← Book details Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 137 OF 152

Sashe 137

Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

They didn't take long time suka sake shiryawa suka fito,wani motar daban suka d'auka suna tafiya cikin mota sai hira suke kamar ba su ne wad'annan miskilan ba da abaya magana take musu wahala,yana driven almost half of her body was in his body,yana kallon hanyan da ya kasance babu wasu abun hawa sosai yace "Roohii!" Ta d'ago fuskarta kad'an tana kallon gefen fuskarsa,da tayi haka yasan tana jinsa sai yace "mene shawaranki?" Tace "on what?" Yace "me kike ganin ya dace mu siya for baby's and Annie?" Tayi shiru tana tunani a hankali tace "duk abunda ya dace a siya kawai" ya b'ata rai yace "what have i asked u?" Tace "mene ne shawara na kace" ya kad'a kai yace "ke kuma me kika yi?" Dariya tayi tana pecking cheek d'insa tace "ni dai Allah ban san me zan fad'a ba,kawai sai munje za mu zab'a abunda ya dace ko?" Shiru yayi sai kuma yace "Ok! Hakan yayi" har sun yi nisa da gida Nusrah tace "ba muyi waya mun tambaya ba fa ko sun koma gida" murmushi yayi yace "no suna hospital,baza su discharged nasu yau ba",suna shigowa ward da Annie take,suka tarar bak'in da suka zo basu tafi ba har lokacin,da sauri ya rik'o hannunta yana tsuke fuska,tana yin magana sai taji yace "Um'um" ta kalli yadda fuskarsa ta koma ita dai kamar za ta fashe da dariya,ta daure dai tana ta b'oyewa,sam basu kula da Mr Rafeek a wajen ba sai da suka kusa k'arasowa,kasancewar ba ya k'asar ya je taro Egypt da suka yi waya Abbah ya sanar da shi haihuwar shi ne fa ya taho,Nuraz ya bud'e ido sosai yana kallonsa sai kuma ya saki fuska yana murmusawa yace "Hi Dad!" Yana d'aga masa hannu,Rafeek looked at them with a smile yace "hello beta" to them as well,suna zuwa Nuraz ya rungume shi yace "welcome back Dad ya hanya?" Rafeek yace "Alhamdulillah" Nuraz da wani shegen shagwab'ar sa tun na yarinta da yake ma Annie ya d'an ja jikinsa kad'an yace "i just forgot fushi muke yi da kai ma Daddy tunda bamu san za ka dawo ba" Rafeek ya biyewa d'ansa yana shafa kansa yace "really apologize beta kaina bisa wuyana,but it's not my fault ku yi blaming Abban ku" ya k'arasa maganar da nuna Abbah,Nuraz ya zaro ido kamar ya ji tsoro yace "A'a ba sai mun ce komai ba tunda Abbah ne mun hak'ura ko Roohii?" Ya k'arasa maganar da yiwa Nusrah tambaya,ta kuwa d'aga masa kai tace "Ehhh mana" babu wanda alak'ar sun bata burge ba cikin y'an uwan su Annie,it was there Nusrah tayi k'asa da kai to greet her father-in-law and welcomed him,ya amsa fuskarsa a sake sai sa musu albarka yake yi,a nan Baba ya nunawa Nuraz danginsa na b'angaren Lolly and introduces him to them,haka Nusrah ma matsayin matarsa,they were all surprised wai Lolly tana da saurayin d'a kamarsa Annie kuma sai yanzun ta haihu,even though sun samu labarin abunda ya faru a bayan but basu yi tsammani ba,bayan an gama nuna masa y'an uwa sai ya d'an sake,da mazan suke maganar neman masauki ma Hajiya ce tace "wane masaukin sai dai idan ba ba duniyar kou?" they stayed in the hospital har dare,lokacin sun fito za su tafi kuma suka ga motoci manya na alfarma da securities,they were not surprise dan tun a karon farko da suka ga Rafeek suka ganeshi saboda yawan maganarsa da jin sunansa a news,so duk basu gama tsinkewa da al'amarin ba ma sai da suka shigo mansion,nan Guy's suka fara raina kansu Hajiya tace ai sai su tafi apartment d'inta duka,suma su Lolly sun had'a kai ita da mijinta suna sai dai a raba tsakanin su da Hajiya,Nusrah was on the sidelines suna kallon drama,da suka ga abun ba mai k'arewa bane Nuraz ya rik'e mata hannun yace "Let's go inside Roohii,idan sun gama duk za su hak'ura" yana fad'a suka yi sallama da y'an uwa suka wuce apartment d'insu,a hankali Junayd yayi murmushi yana taba Kazim yace "I wish i could find a woman like this babe" Abdoul dake gefe yana jinsu because shi dama ahlus'sunnah ne yace "babu dai kyau kallon matar wani" Kazim yayi murmushi yace "wollahi broah ko ni ma ban yi tunanin tana da aure ba da farkon har na ji na fara wani tunani a raina" Junayd yayi murmushi yace "dole ne ai ko wane ne ya ganta yaji bak'on yanayi" shi dai Abdoul yana ji yace "tou sai kuyi musu fatan alkhairi,and mu kuma Allah ya zab'a mana wasu" Kazim yace "ameen brother."

