake yanzun,ba sai ta tashe shi ba,za taje ta hau cab kawai,suka mata fatan alkhairi ta fita,since her heart was broken ta fito ta tsaya bakin street ta nemi cab suka wuce,da ta shiga skul ma a time d'in bata da wani lecture kasancewar ranar sai 12 noon za ta shiga class,cafeteria ta wuce ta samu guri ta zauna tayi shiru tana tunani,bayan wani lokaci tayi deciding kiran wayar Aatif,miss call biyar tayi masa amma bai d'auki ko d'aya ba,ta tura masa text message,she was telling him if he saw the call he had to called her back,har to 11 tana zaune cikin cafeteria bai kira ba,ita kuma bata gaji ta tafi ba,still at that time there was nothing da ta ciwa cikinta,she was sitting all the time,,bayan lokaci tana ta zaune she looks out her phone to see whether he calls her ko ita ce bata ji ba,still ta ga wayam,ta gaji da zaman ta mik'e ta fara tafiya a wahalce,yinin ranar babu abunda ta tsinta a skul,lectures d'inma ba sosai ta gane abunda aka yi ba,4 dot suka fito ta kamo hanya tana tafiya ita d'aya cos tana jin ba zata iya tsayawa jiran su Veronica ba kasancewar za suje library,tayi musu sallama ta wuce.

Yadda ya bar wajen a fusace haka ya shige motarsa had'e da banging door d'in da d'an k'arfi,duk dama ba dad'in zuciyarsa yake ji ba cikin week d'in haka ya fizgi motar ya bar arean,sai daya fara zuwa hospital ya kammala aikin da yake yi after then he plans to go to Oxford University to pick her up,4:00pm sharp ya tsaya inda ya saba ajiyeta yana tunani da addu'ar Allah yasa bata koma gida ba,yana zaune cikin motar yana kalle² da tunanin inda zai ganta,can daga d'an nesa da inda yayi parking kad'an ya hangota zaune ta buga tagumi,yayi still yana kallonta na wani lokaci kafin ya cire seatbelt ya bud'e motar ya fita cikin mutuwar jiki,har ya tsaya kusa da ita bata sani ba,ya saki siririn ajiyar zuciya ya zauna kad'an bai yi magana ba,kusan mintuna goma ya d'auka da zaunawa a gurin yaga alamun tayi nisa sosai a hankali ya d'aga idanunsa ya kalleta,gabansa yayi mugun fad'uwa daya kalleta a nutse,yadda tayi zuru² cikin yini guda idanunsa suka hango masa wani irin tashin hankalin da take ciki,a hankali ya kira sunanta cikin muryar tsoro,ya maimaita kiranta ya fi a lissafa bata ji ba,sai da yayi tapping a dai² fuskarta sannan taja dogon ajiyar zuciya a hankali ta kalleshi,suna hada ido tayi saurin lumshe nata idanun,hawayen dake mak'ale trying not to cry tun safen began to pour out,cikin kid'ima yana kallonta da tashin hankali ya kasa magana sai wasu irin saliva's da constantly yake swallowing,yaga ba ta da niyyar dainawa gashi sai kallonsu ake yi,babu shiri ya mik'e ya kama hannunta,jakar da komai nata ya d'auka muryarsa a shak'e da tsoro yace "let us leave the place" ta d'ago kanta tana girgizawa alamun bazata tashi ba,idanunsa ya lumshe ya bud'e yana kallon mutanen dake wucewa suna kallonsu wasu har gulma suke ya sake cewa "get up,kina kallon yadda ake kallonmu fa,kada kisa ayi tunanin na yi miki wani abu" tana kuka tace "Ka yi tafiyarka kawai,ni babu inda zanje" ya kalleta da wani irin fuska yace "Za ki tashi ko sai na b'ata miki rai.?" Ta sake Kecewa da kuka muryarta tana wani irin kyarma tace "Ni ka rabu da ni,idan na tashi ina zanje ne.!? I have no other advantage,what good is my life.? The father who gave birth to me said that he didn't want me,he doesn't need me,amfanin me zan yiwa duniyar da mutanen cikinta.!?" Wani irin tausayinta yaji ya sake kamashi a hankali ya furta "Na ji tashi mu tafi" ta sake girgiza masa kai za tayi magana ya fizgota and talking in agony "What kind of person are u? Ayi ta binki ana maimaita magana d'aya baza ki saurara ba,if u have the right kill urself,akanki aka fara da za'a gama a kanki.!? Su mutanen da kike damuwa da su an fad'a miki dan kin shiga wani halin za su damu ne.!? I don't want a stubborn person,if u can get up idan ba zaki iya ba kuma zan wuce na barki" ta sauke kanta k'asa tana ci gaba da kuka,yana kallonta yace "will u get up.??" A hankali ta mik'e tana had'a hanya yayi saurin rik'e ta yana mata wani irin kallo,suka k'arasa inda ya ajiye mota ya bud'e ya taimaka mata ta shiga sannan ya bud'e back seat ya sa jakarta ya koma d'aya side d'in ya shiga ya tada motar,sai da suka fita daga skul d'in har sunyi nisa yayi parking,bai kalleta ba yace "what happened yesterday.!? Did u talk to him.!?" Ta kad'a masa kai tana goge hawayenta,yace "Ehmn!" Ta d'ago ta kalleshi taga ya zuba idanunsa akan hanya duk da a tsaye suke guri d'aya,ta sake goge hawayen da suka sake tahowa ta fad'a masa