Sashe 149
Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
A sad'ad'e tayi shiru bata ce komai ba har suka gama waya da Afaf ta kira su Kalthom suka sha hira,sai da ta bari ta gama komai,ta kalleshi ta b'alla masa harara because ta fahimci murmushin da yake yi mata then ta wuce bathroom,sarai ya ganta ya ga abunda tayi but sai bai yi mata magana ba ya ci gaba da murmusawa abunsa yana clicking computer,Nusrah kam tana shiga bathroom wurin first aid drawer d'insu ta wuce,dama ta bayar an siya mata abun gwajin ciki,tayi murmushi ta cire guda,ta fara yin fitsari bayan ta saka kan tsinken ta ajiye ta wuce ta cire kayanta,bayan ta gama wankan,she tied a towel and went to the place where she put the thing,idanunta suna sauka kai taga it marked two lines,ai bata san lokacin data fasa k'arar murna ta fara tsalle ba,Nuraz yana zaune yaji ihunta da sauri ya ajiye computer ya nufi hanyar bathroom yana kwala kiran "Roohii! What happened? Open the door please!" yadda ta jiyosa yana magana yasa ta d'an nutsu but continue to dance in the bathroom,yana tsaye bakin bathroom d'in rik'e da handle jin shiru bata zo ba yace "Open the door i said" murmushi ta saki tana yarfe hannu da d'an tsalle,then ta k'arasa jikin k'ofar ta bud'e,a rikice ya rik'ota yana lek'en cikin bathroom d'in yana fad'in "ihun na mene ne kike yi?" Murmushi tayi tana kallonsa sai ta sake fasa k'ara ta k'ank'amesa tana fad'in "I'm pregnant Hayat!" Wani irin zaro ido yayi na surprise sai kuma ya d'agata suka fara juyi a gurin in a state of ecstasy,sai da suka d'auki lokaci suna murna ya tuna ya sauketa yana kallon idanunta yace "ya akayi kika tabbatar?" Bakinta ya k'i rufuwa sam ta nuna masa stripes d'in tana cewa "I did the test" wani wawan runguma ya sake yi mata,a guje ya sureta yayi sama da ita,bai direta ko ina ba sai saman bed yana cewa "woah! Yarinya Allah ya kaman min ke,dama tunda kika yi musu yau zanyi shagali" wani zaro ido ta fara yi sai kuma ta had'e rai ta fara k'ok'arin sauka daga bed d'in tana cewa "Ni wallahi babu wani abun da zaka min" murmushi ya saki da sauri ya rik'o waist d'inta ya had'a jikinsu,yana kallon fuskarta da tayi kicin² yace "Didn't i tell u not to make a hasty decision?" Ta sake had'e rai tace "tou ni ina ruwana? Do i have anything to do with u?" Yace "ba ruwa ba har river nile ma kina da shi in dai da ni ne" ta hararesa ta murgud'a baki tace "Let me go na shirya,gurin Mom ma zanje naga baby na,tunda ita ta yi min yaji" yayi dariya yana d'ora hannunsa a wuyanta d'ayan kuma ya saka cikin towel d'inta yana feeling yace "O'ohhh! Kin sauke fushin da kike yi ne madam?" Ta tab'e baki tace "tou ni ya zanyi idan ban daina ba? Bayan a kanta ma sai da kasa naji duk na rasa k'warin jikina" yayi murmushi,bai ce komai ba yana kallonta ya d'aga ta,a hankali ta sauke hannayenta a wuyansa tana kallonsa yayi mata murmushi yana lumshe idanunsa yace "thank u" tayi dariya kafin tayi magana ya wuce da ita gaban mirror. Shi ya shirya ta tsaf in a royal blue na wani summer women wide leg rompers cotton linen backless jumpsuits ya kawo turban cap yasa mata,lips d'inta sun sha red chapstick,yadda tayi masifar kyau a cikin kayan shi kansa sai da ya sake yana kallonta,tayi juyi a gabansa tayi fari da idanu tana d'aga masa gira tace "ya ka gani?" Yayi ajiyar zuciya yana rungume ta tsam a jikinsa cikin kunnenta da wani munafukin voice yace "U're so beautiful,i love u" ta k'ifta idanunta tana sakin sirrintaccen murmushinta ta rik'o hannunsa da sauri tace "love u too,muje tou naga Babynah" yayi murmushi daga haka ya rik'ota zuwa gefen jikinsa suka fice daga apartment d'in.