← Book details Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 152

Sashe 44

Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

    Bayan sun fito daga lectures suna tare da Veronica Jackson,Maria Robles sai Sarah Alee da yake ita y'ar 9ja ce karatu ya kaita suke gaisawa sosai har mutunci ya had'a su suke fita tare,a wajenta ta san su Maria da Veronica kasancewar apartment d'aya suke zaune,suna tafiya za su cafeteria kiran Aatif ya shigo wayarta,ta d'an tsaya kad'an ta fito da wayar tayi answering,sallama tayi masa ya amsa yana fad'in "Ina gimbiyata za taje ne take tafiyar k'afa.!?" Tayi murmushi tace "Ba dai ka ganmu ba.!?" Yayi murmushi yace "A'ah ban ganku ba amma dai na gano ki ke d'aya" tayi murmushi tace "Ba ni kad'ai bace ai" yayi murmushi cike da zolaya yace "Idanuna ni kuma ke kad'ai suka nuna min" tayi murmushi bata ce komai ba,yace "Ina za kuje ne.!?" Tayi ajiyar zuciya tace "cafeteria" yace "Okay.! Bari mu tafi tare" tayi saurin katse shi tace "A'a mu had'u a can" yayi shiru kamar bai son hakan sai kuma yace "Ok.!",basu jima sosai da shiga cafeteria ba suka sa akawo musu drink da snacks,tana zaune tayi facing inda duk mai shigowa za ta gansa,ta hango shi yana shigo wajen,sanye yake da white trouser da white shirt mai V-neck,idanunsa a cikin sunglasses mai duhu,tunda ya shigo ta kalle shi haka nan taji gabanta ya fad'i,ta lumshe ido a hankali ta bud'e taci gaba da kallonsa har ya zauna d'an nesa da su kad'an,k'arshen had'uwa,kyau da tsari Aatif yana da su kuma ya kai namijin da ko wace mace za tayi fatan samunsa,tsarin rayuwarsa da komai nasa cikin nutsuwa yake yinsa and dai² iyawarsa yana bawa duk wanda suke tare girma da muhimmanci,fari ne shi sosai dan ya fi Nuraz haske,kana kallonsa zaka gane yana tattare da duk wani nau'in hutu da jin dad'i,sai dai fa idan ana batun kyau dole ne a fara ambaton Nuraz kafin ace shi,asalin mahaifinsa D'an Nigeria ne daya fito daga jihar Gombe,k'aramar hukumar Akko,cikin garin *KUMO* haka ma Mamansa itama y'ar Gombe ce amma ita ainihinta a *JEKA DA FARI* ta taso,,kiranta yayi duk da ya ganta bata d'auka ba ta nemi excuse wajen su Sarah ta nufi inda yake,tun kafin ta k'araso ya zare glasses d'in idonsa yana sakar mata murmushi,ta sake yi masa sallama ya amsa,ta zauna tana gaishe shi,cikin sakin fuska ya amsa mata yana tambayarta lectures,shiru suka yi na wani lokaci kafin yasa a kawo musu drinks,ta kalleshi tace "Bana shan komai fa",ya kalleta zai yi magana tace "Ai mun sha tare da su Sarah" ya tab'e baki kad'an bai kulata ba yasa waiter ya kawo,ya tafi kawowa tayi shiru tana tunani,ya d'an buga table d'in kad'an,tayi saurin kallonsa yace "Yaya ne.!?" Ta girgiza masa kai tace "Nothing" yace "Allah ya sa" tayi saurin kallonsa saboda kalmar daya fad'a sai taji kamar Nuraz ne a gurin,tayi shiru ta sunkuyar da kai ya katse mata tunani "Ehmn.! Wane labari ne kike son fad'a min.!?" Ta d'ago da sauri tana had'iyan wasu irin terrified saliva's,a hankali tayi blinking idanunta tace "My story" ya gyara zama yana murmushi yace "Wawhh.!" Tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya yace "Kin yi shiru,and u know am eager naji" ta d'anyi calming kanta sannan a hankali ta fara fad'a masa,tunda ta fara yake kallonta da wani irin yanayin tausayinta a idanunsa har ta gama,fuskarta da hawaye sosai ta d'ago idanunta for da first time tunda ta fara magana ta kalleshi,yadda ya zuba mata idanunsa ko k'iftawa babu yasa taji duk guiwoyinta sunyi sanyi,a hankali cikin mutuwar jiki ya ciro handkey ya mik'a mata,ta karb'a a hankali ta goge fuskarta,ta mayar masa ya karb'a yasa a aljihu,kusan mintuna biyar taji bai ce komai ba,ta kalleshi yayi shiru da alamun tunani yake fuska da damuwa,kamar za tayi magana Sarah ta k'araso ta musu sallama,Nusrah ta kalleta tana k'irk'iro murmushi,suka gaisa da Aatif ta kalli Nusrah tace "Baby we will go home" Nusrah tace "Ku jira mu wuce tare sai ku sauke ni a hanya" Sarah za ta amsa Aatif yace su tafi zai kaita gida da kansa,tayi saurin kallonsa za tayi magana taga bai kalleta ba,suka yi sallama da Sarah,tana zaune su Maria suka zo wucewa,suka yi waving d'in juna tana kallo suka fita daga cafeteria,a hankali tayi ajiyar zuciya,bayan tafiyarsu babu jimawa Aatif ya mik'e yace "Muje na kaiki gida" ta tashi bata ce komai ba har suka fito inda yayi parking,ya bud'e mata front seat ta shiga,ya rufe ya koma side d'in driver ya shiga,sai daya fara sa seatbelt sannan ya tada motar suka fara tafiya a hankali har suka fita daga skul d'in,a bakin apartment d'insu ya tsaya,da wani irin murya ya rarrasheta,after ya nuna mata shi ita yake so ba komai ba,suka yi sallama yace idan ya isa gida za suyi waya,ta masa fatan komawa lafiya,a hankali ya d'age glasses yayi reverse tana d'aga masa hannu,har ya kusa fita daga arean sannan ta juya zata shiga gida,ta fara tafiya ta hango motar Nuraz tana shigowa line bata tsaya ba ta shige ciki.