yadda suka yi da shi,yayi shiru yana tunani a hankali yace "why don't u call him.!?" Tayi shiru bata amsa ba,ya cire belt d'in ya juya backseat ya d'auko jakarta,tana kallo ya bud'e ya ciro wayarta ya kalla yaga akwai lock ya mik'a mata yace "bud'e",babu musu ta cire yace "call him",ta tsaya kallonsa ya juyo ya kalleta yace "call him" babu musu ta fara kiran line sa,har wayar ta katse ba'a d'auka ba,yace ta kuma kira,ta daure ta sake kiransa still ba'a d'auka,ta sake maimaitawa daf da kira na uku zai katse aka d'auka,tayi ajiyar zuciya a gajiye ta amsa sallamar da yayi,ta daure ta gaishe shi,ya amsa a sanyaye cikin daurewa tace "Why don't u call.!?" Da farko yayi shiru can kuma yace "Am sorry baby,uzuri ne ya rik'e ni that's why i didn't call,but when i got out of the office i would call in sha Allah" tayi ajiyar zuciya tace "Ok.!" Bai jira ta sake magana ba ya katse,Nuraz ya kalleta yace "what did he say.!?" Tace "He said he'll call me when he comes out of the office" ya gyad'a kai yana tab'e baki,a hankali yace "Ok duk lokacin da ya kira ki sanar da ni" har ta amsa kuma tace "Well. I don't know how to tell u" bai kalleta ba yace "za muyi waya.!?" He spoke as if he were asking her permission,ta gyad'a masa kai tace "toh" yace "To ajiye number,duk yadda kuka yi sai ki sanar da ni" ta sake gyad'a kai,ya fad'a mata digit d'in tayi saving,har ya tayar da motar ya juya yana kallonta na wasu seconds bai yi magana ba ya fara driven ya mayar da hankali kan tuk'in suka bar arean,a wani had'ad'd'en eatry ya parker ya fita ya barta a motan,yaje yayi mata lafiyayyen take away ya dawo,tana zaune shiru ya bud'e back seat ya tattara jakarta da komai yasa su gefe ya ajiye mata take away d'in sannan ya koma front seat bai kalleta ba still yace "Koma can ki ci abinci" ta d'ago kanta da sauri ta kalleshi tace "I'm not hungry" ya d'ago idonsa ya kalleta yace "really.!?" Ta kad'a masa kai,ya tab'e baki yace "je ki ci tukuna,the words come later" ta bud'e baki zata sake magana ya kafeta da ido,babu shiri ta had'iye nata maganar ta fita a sanyaye ta koma baya,ta d'auka leather da ta gani ta fara bud'ewa,package ne madaidaici sai bottle water ta fito da shi ta bud'e chicken noodles ne sai tiriri yake,da grille fish da yaji spices a saman,aroma d'in yana bugar hancinta taji yawunta ya tsinke,y'ay'an cikinta suka fara kukan yunwa,a hankali ta d'auki fork d'in data gani tayi bismillah ta fara ci,sam bata yi tunanin haka yake da taste ba abincin yana kallonta ta mirror ta fara cin abincin a hankali,bata wani ci sosai ba ta tattara komai za ta mayar taji maganarsa "what have u done.!?" Ta d'ago a hankali tace "I'm satisfied" ya tab'e baki yace "Kada ki mayar maza ki cinye su,idan kin bari waye zai ci.!?" Tace "Allah na k'oshi" ya girgiza kai "D'an abun da kika cin nawa ne,ko jaririn dake koyon cin abinci aka bawa wannan dai ba isarsa zai yi ba" ta marairaice za tayi masa musu yayi saurin juyowa yana kallonta "Ki cinye nace,nifa na tsani muyi ta jayayya,ke cikin naki ma sai kin masa mugunta.!? Dubi fuskarki da kanki,i think all the day this is what u started eating.. Azumi kike yi ne.!?" Ta girgiza masa kai a hankali,ya had'e rai yace "Maza ki cinye mu tafi" ta lumshe ido a hankali ta bud'e taci gaba da ci,tana jin ta kai linter har kamar za ta yi amai ta d'ago tace "Na k'oshi" ya janye idanunsa akan tablet d'in da yake pressing ya kallota ta mirror,yadda abincin yake kamar yaro ne yaci yasa ya tab'e baki yace "Sai ki fita dashi kisa a trash",ta kalleshi tace "babu kyaufa",ya juyo kad'an yana kallonta yace "If u don't want to pull out,how do u want to deal with it.!? Su nan babu ruwansu da almajirai bare kice a bayar" tayi shiru tana tunani ta d'an kad'a kai a hankali she feels nervous ta bud'e motar,har ta sa k'afarta a waje yaga yanayin dake fuskarta a hankali yace "ba ni nan" ta juyo a hankali tana kallonsa kafin ta mik'a masa ya karb'a,tana kallonsa taga ya bud'e,a hankali yake ci shima d'in kamar baya so,ta jingina da seat ta lumshe idanunta,har ya gama ci ya fita ya dawo sannan ya tada motar,bai damu da zamanta a bayan ba duka ya yi tunanin ko bacci ya d'auke ta,har suka tsaya bakin apartment ya gyara parking yayi shiru yana tunanin tashinta yaji motsinta ya d'aga kansa yana kallonta ta mirror as she collected her belongings tana fita ya biyo bayanta,a bakin entrance suka tsaya duka tana knocking door d'in cikin siririyar murya tace "Thank u" he said nothing Bareerah ta bud'e musu suka shige suna gaisawa da ita.
Chapter 45 · 0% Book details