Sai da Annie tayi spending five days a hospital sannan aka sallame su,alhamdulillah jikinta ko da yaushe sai kyau yake yi,tana sake warkewa baby's suna samun kulawa,ranar da aka sallamesu da yake da safe ne,y'an uwa suka yi musu rakiya zuwa gida,Nusrah kam ita dama Nuraz cewa yayi ba sai sun je ba tunda sallama ne kawai zuwa dare sai suje,bcus kullum suna hospital d'in tunda aka yi haihuwar even though ta so ta je ayi rakiyar da ita,sai da ya bari ta gama fushin da yamma suka fita siyayya,wani babban mall ya kai su a can suka yi ta jidar kaya duk abunda za su siya na mazan iri d'aya suke d'auka,ita kuma baby girl sai a d'auko mata na mata wanda colour d'in yayi dai² da na brothers d'inta,Nusrah duk ta fi zak'ewa wajen zab'en kayan baby girl,suna gama siyayyar an musu packaging kayan a manyan bags aka fitar musu da su,aka sa musu kayan a back seat then suka d'auki hanyar gidan Annie,lokacin su Hannah da Afaf sun zo gidan sai tambayar Nusran suke yi sai gasu suna shigowa da manyan bags hannu biyu²,Annie da kowa da yake gidan sunyi mamakin kayan da suka jido,ita kam ma har fad'a tayi musu,Nuraz ya jingina da ita kamar yaro ya shagwab'e yace "Annie! Idan bamu yi miki ba a duniyar nan waye za mu yiwa?" Before yayi adding wani phrase quickly tace "tou Allah ya muku albarka ya raya min ku,but what u do not understand is that kayan ne sunyi yawa" su dai sun riga sunyi haka suka nuna mata babu komai sai a bayar da wasu. Kwanaki suna ta tafiya,ranar suna da yake ba wani taro za ayi ba duka dai family ne kad'ai but they plan to have a dinner at the mansio,ranar suna da yamma Malam suka yi waya da Abbah yace anyi rad'in suna,suna gama magana Abbah ya fad'i sunan yaransu but right away Annie had recently known tare ma suka yi shawara,ita macen ansa mata KHADIJAH named Nusrah's dead mother za su na kiranta da (Afroze),sai Alhassan shi kuma MUHAMMAD (sunan Baba),shi kuma Alhussain (sunan Malam) USMAN nicknames d'insu (Alhassan) da (Alhussain).

On the night at the mansion suka gudanar da k'ayataccen dinner na iya family d'in,samari da y'an mata da suke nan kowa ya kame mutuncinsa kada ayi abun kunya,while a bayan fage kam tuni suke da digit d'in juna,shi Junayd shi ne yake son Kalthom y'ar wajen Maimunatu,Abdoul kuma Hannah,sai Kazim shi kam Afaf ce ta san,daga Nigeria gefen Abbah nobody came except Malam alone yazo yaga jikokinsa and to see where Mr Sajid and his family were living,Aatif ma yazo dinner d'in though he did not want to come Daddy yace dole ne yaje,abun family bai isa ya ware kansa a ciki ba,otherwise kuma sai dai ya canja wani mahaifin,haka ya zo amma abun mamaki daga Nuraz har Nusrah da take jininsa babu wanda ya kalleshi bare su nuna sun sansa,duk ya takura da zaman su kuma kamar had'in baki a gaban kowa was not ashamed to express their love to each other,while on the other hand,if Aatif tried to run away sai yaga hankalin Daddy yana kansa,dole babu yadda zai yi haka ya zauna,yana kallon yadda Nuraz da su Kazim suke fira suna dariya amma suna had'a ido da Nuraz ko akace "Aatif baka ce komai ba,ba ka magana ne?" Sai yaga fuskar Nuraz ta canja ya gimtse,sai dai kawai yayi musu murmushi ko yace "no kawai hiran nawa ne bai zo ba",Nusrah ma ana can cikin y'an mata sai hidima suke yi,da yake ita kad'ai ce take da aure amma kansu a had'e yake dukansu,lokacin da za su tafi Aatif ya fi kowa murna,suna barin gidan kuwa Daddy yace da wa Allah ya had'a ni ba Aatif ba,nan ya dunga masa fad'a,jikin Aatif ya sake yin sanyi but the other side of his mind had something da yake k'ullawa,har suka isa gida bai sake ko tari ba.
Chapter 137 · 0% Book details