← Book details Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 145 OF 152

Sashe 145

Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

      Suna fitowa daga wanka bayan sun gama shiryawa,yaga tana shirin binsa su fita yayi sauri ya rik'ota,ta marairaice tace "please Hayat" ya kafeta da kallo yace "what?" Ta marairaice tace "Let me go with u please,ina son zuwa can" kai ya kad'a mata yace "muje ki yi bacci na fasa fita" ta had'e rai za tayi masa musu ya d'auke ta ya kwantar saman bed then ya kwanta kusa da ita yace "Ahaan! Ayi bacci lafiya" kamar za tayi kuka haka ta kwanta tana kallonsa,ya kwantar da kanta a jikinsa yana shafa kwantaccen gashinta har bacci ya fara fizgarta,lokacin da ya tabbatar baccinta ya fara nisa da wayo ya zare jikinsa ya dawo da Maysam kusa da ita then ya fito daga bedroom d'in,yana ratsowa parlor ya tarar shiru sai maidservant kad'ai suke hidimomin su,yana fitowa cikin apartment d'in sun nan d'in ma dai he saw no one sai security dake patrol cikin mansion d'in,yayi murmushi ya wuce apartment d'in iyayensa,yana tafiya zuciyarsa fes wani irin nutsuwa yake ji da farin ciki suna sake huda jikinsa,sai dai me entrance d'in shiga flat d'in yana gama bud'ewa bayan ya gama welcoming nasa,ya d'aga kai yana sakin murmushinsa mai kyau kwatsam idanunsa suka sauka kan Aatif who was sitting there suna magana da Daddy'nsa,yayi still a wajen yana kallonsu his thought kuwa a lokacin shi ne ya koma inda ya fito without ya shiga yayi uzurin da ya kawosa,because to his entire life he didn't want anything da zai had'a sa alak'a da Aatif,a duk lokacin da ya gansa yana tuna abunda ya faru tsakaninsu wancan lokacin and he still felt the pain,his words affected him every time he saw something that would remind him of his presence in the world,shi yasa har yanzun ya kasa sake masa fuska,Daddy'nsa da tun tsayuwarsa a gurin ya gansa yayi masa murmushi yace "Beta!" Numfashi Nuraz ya d'an fesar yana sake had'e rai da yaga duk hankalinsu ya dawo kansa kawai sai ya juya da niyyar barin wajen,duk yadda Rafeek yaso yaji abunda yake faruwa bai iya tsayawa ba yace "Daddy we will talk idan na dawo,i'm just going out" yana fad'an haka ya bar musu wajen cikin sauri,jikin Aatif yayi sanyi because he could see how Nuraz was actually hating him,bayan tafiyar Nuraz bai jima ba shima sosai yace da Rafeek "Abbah zan koma,Allah ya raya" Rafeek ya amsa yana yi masa godiya because ya ji dad'i sosai and shi duka ma kuma bai san da wani matsala dake tsakaninsu ba.

*****

       On Aatif's side kam since ya bar mansion,driven kawai yake but inside him abun da Nuraz da Nusrah suke yi masa yanzun seemed as if they didn't know him yana cinsa a rai,after that kuma kasancewar Nusrah jininsa duk ya sashi jin kunyar abunda ya aikata a bayan not a little,ya ji haushin kansa and regretted about it all because of what the evil heart and the devil made him do,but what would he do? Mene ne zai yi su yafe masa? Though ya so Nusrah a bayan,abunda yayi mata wancan ranar dai² da second d'aya bai tab'a jin haushin kansa ba sai yanzun da ya tabbatar ta yi masa nisan da kafin ya tarar da ita zai d'auke shi tsayin zamanai,nisan su yanzun tamkar ma sama ne da k'asa,abun ba zai misaltu ba ma,here ya gano masu iya magana da suke cewa  "bar raina allura,domin kuwa itama k'arfe ce" and idan har ka san farkon ka u certainly do not know ur end,yau baka yi wulak'anci bama ya ka k'are bare ka yi? Shi dai yau ga shi ya wulak'anta y'ar uwarsa ta jini,ya fad'a mata maganar da ko wani bare ba zai so a gayama ba,and kuma ya dawo yana jin haushin kansa,shin ma duk me ya kaishi ne? Sanadiyyar bin ra'ayin zuciya kawai ta kaishi ta baro,yana zamansa lafiya ya je ya janyo ma kansa b'acin suna,duk suna yi masa kallon wani mutumin banza,and halinsa detriment of all his dignity and worth.

