← Book details Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 152

Sashe 50

Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Yana shiga bedroom he took nothing but his car keys,the nerves in his forehead duk sunyi bar'o bar'o,ya fito a fusace had'e da banging door d'in ya kama hanyar fita,Nusrah tayi saurin tashi ganin zai fita and begins to run after him cikin tashin hankali tana masa magana,babu wanda ya kula yayi ficewarsa,ta dafo masa baya har waje,ya bud'e front seat ta side d'in driver ya shiga ya kulle yana k'ok'arin tada motar tayi saurin bud'e d'ayan side d'in ta shiga,mukullin tayi saurin cirewa ya d'ago idanunsa ya sauke akanta cikin hayaniya yace "give it to me.!" Yana mik'a mata hannu,ta girgiza kai tace "A'ah" yace "Ba ni ki fita nace.!" Ta sake girgiza masa kai tace "Ba zan bayar ba" cikin k'arfin hali,wata uwar tsawa ya buga mata yace "Za ki bani ko saina shak'e ki kin rasa numfashi.??" Ta d'auke kai gefe tace "will u try.!?" Tana turo masa wuyanta,yayi k'wafa yana jijjiga kai bai ce komai ba,ta koma ta zauna sosai tana kallonsa tace "Wane irin zafin zuciya ne haka.!? Daga zuwan mata baka jira ka ji abunda ya kawo ta ba kawai ka hauta da masifa,dama laifin wani yana shafar wani ne.?" Ya juyo a fusace ya fizgota ta fad'o jikinsa a firgice,yana zare idanunsa da suka koma ciki,da wata irin kakkausar murya yace "Give me my key and then hurry to get out from my sight" duk da ta tsorata da shi hakan bai sa ta fasa ba tace "Bazan bayar ba" ya daka mata tsawa yace "Ke bani nace" ta gyara bakinta tace "Sai kayi kuma" hannunta ya dank'o zai b'amb'are ya kwace key d'in tayi maza ta tura shi cikin riga,he lifted his red eyes over her yayi k'wafa angrily pushed her back ta koma ta zauna,her head hitting the car's cover ta saki k'arar azaba,da sauri ya rik'o ta bakinsa har b'ari yake wajen fad'in "Sannu! Baki ji ciwo ba.!?" Ta d'ago idanunta ta sauke a kansa,ya janye hannunsa daga jikinta da sauri ya harareta,ta tab'e baki kad'an tace "Idan naji ciwo ma ai kai ka janyo" ya tab'e baki yana kallon waje "Ko kuma ke ba,ni na shiga sabgar ki ko ke kika shigo nawa.!?" Ta juya tana kallonsa tace "Mu duka muka shiga harkar juna,amma kaine ka fara" ya juyo da kansa yana kallonta "Kada ki rainawa kanki hankali ni na biyo ki ko ke kika biyo ni.!?" Bata yi magana ba tace "Sai kuma kayi" yace "Sai muyi dai" ta tab'e baki tace "Wai daka fito ma ina zaka je da.!?" Yace "Ina ruwanki da inda zanje.!?" Tace "Ruwan nawa dana gani shi yasa nayi tambayar ai" yayi siririn tsaki bai kulata ba,ta sake juyowa tana kallonsa,yadda yayi kicin² kamar wanda aka aikawa sak'on mutuwa ta tab'e baki k'asa² tace "Mutum sai miskilanci" yayi saurin juyowa yace "Me kika ce.!?" Tace "Ina ruwanka ko kaji nace kai.!?" A fusace ya dank'o ta cikin fushi yace "Maimaita abunda kika fad'a yanzun" tace "To ina ruwanka ne wai ko da kai nake.??" Ya kalli k'wayar idonta dake k'ik'k'iftawa ya saketa yace "Mutum sai shegen tsoro" ta tab'e baki bata ce komai ba sai tambayar da ta sake yi masa "Where do u think to go.!?" Ya d'auke kai yana kallon waje yace "Bar!" A sukwane ta juyo idonta a wajen tace "What are u going to do.!?" He didn't bother yace "Me ake zuwa yi.!?" She carefully stared at him tace "Dama