← Book details Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 130 OF 152

Sashe 130

Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

       Yace "Sharad'in aikinki shi ne duk abunda muka yi idan bai yi tasiri akan su ba zai dawo gareki!" Idanun Hajiya Karima's were closed and she saw nothing except d'aukar fansa,ba tare da tunani ba tace ta ji ta amince,sun yi hakan da shi ya fi a lissafa tace ita dai ta amince,Boka yace "d'aga hannunki na hagu sama!" Tayi kamar yadda yace,sai ga abu kamar tandun kwalli na k'arfe da wasu irin layu da aka rufe da jar fata,a tsorace ta d'aga kai tana dubawa,taga babu kowa a kusa da ita,lamarin ya girgiza su sosai har ita Hajiya Mariya,Boka yayi dariya kafin ya d'ora mata bayani "lallai ki tabbatar kin adana wad'annan kayan,idan kin yi wasa da su shaid'anu za su dawo mana da su,ranar da za kije can gidan,za ki tafi da su duka,shi kwallin idan kika je shiga za ki saka a idonki na hagu kad'ai,kina shiga ki kira sunanta sau uku amma ba yadda za ta ji ba,dakarun shaid'anu da za mu wakilta suyi aiki,za su k'arasa sauran aikin,yayin da za musa taji kamar ana kiranta,a wannan lokacin ki tabbatar kina cikin gidan,da zaran ta ji za ta waiwayo,amfanin kasancewarki cikin gidan shi ne tana ganinki za ta rasa nutsuwarta,za tayi tunanin ke kika kirata,za ta amsa kiran,da zaran ta amsa,shi kenan buk'atar ki ta biya,sai ki binne layun a cikin gidan ki fito,aikinki ya kammala sai jiran sakamako!" Hajiya Mariya dake gefe ta washe baki "Wannan ai duk babu mai wahala a ciki,ko ni zan iya aiwatarwa indai shi kenan abunda za ayin" Boka dai bai sake cewa komai ba bayan nan ya salleamrsu da fad'in "za ku iya tafiya sai dai daga nan zuwa kwanaki biyu ina jiran zuwanku,shi kuma sakamakon aiki sai nan da wata guda!" suka amsashi sannan suka kama hanyar tafiya,har suka baro cikin surk'uk'in dajin babu wacce ta sake magana. Tafiyar awanni biyu da mintuna ta dawo da su cikin gari,tun da suka dawo Hajiya Mariya take zuga Hajiya Karima kan lallai kada tayi sanya,ta hanzarta a gobe taje ta aiwatar da aikin zuwa jibin su koma,Hajiya Karima tayi na'am da batun Gwaggonta,bcus ita kanta ta damu gari ya waye taje ta gabatar da aikinta kamar yadda bokan yace.

     At about 11:05am Hajiya Karima sun gama shiryawa,Hajiya Mariya tana kallonta fuskarta d'auke da makirin murmushi take yi mata kirari,literally duk mai hankali yaji ana yi masa irin wannan kirarin he most knows there's no love cikin yabon da ake yi masan,tare suka fito bayan sun yiwa Hajiya Amina sallama suka wuce gidan Abban,11:40am a bakin get d'in gidan yayi musu,tun daga nan suka fara rigima da get man saboda ya sanar da su Abbah ba ya k'asar,Hajiya Mariya ta d'age kai tace "da waye yace maka wajensa muka zo? Idan za ka bud'e get ka bud'e mu wuce,ina ce aikinka kenan gadi?" Da suka takura sai sun shiga tunda yaji suna cewa they would call Abbah and tell him ya hanasu shiga,sai bai yi tunanin komai ba ya bud'e musu get suka shige suna zaginsa uwa da uba,shi dai bai sake kula su ba har suka yi nisa da get.

