← Book details Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 150 OF 152

Sashe 150

Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna shigowa flat d'in suka tarar da Maysam sai cilli take da throw pillows tana ihu da dariya,Nusrah ta bud'a ido tana kallon y'arta da babu abunda yake damunta sai wasanni take abunta,Nuraz yayi murmushi yana sake mak'ale ta a jikinsa yace "kin gani ba,i told u dama bata tare da ko wane irin damuwa" tab'e baki tayi ta d'auke kai daga kallon Maysam tace "Mmm! Ai shi kenan tunda zan haifo wani baby'n soon,sai Mom su rik'e Maysam mu kuma mu d'auki new one" murmushi ya saki mai sauti yace "No! Ni bazan iya barinta ba,sai dai su karb'i sabon,kin san ko hausawa ma cewa suke da tsohuwar zuma ake magani" tace "if it's not available dole ayi da sabo ai" suka yi dariya a tare,Lolly ta taho hannunta rik'e da bowl tana fad'in "HABIBTIY! Where are u?" Da gudu Maysam ta sauka kan chair da take tsalle² ta b'oye bayan kujera tana lek'en hanyar da Lolly take tahowa,Lolly ta k'araso tana dubawa bata ganta ba,ta waiwaya a hankali suka had'a ido da Nusrah dake murmushi tana satan kallon inda Maysam ta b'uya,Lolly tayi dariya tace "yaushe kuka shigo min ku kuma?" Nuraz dake kallonta yace "Mom yanzun muka zo,where is my Dad?" Hannu ta watsa cike da zolaya alamun bata sani ba,za tayi magana da gudu Maysam ta fito tana ihun "Mami oyoyo!" Nusrah tayi dariya ta bud'ewa Maysam hannu ta shige jikinta tana dariya,Lolly ta bud'e ido tace "shi kenan na kamata" Maysam ta bata fuska while su duka suna yi mata dariya,cikin surutunta da zak'in murya tace "ni baci kama ni ba" suna yi mata dariyar yadda take rufe ido tana surutu Mr Rafeek ya fito daga bedroom,da suka zauna bayan sun gaisar da iyayen nan suka fara hira,yanayin yadda suke yi da irin shakuwar dake tsakaninsu idan ba wanda ya sani ba sai ya rantse Nusrah is not their daughter-in-law,they all set wani kunyar surukai aside,su a garesu kallon y'a suke mata,Mr Rafeek dake zaune yana kallon iyalinsa dake cikin farin ciki yayi wani lafiyayyen murmushi,Lolly dake zaune next to him tana kallonsa tace "lafiya dai Yallab'ai kake murmushi?" Ya sake yin murmushi yana kallon cikin idanunta cike da shauk'i yace "I just remember something about our past life" a 360 Lolly ta had'e rai tace "za ka fara kou?" Yace "Just as we can't change what has happened,i just can't stop talking about what i have done to u dear,ni kaina na san ban kyauta ba,and that's why har yanzun nake jin haushin kaina da fifita karatun boko akan addini na" ta tab'e baki ita dai bata ce komai ba,ya kalleta yayi murmushi yace "kin san wani abu kuma?" Tayi jim tana kallonsa tak'i cewa komai,ya sake yin murmushinsa mai kyau yace "kin tab'a tunanin wani abu game da abubuwan da suka faru da muka dawo UK? I mean before then and after? Shin kinyi tunanin abunda ya faru lokacin da kuke shirin tafiya ku barmu a airport?" Lolly dai ta zuba masa ido sai kallonsa take yi but ta kasa magana,yana yi mata wani irin murmushi yace "Everything that had happened long time ago,daga ranar da na fara ganin ku a bakin Ali Jericho store,har zuwa komai da ya faru tsakaninmu was all planned,except rashin lafiyan da nayi lokacin and Clark shi ne manager shi ya tsara komai" mamaki ne ya cika Lolly tana yi masa wani irin kallo tace "plan fa kace?" Ya gyad'a kai yana yi mata murmushi then ya fara bada labarin a nutse "Sure! Duk abunda ya faru was just a planned,taron y'an jaridun da suka zagaye mu and everything har zuwanmu gida tare all shirinsa ne" ba ita kad'ai ta ji mamakin maganarsa ba hatta su Nusrah duk sai suka mayar da hankalinsu kansa suna sauraren ya warware musu yadda al'amarin ya faru,here he began to explain "If u haven't forgotten,lokacin da muka fara had'uwa da ku was at Albert street kun fito daga store,sure a wannan lokacin da na ganki na shiga rud'ani da taraddadin anya kece da gaske ko kuma dai idanuna suke yaudarata? But before i can regain my composure har kun b'acewa ganina neman duniya babu ku a wajen,na shiga tashin hankali sosai da na duba ban ganki ba,because da jimawa na je Nigeria neman ku saboda na nemi afuwar laifin da nayi miki,sannan na tabbatar miki a shirye nake na karb'i yaro na sannan na dawo dake gare ni,but sai dai mun rasa inda kuke,we had a hard time in finding u,mun d'auki tsayin lokaci muna jiran samun labarin ko wanda ya tab'a ganin ku but we lost,daga nan bayan lokaci na dawo UK na bar komai a hannun Baba da Yaya Abdullahi,sai idan na samu aiki yayi min sauk'i nake zuwa na duba halin da ake ciki,a haka lokaci