kana sha ne.!?" Ya d'age shoulder's yace "I'm going to start today" hankalinta a tashe ta juyo dukanta ta fuskance shi tace "Pleasee don't go" ya juyo yayi mata wani irin kallo yace "Why not.!?" Tace "Dan girman Allah ba don ni ba" ya tab'e baki yace "I haven't made a promise to u bazan je ba ko bazan sha ba" tayi shiru tana kallonsa ta rasa abunda zata fad'a,can tace "To wai duk mene ne ya janyo.!?" Kai tsaye yace "B'acin rai" tace "Saboda b'acin rai then u rebel against ur Lord ko.!?" Ya juyo ya kalleta ya d'auke kai yace "Kinga Malama first give me the key and then naje na dawo sai ki min lecture" ta marairaice tace "Dan Allah ba don ni ba kace ka fasa zuwa,babu kyaufa kaima ka sani,sannan idan ka sha ka san nau'in sab'on da zaka aikata kana cikin maye.!?" Ya juyo yana kallonta ya tab'e baki "Ina ruwanki da sab'on da zanyi,naga dai kaina zan d'aukarwa nauyin zunubin ko.!? Besides iyaka ace bayan giya na nemi mace,shi kenan fa" hawayen idonta tayi k'ok'arin mayarwa tace "That's not it" yace "So what.!?" Tace "The sin and the severity of guilt will continue to spill over ur family" yace "by then i will repent" cikin hayaniya tace "U will repent.! Daga baya kenan ko.!? Are u sure ma ubangiji zai barka har ka gama aikatawa sannan ka tuba.!? Ko kana da grantee idan ka tuba he will forgive u.!?" Yace "Of course he will forgive me" a fusace ta juyo hawaye suna sakkowa a idonta tace "well.! Tunda kace haka" keys d'in ta ciro ta mik'a masa tace "Ja motar muje" ya juyo yana kallonta yace "where are we going.!?" Tace "Inda zaka je" yayi murmushi ya tada motar suka fara tafiya,a bakin *Round 6 bar & night club* yayi parking bata kula shi ba ta bud'e motar ta fice,ya juya zai mata maganar shi da wasa yake mata dan baya so ta dame shi ne,yaga har ta fice ya fito da sauri a tunaninsa idan sun zo ba zata iya fita ba,shi tunda yake bai tab'a zuwa ba sai dai ya wuce yana yiwa masu shiga fatan shiriya,ya biyota da sauri yana kira tak'i tsayawa sai da ta jashi har ciki,da kyar ya risketa a bakin bar d'in ta haye saman stool tayi d'are² ya tsaya kusa da ita yana haki,ya sunkuya dai² kunnenta saboda sautin music da aka k'ure yace "What are u doing.? Did i told u to come in.!?" Bata kulashi ba tayi oder cup biyu na veer,ya zaro ido yana kallonta yace "Ki bari bana son abunda kike yi" ta d'ago ta kalleshi lokacin da me kula da gurin ya mik'o mata yana murmushi yace "A sha lafiya" She smiled at him ta d'auki cup za ta kai bakinta,quickly he twisted her arm ta dago ta kalleshi tace "What's that.?!" Yace "Ba ki da hankali za ki sha.!?" Tace "u don't mind ka sha kawai" tana sakin wani mugun smiling as she took the other cup tana mik'a masa "Karb'i ka sha kaima dama abunda ya kawo mu kenan" ya k'wace cup d'aya a hannunta ya ajiye,yace "Kina hauka zaki ce na sha" tayi dariya tace "A'a na ji kace ne zaka sha,shi yasa nima zan sha" ya kamo hannunta zai kwace d'ayan cup d'in ta sake d'auko d'ayan yana kallonta da b'acin rai yace "Wai ke me yasa kike haka,daga fad'a miki zan sha shi ne saboda kin fini rashin hankali sai ki d'auka za ki sha.!?" Tace "Gani nayi kai fad'a kayi,ni kuma shi yasa zan aikata" yace "ajiye mu tafi to",ta d'ago tana kallonsa tace "A'a saina sha,kaima ka sha ga shi" tana