     Har ya shigo compound d'in gidansun yayi parking tunani kad'ai yake yi da maganganun zuci,ya d'auke shi tsayin lokaci zaune cikin motarsa without knowing of what to do,Mommy da suke fitowa za su fita unguwa tare da su Afaf,ta kalli motarsa da ta fahimci a kunne yake,tana kallon Hannah fuskarta da mamaki tace "ke! Who's in the car there?" Hannah ta kalli motar ta tab'e baki tace "Mommy Yaah Aatif mana,who will get in if not him?" Mommy ta sake bin motar da kallo kafin ta fara tafiya,tana zuwa tayi knocking,a hankali cike da mutuwar jiki bayan ya dawo tunaninsa ya sauke glasses d'in,ganin Mummy'nsa ce ya lumshe his red eyes with signs of distress,Mommy ta bisa da kallon tsanaki kafin ta yi magana ya fara k'ok'arin bud'e motar ya fito,ta matsa a little bit ya sakko,tana ci gaba da kallonsa har sannan tace "lafiyarka k'alau kuwa Aatif?" Yayi shiru kamar ba zai ce komai ba,sai can ya d'an k'irk'iro murmushi yace "I'm fine mom" ta girgiza kai tace "u know i won't agree,say something different than that" saurin kallonta yayi yana lumshe ido ya rik'o hannunta a little and adjusted his stance,Mommy duk ta zuba masa ido tana kallonsa jira take taji me zai fad'a,yayi shiru yana tunanin yadda zai iya fad'a mata,a hankali Mommy ta shafa kansa fuskarta d'auke da wani expression wanda a fuskar mahaifiya kad'ai ake ganinsa idan taga yaranta a damuwa tace "ko dai muje ciki muyi maganar ko kuma idan mun dawo?" Ajiyar zuciya ya sauke ya kad'a kai a hankali da fad'in "Idan kun dawo d'in" Mommy tace "alright! Maza je ka kwanta ka huta" d'an murmushin yak'e ya k'irk'ira and gave her a side hug then ya fara tafiya,Mommy ta bishi da kallon tausayi har ya shige cikin gidan ya barsu tsaye a compound,bata iya motsawa a gurin ba sai da Hannah ta matso ta rik'o hannunta,da sauri ta sauke ajiyar zuciya tace "muje kou" Hannah ta kalli Mommy tace "but Mommy kamar Yah Aatif yana cikin damuwa fa,ko za ki fasa zuwa sai mu tafi mu?" Murmushi tayi tace "No! Let's just go,he said we'll talk when we get back" a hankali Hannah ta kad'a kai tace "tou mu tafi."

     Da daren ranar bayan sun dawo suna zaune Mommy ta kalli Aatif who's lying on the rug ya tada kansa da hannu yana kallon ceiling,tayi shiru tana kallon how deep he was cikin duniyar tunani tayi calling sunansa out "Aatif!" A hankali yayi blinking madaidaitan idanunsa and letting out a sigh of relief,Mommy dake kallonsa tace "wai ba da Aatif nake magana ba,kayi min shiru?" Kansa ya d'an juya yana tsuke baki yace "I'm sorry Mom" siririn tsaki tayi tace "za ka tashi ka min bayanin abunda yake saka damuwa kwanakin nan ko kuwa?" Fad'uwa yaji gabansa yayi a hankali ya mayar da idanunsa ya lumshe yana sauke numfashi,yadda yayi shiru ya rufe idanu angrily Mommy tayi k'wafa da fad'in "u are very stupid,ina magana ka kulle min ido,ni sa'ar kace ko meye ne wannan sabon iskancin kuma?" Saurin tashi yayi ya zauna zai yi magana Mommy taci gaba da fad'a "irin wannan abubuwan da kake yi su suke sawa Daddy yake ganin kamar ni nake cewa kayi,kana d'aukan alhakina da yawa fa Aatif,but ban sani ba ko soyayyar da nake nuna maka yasa kake min haka ko kuma abokiyar wasanka ka mayar da ni,ka shiga hankalinka da ni ina fad'a maka,otherwise kuma za'a ji kanmu da kai a gidan nan" tunda ta fara fad'a ya sunkuyar da kai,bai yarda ya d'ago ba sai da yaji ta yi shiru sannan ya d'ago a hankali cikin cool voice yace "I'm sorry Mom,ni ba wani abu yake damuna ba,i'm just trying naga cousin sis da Noor sun daina fushin da suke yi,i know i didn't give a damn about what had happened,wannan shi ne kawai damuwa na,after that babu komai and i'm not hiding anything from u" wani kallo Mommy tayi masa mai cike da tsantsar tausayi,kafin tayi magana aka bud'e entrance aka shigo,duka suka waiwaya suka kalli Daddy dake shigowa fuskarsa d'auke da wani irin murmushi suka yi masa barka da dawowa,ya amsa yana zaunawa next to Mommy dake saman armchair,no one expected yaji maganar da suke yi sai da yayi murmushi ya kira Aatif "Aatif" da sauri Aatif ya sauke kansa k'asa yace "Na'am Daddy" Daddy yace "sure yanzun na yarda hankali ya shiga cikin kanka,tunda har kake realizing u have made a mistake,but abunda zan fad'a maka shi ne ka samu time kaje ku zauna da su sai ka basu hak'uri,ina tunanin idan ka yi haka za su fi d'aukan lamarin da muhimmanci" nasiha sosai Daddy yayi masa and gave him more explanation of how to apologize,yayi wa Daddy godiya then ya tashi ya wuce bedroom d'insa,da ya shigo zama ya fara yi bakin bed yayi shiru remembering of their relationship with Nusrah har yadda suka rabu,lokaci d'aya wasu irin hawaye suka kawo idanunsa because he never thought that after their separation zai shiga damuwa,sai daga bayan lokacin yana Amsterdam wani irin soyayyarta yayi ta d'awainiya da ruhinsa by then lokacin da ya shirya yiwa Mummy'nsa bayanin komai har ya gama tsara yadda zai nemi Nusrah su dai²ta kwatsam sai ya samu labarin aurensu da Nuraz,a hankali ya koma ya kwantar da bayansa saman bed d'in while k'afafunsa suna k'asa,ya d'auki tsayin lokaci a hakan kafin da kyar cikin wani irin muryar damuwa ya furta "Yah rabbi kasa zab'in da kayi min a yanzun shi ne mafi alkhairi a tare da ni,ya Allah ka basu zaman lafiya su kuma,ka raya abunda ka azurta su da samunsa" yana kwance almost an hour shiru yana tunani,da yaga damuwa yana neman yayi affecting kwakwalwarsa da wuri ya tashi ya d'auka phone d'insa dake gefensa ya fara kiran line Deeja,suka yi hira sama² but basu wani jima ba suka ajiye because he's not in a good mood,but duk da hakan ya ji dad'i and ko babu komai damuwar dake mak'ale a ransa ta ragu.

*****
Chapter 145 · 0% Book details