← Book details Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 152

Sashe 75

Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Like a rainstorm haka parlor'n yayi shiru,with the exception of the AC noise sai ajiyar zuciyoyi shi kad'ai ne abunda ke tashi,yayin da kawunan da yawa daga cikin su ya kasance a sunkuye a k'asa sun rasa abun fad'a,all their bodies were cold,of course none of them disagreed with what Baba had said,they were certain that this was what the Lord had decreed upon them even if they did not love. After a long time of repeating the events and looking for forgiveness,Baba ya d'ago idanunsa a hankali da suke cike da hawayen farin cikin jin gudan jininsa a tare da shi ya sauke akan Nuraz,he made sure duk wannan abu da yake faruwa ba dalilin kowa bane face na sa kamar yadda ya samu labari,a hankali ya mik'a masa hannu ya kira sa,matsawa Nuraz yayi kusa da shi yana kallonsa,Baba ya dafa kansa muryarsa a raunane ya furta "Allah yayi maka albarka" lumshe ido Nuraz yayi a hankali ya bud'e yayi ajiyar zuciya,yadda yake jin zuciyarsa a yau ji yake kamar wanda aka ciro daga kurkuku,the joy in his parents eyes today erases any sadness he has been following through with the recent paintings,surely ubangiji ya isa abun godiya da ya bashi damar yin tunanin ya kamata su ziyarci gida,murmushi yayi mai sanyi had'e da amsa addu'ar Baba,briefly they spent the whole day a nan K'ofar Na'isa,cikin y'an uwansu ana ta sake tattaunawa akan rayuwar baya.

Till about eight o'clock pm sannan suka yi niyyar tafiya,bayan sun yi sallama da kaf y'an uwansu da Baba yasa aka kira wad'anda suke a cikin gari,har bakin mota haka aka yi musu rakiya kowa yana cikin farin ciki da zuwan wannan rana,while in the heart of Baba he felt as if he should not let them go,after they informed him that they would return home as soon as they had packed their belongings,suka yi sallama da kowa suka kama hanyar Sardauna crescent cike da kewar gida da y'an uwansu along with some of Rafeek's guards,since they had made their way back home babu wanda yayi magana har suka k'arasa gida sai farin ciki suke yi,suna shiga parlor Bareerah tayi musu barka da dawowa suka amsa cikin tsantsar farin cikin da ya kasa b'uya,Annie ta kalli Nuraz da yayi shigowar k'arshe tana kiransa da wani murya,a hankali ya k'araso inda take ya zauna yana sakin murmushi,Annie ta rik'o hannunsa tana murmusawa itama ta furta "Thank u *Noor"* kai ya girgiza mata yana lumshe idanunsa da bud'ewa yake fad'in "Annie mene ne abun godiya kuma.!? I did nothing fa" she smiled and said "Kai kayi komai habibiiy,all the time we were unable to remember our identity,but today a dalilin ka all the fear we have conceived a cikin shekarun da suka gabata ya yaye,shukhraan'kthiir habibiiy surely kai d'in ka kasance such an indestructible *LIGHT* wanda ba iya gida d'aya yake haskawa ba duka duniyar yake yalwatawa da haskensa" girgiza mata kai ya sake yi "Haba Annie duk abunda ya faru fa kada ki manta kece sila,da ace a wannan lokacin baki shigo rayuwarmu ba surely da mun kasance a cikin duhu,kece hasken daya tsamomu daga wannan mummunar makomar,da baki kasance tare da mu ba da komai ya jima da lalacewa,dukan mu da mun kasance tamkar marayun nan who lost their privileges.."
Hawaye ne suka taru gefen idonta tana kallonsa da murmushi a fuskarta ta rungume shi tana shafa kansa da sawa rayuwarsa albarka,Lolly dake saurarensu da jimawa bata ce komai ba,ta nemi guri kusa da shi ta zauna suka sa shi a tsakiya,rubbing his body with tears of joy in her eyes and then began to speak "Of course u are all light to me,ba ni da kamar ku a duniyata,a kullum idan ina tare da ku ina jina cikin gata,and i find myself not to worry about anything related to my life,dan Allah ina rok'on alfarma kuci gaba da kasancewa tare da ni,do not give up because if i lose u,surely i do not know what kind of life i will find myself in.'' Suddenly Annie wiped her tears in a calm voice ta fara magana "Our being together or on the contrary is all a rule of God,if he wants to keep us together no one can stop that,gata ubangiji shi yake bawa duk wanda yaso,amma ki dunga tunawa da cewa duk abunda ya samu bawa dama can is written down,both life and death are beyond his control,if he wants at the same time he will be able to hold us back or to leave us,so that whatever happens idan har daga gare shi ne dai² ne a gurinmu,bcos he made that promised,so abunda nake so mu gane shi ne duk a yanayin da muka samu kanmu ina fatan za muyi hak'uri mu karb'i jarabawarsa gare mu." Gyad'a kai suka yi su duka da fad'in "we will if God willing" Annie tace "Allah yasa" suka amsa "Ameen" Tunda suka zauna Nusrah ta yi shiru bata ce komai ba sai kallonsu kad'ai da sauraren maganganunsu da take jin kamar dan ita suke yin su,lokaci guda yadda taga suna cikin farin ciki jikinta duka ya d'auki sanyi and she is wondering about how her Father is.? Is he alive or dead.? Wani abu ya same shi bayan tafiyar ta ko a'a.? Yana lafiya ko ba shi da ita.!? Shin idan yana raye zai yarda ya karb'eta a matsayin y'arsa yanzun ko a'a.? She was overwhelmed by such questions,and at the same time felt her heart sink,with tears that she was trying to avoid her eyes began to flood,ta jima a cikin wannan halin ganin no one a cikin su da ya kula da yanayin data tsinci kanta a sanyaye ta silale ta bar musu parlor'n bcos bata so ta b'ata musu yanayin farin ciki da suke ciki.....