mik'a masa kofin trying to put it in his mouth,a fusace ganin tana neman d'ura masa abaki ya doke kofin ya fad'i ya fashe,the explosion of the glass cup had to stop the music dake tashi hankulan turawan ya dawo kansu,hannunta ya dank'a a fusace yana k'ok'arin kwace d'ayan cup d'in tak'i saki yace "Saki" tak'i,juyin duniya yayi da ita ta saki tak'i data fusata shi bai san sanda ya kwasheta da mari ba babu shiri ta saki ya ajiye musu,ya zaro wallet d'insa ya cire kud'in da bai san nawa bane ya ajiye musu ya kamo hannunta ya shiga janta,tana dafe da kuncinta saboda shigar ta da marin yayi,yayi ta janta sai da suka fito some of the onlookers were stepped behind him yana fitowa ya bud'e mota ya jefata,ya zagaya d'ayan side d'in ya shiga ya tada motar,da mugun gudu ya bar gurin yana dana sanin ambaton zai sha da yayi da jan istigfari a zuci,har suka shigo line bai kalleta ba,itama bata fasa kuka ba,ya gyara parking bai kalleta ba yace "get out" bata kalleshi ba tace "Mari na fa kayi" ya juyo a fusace yace "Na mare ki,za ki rama ne.!?" Ta sake fashewa da kuka,cikin kuka tace "To kawai daga cewa zan sha sai ka mare ni,tun farko kai me yasa ba'a dake ka ba da kace zaka sha ka nemi mata.!?" Ya tsaya kallonta da sakakken baki yace "Da nace haka ina ruwanki.!?" As she added the volume of her cries tace "To ni da nayi ina ruwanka da ni.!?" Ya matse forehead a masife yace "Be quiet.! Don't let me feel too bad yanzun ki janyo na zane ki" tana kuka tace "Allah nima saina fad'awa Annie abunda ka yi" yace "kada ki fasa maza go and tell her,but ki tabbata from the time kika fad'a from that time i will begin to do what i didn't intend to" ta juyo da sauri tana tsayar da kukan tace "What are u going to do.!? Giyar za kaje kasha ka nemi matan.!?"
A fusace yana mata tsawa yace "Ehh! Su d'in zanyi ina ruwanki idan na yi.!?" Ta sake fashewa da kuka tace "Allah ba zaka jeba,kuma duk wacce ka nema Allah saina.." Bata k'arasa ba yace "Sai kin yi me.!?" Cikin hayaniya tace "Ina ruwanka da abunda zanyi.!?" Ya jinjina kai yace "get down" tace "bazan fita ba wollahi sai dai mu fita tare" yayi shiru yana kallonta yace "ke fita nace,komawa zanyi tunda ke baki da hankali" tace "Rashin hankalin yasa nace zan sha beer d'in,if u want by then u can took me as ur prostitute.." Ya juyo a firgice "do u know what u're saying.!? Ba ki da hankali ko.!?" Tace "u don't care! Since i have no value da za'a iya aure na a zauna da ni,na yanke shawaran zame maka karuw..!" Bata karasa ba ya shak'o wuyanta cikin masifar zafin rai yace "If u repeat it again wollahi sai na ji miki ciwo,baki da hankali baki da tunani kike kiran kanki da wannan sunan.!? Ko su karuwan da suka tsallake gaban iyayensu suke zaman kansu suna gudun a kira su da sunan shi ne ke dan baki da lissafi kike neman sawa kanki.!?" Ya tura ta baya ya daki steering wheel a zafafe ya furta "Tur da wannan furucin,fita ki bani guri,,fita nace" ya k'arasa yana mata tsawa,ta had'e kai da guiwa ta sake fashewa da kuka mai tsanani,ya dafe kai he felt himself regretting akan maganarsa,sun jima a haka idanunsa a lumshe banda neman gafarar Ubangiji babu abunda yake yi,ta sassauta kukan a hankali in a frightful voice ta fara magana.....
Chapter 50 · 0% Book details