        Suna tsayawa a varenda dai² bakin entrance,Hajiya Mariya ta waiwaya taga babu kowa tayi ma Hajiya Karima alama,da sauri suna waiwaye irin na mutumin da ba shi da gaskiya ta d'auko kwallin tasa then ta mayar jaka suka yi knocking,suna jin tafiya kafin azo bud'ewa Hajiya Karima ta kira sunan Annie as their witch says and ta gani jikin Invitation card,suna jin takun takalmi a kusa sosai suka kalli juna,they smile together and gazing into the parlor lokacin da ake bud'e k'ofar,idanu hud'u suka yi da Binitta,ran Hajiya Mariya ya d'an sosu,but ta yi k'ok'ari ta danne tana kallon Binitta tace "To azagwai har yanzun ashe ana nan? Ba mu hanya mu wuce ko?!" Binitta tayi murmushi tana kallonsu duka bata tanka maganar Hajiya Mariya na farko ba tace "Aunty sannu de zuwa" Hajiya Karima bata ce komai ba sai d'aure fuskar da ta sake yi,Binitta ta basu hanya suka wuce and walked up behind them,suka zauna cikin parlor d'in sai kallon yadda aka sake gyara gidan suke yi,suna jinjina uban dukiyar dake cikinsa,suka wani tab'e baki a tare had'e da yin tsaki,Binitta bata tsaya ba taje ta kawo musu drink da snacks,ta ajiye musu sai murmushi take yi da gani ka san tana cikin farin ciki yanzun,Hajiya Mariya ta kalleta tana yatsina fuska tace "Ina masu gidan?" Binitta tayi y'ar dariyar da ta bayyana hak'oranta tana nuna musu entrance,suka waiwaya a tare because they all thought su d'in ne a wajen,sai da suka ga wayam suka yi tsaki,cikin hayaniya Hajiya Mariya ta waiwayo kan Binitta "What kind of stupidity is this? Ana tambayarki kin mayar da mutane sa'annin ki?" Binitta bata ji haushi ba ta sake yin murmushi tace "Ai Hajiya baya k'asar,sun yi tafi da boss!" A tare suka zaro ido suna tambaya "Ehhh!?" Ta kad'a musu kai tace "Tunda akayi musu aure sunka yi tafi har yanzun basu dewo ba" a rud'e Hajiya Mariya ta kalli Hajiya Karima,saboda rud'ani da tashin hankali Hajiya Karima doesn't know when ta d'ora hannu akai tana fad'in "Na shiga uku!" Hajiya Mariya ta yi shiru duk ta rasa abunda za tace sai kallon yadda Hajiya Karima tayi take,da sauri tayi mata alama da ido,ta had'iye saliva's da kyar,k'ok'arinta ta saita nutsuwarta a gaban Binitta but abu ya fi k'arfin ta,sai wani irin abu take yi ita ba wacce ta samu matsalar kwakwalwa ba ita ba mai lafiya ba,haka suka tashi jiki babu k'wari ko sallama nasu yiwa Binitta ba,instead of da suka fito su hak'urewa k'arasa aikin,here Hajiya Karima ta dage lallai sai su binne layun,Hajiya Mariya tace a'a su yi waya su tambayi bokan,Hajiya Karima ta kafe lallai sai anyi saboda haka Boka yace su yi,ganin yadda take wasu irin attitude ba cikin nutsuwarta ba dole Hajiya Mariya barinta tayi yadda take so,tana gamawa suka fita daga gidan,but hankalin Hajiya Mariya ya kasa kwanciya saboda abunda take ganin Hajiya Karima na yi like she had a problem,da suka koma gida taji ta kasa nutsuwa so she calls the witch over the phone take sanar da shi what is about to happen,here ya bud'e musu wutar masifa akan me yasa suka binne layun? Da suka je basa nan da sun kira sun fad'a masa kafin su aikata hakan ai,Hajiya Mariya tace "Yanzun yaya za ayi?" Yace "Yanzun kam sai abunda kuka gani,tun farko na sanar da ku sharad'in aikin,kuka ce kun amince,so yanzun babu abunda zan iya yi muku" hankalin Hajiya Mariya ya tashi tayi shiru tana kallon Hajiya Karima tace to "uban shaid'anu yanzun kai babu abunda za ka iya yi mana ne na taimako?" Yace "babu! Sai dai ku jira sakamakon abunda zai faru nan da zuwan kwanaki talatin" Hajiya Mariya tace "me zai faru boka?" Strictly yace "duk abunda ya faru tsayin lokaci da duk wasu mugun k'ullin da kuka yi da hannunku,za ta tona muku asiri.." Bai k'arasa ba Hajiya Mariya ta kurma ihu tana fad'in "mun shiga uku,uban shaid'anu ka taimake mu,wollahi idan asirin mu ya tonu mun bushe" wata mahaukaciyar dariya ya fashe da shi har sai da Hajiya Mariya taji haushinsa,a fusace tace "dole mu bar garin nan,mu gudu kawai mu nemi wani wajen mu k'arasa rayuwarmu zai fiye mana sauk'i" Boka ya sake shek'ewa da dariya yace "hakan ba mai yiwuwa bane,saboda duk inda kuke wata rana dole asirin nan da kuke b'oyewa zai bayyana,dole wanda aka yiwa su sani,sai dai kuma idan mutuwa.." Bai k'arasa ba Hajiya Mariya ta zabgaga masa uban ashar ta kashe wayar had'e da jifa da ita,ta daki bango ta tarwatse.
     (A raina nace kin huta,da kin rik'e kya raka sauran rayuwarki da ita)