*Rashin lafiya ba abune mai sauk'i da bawa zai d'orawa kansa ba,hausawa na cewa lafiya ke sawa a b'uya,sai dai a wani gefen sam ba haka bane,wasu daga cikin ku sun ji ni shiru sai dai basu yi min uzuri ba though sun san bana jimawa kamar haka ban yi posting ba,and they all know that jiki da jini wata rana dole a samu matsala,but they regard it as something different,if i'm perfectly healthy how can i keep u quiet for so long? But rayuwar duniya yau dad'i ne gobe kishiyarsa,ni kaina buri na bai wuce na kammala rubuta littafin nan kafin wannan lokacin ba but Allah bai nufa ba,in sha Allah idan muka yi hak'uri duka kafin azumi cikin yardar Allah zan kammala ku k'ara hak'uri,na gode sosai masoyana da addu'o'inku rabb ya saka muku da mafificin alkhairinsa.👏*

#Share pls.
#Asli Smasher.
💠💠💠💠💠
*©®2020.*

*'DAN MACE..*
(Tʜᴇ ᴘꜱʏᴄʜɪᴀᴛʀɪꜱᴛ)..💥

*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
https://my.w.tt/29u2S26SG2

Pᴀɢᴇ 34.
#Sᴜᴘᴇʀɴᴀᴛᴜʀᴀʟ ᴄʜᴀʀᴍ

Kasancewar hiran da suke yi ya tafi akan al'amarin daya faru a yinin ranar,shi yasa har Nusrah ta bar gurin babu wanda ya sani a tsakanin su ukun,kamar ance ya juya inda take zaune yaga wayam,after he realized that Nusrah was not there,at the same time he felt his heart beat so fast,a hankali ya rufe idanunsa inwardly yake jin bai kyauta ba,silently sai ya fara addu'ar Allah yasa duk abunda zai faru ko yake faruwa da ita ya zama mai sauk'i,though Nusrah bata jima da barin parlor'n ba hakan yasa yaji shi kansa zaman gurin ya dame shi,a wayance yayi sallama da su Annie,without ya bari sun gane halin da ake ciki ya wuce bedroom d'insa.
On the side of Nusrah kuwa tana shiga bedroom d'in zaunawa tayi gefen bed,as she feels her heart heave slowly sai kuma ta zame ta kwanta,kuka take son yi ko za taji saukin abunda yake damunta but the tears do not pour out,da taji zuciyarta na neman tarwatsewa a dalilin damuwa ta d'auki wayarta a hankali ta shiga applications side ta bud'e alk'ur'ani,zuciyarta a raunane ta fara karanta suratul anbiya'a in a kind of sad voice,ta d'auki lokaci sosai tana karatun until she reaches the suratun noor,,idanunta da suka cika taf da sababbin hawaye ta lumshe,while k'asan ranta tana jero addu'o'i akan Allah ya sauk'ak'a mata damuwar da take ji a ranta,even though ta ji sauk'in damuwarta da kashi 80,but still tana ji a ranta ba wai damuwar da take ciki ne yasa sauran damuwarta bai gama gogewa ba,sai dan tana jin tsoron halin da mahaifinta yake ciki,after she had cried a sad'ad'e ta tashi ta shiga toilet,sai da ta fara yin wanka and then ta d'auro alwala,after ta gama y'an sabgoginta bata yarda ta fita ba ta kwanta saman bed had'e da rufe idanunta,duka ranar haka ta dunga jinta cikin fargaba da rashin tabbas har gari ya waye,but still bata fasa yiwa mahaifin nata addu'ah ba akan Allah ya kawo masa sauk'i cikin al'amuransa.
Chapter 75 · 0% Book details