      Tun da ta dawo ta shige d'aki tayi zamanta a can tana jiran kiransa,har after maghreb bata sake fitowa ba,sai da Lolly tayi kiranta jin shirun ya yi yawa,ta fito rik'e da wayarta ta zauna kusa da ita,Lolly ta kalleta tace "Ke kam baby kina jin dad'in zama kiyi shiru,shi kenan shi mutum sai yayi ta zama cikin d'aki shi kad'ai" tayi murmushi bata ce komai ba,wayarta ta duba taga ko Aatif ya kirata,taga babu alamun miss call akai,ta bud'e network ta fad'a duniyar gizo²,nan ma ta duba babu sak'onsa,tayi shiru tana tunani,har to 11 tana zaune shiru duk bayan mintuna ta sake dubawa ko ya kira sai taga bai kira ba,zuciyarta ta damu sosai,Nuraz ya saci kallonta ya ganta a damuwa,yayi shiru yana tunanin yadda zai tambayeta ko ta samu sun yi maganar da shi.!?,idea ya zo masa ya d'ago yana niyyar tambayarta ta mik'e tana k'irk'iro hamman k'arya tace "Aunty good night" ta kalleta tace "Toh.! Angel sai da safe" ta kalli Annie tace "Annie sai kin shigo." Ta gyad'a mata kai tana lumshe ido,ta yiwa Bareerah sallama ta wuce,har ta tafi idanunsa suna kanta,ya rasa me zaice da zaisa ya bar wajen ba tare da su Annie sun gano shi ba,zuwa wani lokaci ya mik'e shima yayi musu sallama,ya wuce bedroom d'insa.....

