← Book details Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 152

Sashe 78

Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

As Annie walked out of the parlor,Nuraz dake cike taf da bak'in ciki ya dakata yana kallonsu yace "Annie just go i'll come after u" yana fad'a yayi saurin juyawa zai koma,quickly Annie pauses and ask him "Where are u going.!?" Idanunsa masu cike da b'acin rai ya sauke akan Nusrah yace "Just go i'll follow u" Annie ta girgiza kai tace "Ka ga bana son fitina,idan ka koma me za kayi musu.!?" Yace "Amma Annie" hannu ta d'aga masa tace "Kawai ka wuce muje,duk abunda mutum yayi kansa ya yiwa" ba don ya so ba haka ya wuce suka fita,sai dai duk da hakan yana jin ba zai iya hak'uri ba,dole ne ya dawo ya karantawa matar nan,a wajen suka tarar da mai taxi d'insu yana jiran fitowarsu,jikinsu duk a sanyaye suka fara shiga mota,Nusrah kam tafiya kawai take tana share hawaye da waiwayen gidan a haka har ta shiga ta zauna,mai taxi dake jiran su gama shiga ya tayar da motar su tafi yaji an bud'e get,ko da ganin sun gama shiga nan yayi saurin yiwa mota key yana k'ok'arin barin gurin drivern dake cikin motar data fito daga gidan da sauri ya d'aga masa hannu,tsayawa yayi kad'an har ya k'araso gurin da suke,back seat ya lek'a yana kallon fuskar Nusrah yace "dama Alhaji ne yace ayi muku magana" duka suka bi driver'n nasa da kallon mamaki,kafin suyi magana Abba'n Nusrah ya k'araso gurin jikinsa har tsuma yake yi yana tafiya yana waiwaye,babu wanda yayi magana a cikinsu duka suka bud'e mota suka fito,suna binsa da kallon tausayi da jiran abunda zai fad'a da yasa aka tsayar da su,bawan Allah yanayin da yaga fuskokinsu duk sai ya shiga damuwa muryarsa tana rawa yake basu hak'uri akan abunda ya faru,Annie dake kallon Nuraz da yayi wani irin tsaiwa yana kallon mutumin da wani irin yanayi mai tattare da jin haushinsa tayi saurin yin magana "u do not worry about what happened Alhaji,idan zaman Nusrah ne a gidan nan matsalar matarka,we will take her back in Allah ya yarda ba zamu gagara bata kulawa ba,sai dai shawarar da zan baka ka dage da addu'ah" tana gama fad'a masa ta juya kansu tace "Ku shiga mota mu tafi" kamar masu jiran umarninta duka suka shiga mota,har za ta wuce ta waiwayo tana fad'in "Daga nan zuwa duk lokacin da kaji kana son ganin y'arka,this is the number u can find us" tana fad'a ta mik'a masa d'an k'aramin complementary card d'in data zaro a jaka,kai kad'ai ya iya gyad'awa ya karb'a,kamar wani soko haka ya bisu da ido har suka bar wajen bai iya cewa wani abu ba.

Since suka baro gidan no one spoke again saboda yadda suke jin zuciyoyinsu a cunkushe da damuwa,motar su tana yin parking a bakin get suka fice Nuraz ya tsaya ya sallami mai taxi d'in and then ya biyo bayansu,a bakin entrance ya tarar da Nusrah tsaye saman varenda,da mamakin abunda take yi a fuskarsa yake binta da kallo har ya k'araso,yana shirin yin magana ya jiyo k'arar horn juyawa yayi kad'an,fitowar mai gadinsu yasa shi binsa da kallo har sanda ya gama bud'e get,hankalinsa a gurin yana kallon manyan Jeep d'in dake tsaye ta waje da mamaki har sanda suka jero ciki suka yi parking a harabar gidan.....

