← Book details Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 152

Sashe 42

Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Maganar Mommy taji a kunnenta cikin wannan hayaniyar nata _"To yace baya buk'atarta shin dole ne sai ya dawo da ita gidan nan.!? Ta bayyana cewa itan fasik'a ce,and we said we removed it from our house.!? Malam ka ga tun da wuri ku tattara ku fita mana a gida,mun yafewa duniya ita,idan ka ji baka iya rik'onta kaima daka d'aukawa kanka wahala kana iya sallamarta tayi gaba,duniya da fad'i duk inda take so zata iya zuwa ta rayu.. Wa ya sani ma ko garin yawon ta kwaso wani mugun ciwon shi yasa ta lallab'a ta dawo gida,shi kenan bamu sani ba tazo d'aya bayan d'aya ta goga mana.! Na tabbatar ruwa baya tsami banza,dole akwai sharrin data k'ullo shi yasa ta dawo.. An yi gadon bak'in hali.."_

_"Ni naga damar cire ta daga jikina babu ruwan Hajiya,saboda haka idan iya wannan maganar ta kawo ku,heard my words,,,wish u could go and leave my house.."_

_"Alh ya kamata kayi tunani dai gudun wata rana kada ka zo kana nadamar abunda ka aikata.!"_

_"There is no thought to waste my time on it,it is a final decision banga dalilin da zaisa nayi nadama ba kuma."_

Maganganun ne suka had'e mata a guri d'aya cikin wani irin yanayi suna sake yi mata amsa kuwwa da k'arfi a cikin kanta,hawaye sun gama wanke mata fuska cikin tsananin damuwa ta kama kanta ta rik'e,ji take kamar zai fashe saboda yadda maganganun mutane ukun suke repeating mata kansu babu sassauci,durk'usawa tayi saurin yi tayi kneeling saman k'afarta cikin tsananin damuwar da bata san mene ne zai iya faruwa a gaba ba ta fasa k'ara mai ban tsoro.....

*#thank u my people,u don't worry about it,as u express ur concerns in sha Allah i'll not be ashamed of u,it has already passed,so let by gone be by gone.. I love u all.♥*

#Share pls.
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©®2020.*      

                   *'DAN MACE..*
              (Tʜᴇ ᴘꜱʏᴄʜɪᴀᴛʀɪꜱᴛ)..💥

*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*    
https://my.w.tt/29u2S26SG2

Pᴀɢᴇ 21.
#Mɪɴᴅꜱᴇᴛ

       Bayan fitar Hajiyarsa a apartment d'in tunani yayi ta yi yana jin yadda zuciyarsa tayi masa nauyi saboda damuwa,yayi shiru shi kad'ai kamar wanda aka tsikara ya kira Clark,ya shigo cikin girmamawa ya ce "Here i am sir" RAFEEK ya kalleshi idanunsa sun k'ank'ance sun canja launi yace "Ina report na binciken dana sa kayi min.!?" Clark yayi ajiyar zuciya yayi tunanin wani abune daban yasa boss d'in kiransa,yace "Sir ana nan ana binciken,but kamar yadda ka buk'ata,duk binciken mu ya tabbatar mana babu wani namiji a gidan sai wannan likitan mahaukatan" Rafeek ya kalleshi cike da son k'arin bayani,yace "Ka tabbatar babu.!?" Ya gyad'a kai yace "Sure sir" yace "Sai kuma me ka samu.!?" Yace "Sir. Maganar matar da kayi,gaskiya tunda muke zuwa bamu ganta ba,amma dai muna yawan ganin shi Dr Psycho d'in tare da wata" Rafeek ya zuba masa ido yace "Wata kamar yaya.. Aure ne da shi.!?" Clark yace "Ban sani ba sir,but kullum tare suke fita,wani lokaci tana dawowa ita kad'ai a cab,ko su dawo tare da shi" ya tab'e baki yace "Bana zaton yaron nan yana da aure,but abunda za kayi shi ne idan ka sake ganinsu sun fito ka bi bayansa kaga inda yake kai ita waccan d'in da kace suna fita tare" Clark ya amsa da girmamawa,Rafeek yace "jeka idan ka samu wani abu ka sanar da ni.!" Ya amsa sannan ya fice dai² lokacin da Hajiya take k'ok'arin shigowa,ya koma ya kwanta yana rufe idonsa,Hajiya ta k'araso tana kallonsa,sai data zauna sosai sannan ta tab'a shi,ya bud'e idonsa a hankali ya sauke su kan mahaifiyarsan,tace "Rafeek waye ka sa ayi maka following footstep nasa.!?" Bai damu ba yana sake rufe idanunsa yace "My kid" tayi squeezing face looking tana neman k'arin bayani,tace "Ka samu inda suke zaune ne.!?" Ya gyad'a kai ba tare daya bud'e idanunsa ba,tace "Me yasa to baka je da kanka ba.!?" Yayi saurin bud'e idonsa yana kallonta da idanunsa a waje,a tsorace yace "Hajiya naje fa kika ce.!? Idan tana da aure fa.!? Shi kenan na jefa kaina a masifa.??" Ta girgiza masa kai tace "Ba nufi na kaje gidan ba,ka je ka nemi yaron kuyi magana da shi" ya girgiza kai fuskarsa tana turning zuwa wani irin yanayi yace "Hajiya ba zai tsaya muyi magana ba" tace "Me yasa.!?" Duk hiran da aka yi da shi d'azun daya gani ya kwashe labarin ya sanar mata,Hajiya tayi shiru tana tunani kafin ta d'ago kanta ta kalleshi tace "Duk da haka dai kayi k'ok'arin ka samu kusanci da shi" yayi shiru yana tunani kafin ya amsa,bcos baya son ya sake yin musu da maganarta,bai san mene ne zai gani ba kuma gaba yace "Shi kenan Hajiya in sha Allah zanyi yadda kika ce",tayi ajiyar zuciya bata sake cewa komai ba,sai can ta tuna tace "Kun yi magana da Maimunatu.!?" Ya girgiza mata kai yace "A'ah" tace "Ok.! D'azun munyi waya tace zata kira ka,da na fad'a mata ka ga Hauwa'u,amma baka gano inda take ba" yayi ajiyar zuciya yace "Bamu yi waya ba" tace "Wata k'ila zuwa anjima ta kira" bai sake magana ba ya sake rufe idonsa saboda maganar ma wahala take bashi idan yayi,ji yake k'irjinsa yana masa wani irin ciwo da kyar yake samu yake fitar da numfashi ma a time d'in.