#Share pls.
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©®2020.*

*'DAN MACE..*
(Tʜᴇ ᴘꜱʏᴄʜɪᴀᴛʀɪꜱᴛ)..💥

*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
https://my.w.tt/29u2S26SG2

Pᴀɢᴇ 22.
#Pʟᴀɴ ᴛᴏ ɢᴏᴛ sᴇᴄʀᴇᴛ ᴍᴀʀʀɪᴀɢᴇ

Da ya shiga kasa zama yayi yana ta tunanin yadda zai samu suyi magana da ita a daren kafin safiya amma ya rasa,ga shi ba number ta gare shi ba bare ya kira ta,ya zauna shiru a gefen bed yana tunanin idan basu yi magana yanzun ba sai dai da safe kenan,wata dabaran ya zo masa ya bud'e network d'in wayansa da tunanin yayi search a IG,Twitter zuwa sauran chart ko zai ganta sai ya tambayeta yaji idan ya yi sa'a tana online,yayi saurin d'aukan wayar ya fara dubawa,duk sunan da yake tunani idan yayi search zai samu sai da yayi amma ya rasa ta har Angel da Lolly ke kiranta ya sa bai ganta ba,ya hak'ura cike da damuwa ya ajiye wayar,wata zuciyar tace "To ka fita ta balcony mana idan ba ka so kowa ya sani" yayi shiru yana tunani,can da yaga hakan kamar shi ne mafita ya tashi da sauri,yaje jikin bright glass curtain wall d'in ya bud'e k'ofar da take sada shi da balcony ya fita,dai² window bedroom d'in ya tsaya yana tunanin yayi magana ko a'a.? Ya jima yana tunani ya rasa yadda zaiyi ya koma bakin pool ya zauna saman d'aya a cikin kujerun wajen,shiru yayi ya d'ora chin d'insa a saman hannunsa daya had'e guri d'aya yana tunani,ya juya kad'an ya kallo center window d'in sun,wayansa daya fito da shi ya duba yaga lokaci ya tafi sosai 12 saura mintuna,duka arean ya yi wani irin shiru baka jin hayaniyar komai,ya d'aga kai looking to the sky kamar yana counting Star's,da yaga yana b'ata lokaci ya mik'e a hankali ya koma bedroom ya rufe k'ofan,daren ranar da kyar ya samu yayi bacci.
Da safe ya tashi a d'an makare,ya fito da niyyar dubata,ya tarar tuni har ta tafi skul,ya koma ya gama shirin fita yayi sallama da su Annie,bayan ya baro gida yana tafiya still yau d'inma ya ga motan jiya tana following d'insa,ta mirror ya ci gaba da kallon motar yana tunanin mene ne had'insu da shi da suke bibiyar sa.!? Yayi deciding ya tsaya,gefen street d'in yayi parking yana kallon motar ya ga ta tsaya a d'an nesa da inda yake ya bud'e mota ya fita,inda motar take ya nufa ya tsaya dai² side d'in driver yayi knocking,a hankali aka sauke glasses d'in,Clark dake ciki ya kalleshi bai yi magana ba yana jiran yaji me Nuraz d'in zai fad'a,cikin matuk'ar had'e rai yana kallon baturen da fuskar tuhuma yace "why are u following me.!? Do i have any relations with u.!?" Clark ya tab'e baki kad'an cikin harshensa yace "why should i go after u.!?" Nuraz ya d'age shoulders yace "I don't know,but this is what i want to know.. Do we have any relationship that u always followed for.!?" Clark yayi ajiyar zuciya ya fara d'age glasses d'in saboda bai san me zai ce ba,da sauri Nuraz yasa hannu ya rik'e yana kallonsa angrily "Since u can't say anything,stop following me,if u were sent ne kaje ka fad'awa wanda ya aiko ka na fi k'arfinsa,nafi k'arfin yayi min wani abu,,idan baka ji ba ka sake bina kuma..!" Soundly yayi making snap,without ya sake cewa komai ya girgiza kai ya wuce,as he walked across the place a d'an fusace k'asar wajen tana motsi ya bawa Clark tsoro,quickly yayi swallowing some of the terrified saliva's da suka mak'ale a bakinsa,waya ya fara k'ok'arin yiwa uban gidansan,from the other side Rafeek ya d'auka,Clark yace "Sir. The boy realized we were following him" Rafeek ya lumshe ido ya bud'e yana sakin numfashi da kyar yace "Just come back home",daga haka bai sake cewa komai ba ya ajiye wayar yana sakin ajiyar zuciya while a fili yana maimaita fad'in "Astagfirullah wa'atubu ilaiik"
Chapter 44 · 0% Book details