     Since that day incidence d'in ya faru kullum sai Karima ta fito da wasu sabbin attitude,abun nata tun baiyi k'arfi ba har al'amarin tan ya fara bawa Hajiya Mariya tsoro ta d'auke mata wuta ta daina shiga al'amuranta,da al'amarin tan yaci gaba da lalacewa ta fara surutai marasa kan gado,abun yana damun Hajiya Mariya sai take rufe ta a d'akin,duk neman da Hajiya Amina mak'ociyar su ke zuwa yi sai Hajiya Mariya tace bata garin ta yi tafiya,a hakan kwanaki suka fara juyawa zuwa sati abu kamar wasa har aka fara neman shafe kwanaki 20. The days are long gone,yayin da zuwa wannan lokacin komai ya gama k'azanta,al'amarin Hajiya Karima sam ba'a cewa komai,a ranar da ta cika kwanaki talatin cif kamar yadda Bokan ya fad'a sai ta tashi da wani irin special attitude that has never appears since incidence d'in ya faru,Hajiya Mariya ta fito za taje d'akinta sai taji tana iface² da kiran sunan Abbah tana shek'a dariya,abun nata dai sak hauka,agurguje Hajiya Mariya ta k'arasa shiga tana kiranta,abunda ya bata mamaki sai taga Kariman tana yi mata wani irin firgitaccen kallo,da gudu kuma ta nufo inda take tana fad'in "Sai na kashe ku,duk wanda yace zai raba ni da miji na sai na kashesa" tana maganar tana yowa kanta bakinta har wani irin kunfa yake like ta sha liquid soap,Hajiya Mariya taga babu sarki sai Allah ta fita daga d'akin but sai ta manta bata rufe k'ofar ba,Hajiya Karima tana ganin k'ofa a bud'e itama ta fito ta kama hanyar fita daga parlor dake a bud'e,Hajiya Mariya tana hangen lokacin da ta fito,da gudu² ta biyo bayanta tana fad'in "na shiga uku,shi kenan za ta fita ta tona mana asiri" a gaggauce ta biyo bayan Karima d'in da tayi nisa da tafiya tana yi tana surutai wanda duk wanda ya ganta zai fahimci ba lafiyarta k'alau ba.
Chapter 130 · 0% Book details