***
       Ihunta shi ne ya janyo hankalin Nuraz da sauri ya d'aga kansa ya kallo inda ya barta zaune d'azun daya shigo,mik'ewa yayi saurin yi ya d'auki robe d'in yasa da gudu² ya tsallako realer wajen duk tsayinta ya sakko ya nufo gurin,a durk'ushe ya ganta saman grasses tana kuka mai tsuma zuciya,ya k'araso inda take ya tsuguna yana kallonta fuskarsa d'auke da damuwa ya fara tambayarta "What happened.!?" Ta d'ago jajayen idanunta da suka rikid'e tana ci gaba da kuka mai tsanani,sake tambayarta yayi ta kasa magana gaba d'aya,banda kuka babu abunda take yi,yayi still yana kallonta har na wani lokaci,ganin bata da niyyar yin magana yasa shi mik'ewa zai bar wajen,taku uku yayi ya jiyo maganarta ya dakata kad'an yana saurarenta
   "I don't know what to do.! How can i tell him the story.!?"
    Yayi saurin juyowa yana jifanta da wani irin kallon bai fahimci abunda take fad'a ba
      "He said he wanted to hear it,i didn't know how to tell him what had happened to me.. How could i tell him that my father drove me out of his house.? Ba ni da wani y'an uwan da suka fi min ku a rayuwa ta,idan ya sani zai iya aure na a hakan.!?"
      Kasa sake motsawa yayi ya zuba mata idanu yana kallon yadda take yi kamar za ta cire ranta ta jefar,a hankali ya dawo inda ya tashi ya sake tsugunawa kan k'afafunsa,shiru yayi na kusan mintuna biyu kafin ya samu k'arfin guiwar tambayarta "Did he asked u.!?"
      Ta sake d'ago jajayen idanunta ta sauke a kansa ta kad'a masa kai,yayi shiru yana tunani zuwa wani lokaci yace "What are u crying for,tambayar da yayi miki ne bakya so.!?"
      Tayi saurin sake kallonsa ya kawar da kansa kad'an yace "Whatever happens,try to tell him the truth of ur situation.. The lie does nothing but ruin ur dignity.. If he really care about u zai iya zama dake no matter who u are or what kind of life u face,every person who truly loves u idan har kin fad'a masa gaskiyar al'amarin ki will live with u till the end of life,,but sab'anin haka,surely ba so bane,muradi ne.."
        Ta kafe shi da ido ko k'iftawa babu har ya gama maganar,tace "to ni ai ban san ta yaya ne zan fad'a masa ba"
     Yace "Do ur best ko yaya ne ki fad'a masa,idan ba son ki yake tsakani da Allah ba za ki gane da kanki."
   Ta sake gyad'a masa kai a hankali tace "if i tell him shi kenan.!?" Ya gyad'a mata kai a hankali,ta fara share hawayenta tace "Ok.! I will tell him",ya d'aga kansa looking at the sky yace "Do u love him that much.!?" tambayar da yayi mata tasa ta kalle shi,a hankali tayi taking deep breathe ta gyad'a masa kai,ya d'an rik'e gefen lip d'insa kad'an yace "Ok.! talk to him,idan kun yi waya kice masa yayan ki yana son magana da shi,sai ki bashi number muyi magana"
      Ta tsaya kallonsa tace "What would u say to him.!?" Bai kalleta ba yace "Ba lallai ki san mene zan fad'a ba" ta marairaice fuska kamar za tayi kuka tace "To ni zan fad'a masa maganar.!?" Ya d'age shoulder yace "idan kina ganin ba zaki iya fad'a ba,ina ganin ki tsayar da alak'ar ku shi yafi alkhairi."
      Ta kalleshi za tayi magana ya tashi ya bar gurin,saurin tasowa tayi ta biyo bayansa tace "To ai baka bari mun gama magana ba" yana ci gaba da tafiya yace "What else do u want me to say.!?" Tace "To ai ni baka bani shawaran yadda zanyi ba"

      Ya tsaya bakin entrance yace "What.!?"
Chapter 42 · 0% Book details