#Share pls.
#Asli Smasher.
💠💠💠💠💠
*©®2020.*

*'DAN MACE..*
(Tʜᴇ ᴘꜱʏᴄʜɪᴀᴛʀɪꜱᴛ)..💥

*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
https://my.w.tt/29u2S26SG2

Pᴀɢᴇ 35.
#Fᴏʀᴛᴜɪᴛᴏᴜꜱ

Manyan motocin da suka parker a harabar gidan suka bi da kallo,even though they were new but d'aya daga ciki kana kallo za ka gane ba'a tab'a hawanta ba until today,duba da yadda take shek'i and its seats are all covered,daga Nuraz har Nusrah kamar wad'anda aka sassak'a haka suka bi motocin da kallon mamaki,drivern dake cikin had'ad'd'iyar sabuwar motar brand new toyota k'irar landcruiser prado TX ya fara fitowa da sauri tare da clark dake gaba kusa da shi,a tare suka nufi d'ayar motar dake gefe suka bud'e ta duka side biyu,Baba ne ya fara fitowa ta gefe d'aya sannan Rafeek ya fito ta d'ayan side,Nuraz dake tsaye yana jira yaga waye zai fito yayi saurin bud'e ido looking at them in amazemen har suka k'araso inda yake tsaye he couldn't make any movement,Nusrah kuwa didn't seem to wait for them tuni ta silale ta bar wajen,Baba's face with a kind of smile ya dafa shoulder d'in Nuraz yana fad'in "Kai Yallab'ai babu magana.!?" With a sigh of relief he kept his face smiling and welcomed them,a taren kuma suka nufi hanyar shiga gidan.
Shigowar Nusrah ne yasa Annie dake tsaye tana jiran ganin ta inda za ta b'illo kiranta,jikinta a sanyaye take d'aga k'afafunta har ta isa inda suke yayin da the tears she has been trying to put back on have begun to flow,duk da al'amarin daya faru babu jimawa yana damun zuciyoyinsu but ganin hawayenta ya sake tayar musu da hankali jikinsu ya sake yin sanyi saboda tausayin halin da take ciki,lolly na kallonta with a kind of tausayinta a zuciyarta take girgiza kai tana fad'in "Don't cry Angel please.! Wannan itace k'addarar mu,a duk lokacin da aka ce k'addara ki sani a servant is not enough to change what ever Allah has decreed against him,idan Allah ya so one day the story will repeat it self,but ki daina damuwa kinji muma muna jin babu dad'i" fashewa ta k'arasa yi da kuka kafin ta k'arasa kusa da Annie ta durk'ushe a gurin,hannayenta duka ta rufe fuskarta da su as she felt her heart hurt again,muryarta na season take fad'in "Astagfirullah wa'atubu ilaik..! Allahumma ajirniy fiiy musibatiiy wa'aklufniiy khairan minha.." Not only Lolly dake zaune even Annie ganin yadda take yi sai data karyar musu da zuciya,da sauri ta k'araso ta rik'eta a jikinta tana rarrashinta da yi mata nasiha mai shiga jiki,it didn't take long su Nuraz suka shigo cikin gidan,idanunsa suna sauka akan Nusrah jikinsa ya bashi akwai matsala,but ganin tare suke da Baba da Rafeek sai bai ce komai ba har suka zauna,da mamaki sosai a fuskokinsu suke kallon Baba da Rafeek,Nusrah dake jikin Annie jin sun shigo da sauri ta goge hawayenta bayan ta gaisar da su ta wuce bedroom jikinta a sanyaye,da ido Baba ya bita har ta bar wajen kafin ya juyo da hankalinsa kan Annie fuskarsa d'auke da tambayoyi ya kira sunanta "Maryam.!" Annie tayi ajiyar zuciya tana sunkuyar da kai ta amsa,Baba ya kalleta ya sake kallon lolly zai yi magana Nuraz ya tashi yabi bayan Nusrah,Baba ya sake bin Nuraz da kallo,bayan ya dawo da hankalinsa kansu yace "Where did u get that girl.!? Or.!?" Before he had finished speaking,Annie began to tell him how they had met Nusrah,jikin baba a sanyaye bayan ya gama jin labarinta ya girgiza kai yana fad'in "Ya Allah ka yafe mana,ba don halinmu ba."
Chapter 78 · 0% Book details