yayi ta wucewa babu wani feedback,cikin haka kwatsam Allah ya karb'i rayuwar Abbanah,bayan rasuwarsa still bamu hak'ura ba muna kan neman ku amma kullum shiru babu wani labari har d'auki tsayin shekaru.. Ranar da Allah yayi nufin za mu had'u na ganku a bakin Ali Jericho bayan na dawo cikin nutsuwata i just started to check where ur car had gone,but surprisingly ko k'urar inda motar yabi bamu gani ba,a nan na ji damuwata ya dawo sabo because i didn't even know zan sake ganin ki ko shi kenan kin sake b'acewa?" Yana kallon yaransa da ita kanta Lollyn da tayi shiru ta zuba masa idanunta yace "Do u know of any surprise? At this point da nake tunanin i just lost all the opportunities and hope,Clark was the first person to suggest mu duba CCTV footage na Ali Jericho,time d'in da sam tunanin yin hakan bai wani zo min a kai ba,but na amsa kawai saboda kada na bashi kunya,mun shiga cikin store yayi magana da manager,a nan shi da kansa ya shigar da mu control room and gathered all the operators suka fara bibiyar footage na hours back,tun daga farkon zuwan ku har k'arshe lokacin da kuka fita baby tana rik'e da ke duk mun gani,what we wanted to get a time d'in is ur cab number but unfortunately camera's basa d'aukan hoton wajen,jiki na ya sake yin sanyi na fara tunanin ina ne zan sake ganinki kuma? At the time because of the stress i was going through ciwo na ya dawo sabo,while a gefe d'aya kuma tun daga ranar kullum sai munje Albert street cike da saka rai akan za mu sake ganinku,it took us long har ya kasance ko ba na k'asar akwai security da suke zuwa su duba ko Allah zai sa a gano inda kuke,wata rana cikin irin lokacin da nake gari a lokacin mun fita bakin store na Ali Jericho haka kawai sai na tsinci kaina da son yin tafiyar k'afa,a hankali na bar securities d'ina a wajen because ba na son a dame ni,na fara tafiya zuciyana a raunane ina tunanin idan ban same ku ba mene ne zai faru? Ban san daga ina ko yaya aka yi ba sai naji na buge da wani abu,na tafi zan fad'i because i was not feeling strong naji an rik'e ni,ina d'agowa muka yi ido hud'u da Noor nan take gabana ya fad'i,at first glance da na yiwa fuskarsa nayi realizing lallai duk inda ya fito we had a strong connection,immediately kuma sai kalaman Hajiyata suka shiga dawo min,for 28 years i never thought about it but at the same time they came into my head as if she was saying it right away,abu na farko da ya dakatar da ni lokacin shi ne irin kallon da Noor yayi min,nan da nan naji wani irin abu yana shiga raina da jikina,i was very scared and afraid of how to explain wane ne ni da matsayina a gurinsa,haka ya wuce ya bar wajen but ban bari ya b'ace ba kamar yadda kika yi,nasa aka bi bayansa,tun daga ranar sai naji na fara samun sauk'in damuwata,while a gefe d'aya nasa ana bibiyarsa but babu wani gamsashen bayani,wata rana again time d'in ina zaune ina kallon program a BBC,all of a sudden sai ga Noor ya sake bayyana,so it was there na samu duk amsoshin da nake nema game da shi,but the fear of how to deal with the problem is what really stops me every time i intended to approach u,wannan tsoron da Clark ya fahimta a tare da ni da fahimtar gaskiyar al'amarin da yake tsakaninmu,ya same ni da batun and informs me he has a plan to make if na bashi dama,ni kuma lokacin da yake ba wani ganewa nake yi sosai ba kullum ina cikin damuwa da ciwo na amsa masa,tun daga ranar he continue to run his plan without my knowledge,batun Noor kuma tun ranar da ya gane suna binsa na dakatar da Clark from his follow-up,abubuwan da suka faru in the past na san kun sani,though zuwan mu Nigeria na san kun yi mamaki a lokacin da muka had'u,but shima dai ba wani abu ne na musamman ba,because tun a ranar da kuka bar k'asar da muka je gidan da kuke zama muka samu labarin babu jimawa jirginku ya bar k'asar,da muka samu labarin Nigeria za ku tafi here na yi deciding mu biku can d'in,daga nan muka koma gida muka yi sallama da Hajiyata tayi min addu'ah... Sai ga shi zuwan ya zama wani babban nasara a tare da ni,i didn't think of any problems zai faru tsakaninmu until we got back to UK,lokacin da kuke k'ok'arin barin airport hankalina ya tashi na kasa tunanin komai,here Clark said he knew what he was going to do,so a nan dai yayi magana da y'an jarida,ba'a d'auki lokaci ba saboda dama kullum cikin jiran kad'an suke sai ga su kamar kuraye sun zagaye mu suna neman labari.. I was very happy with the idea of Clark because i didn't think it would work,but damar da na bashi ya janyo min nasara,har abunda ya faru ya so zarta tunani na,wannan ya sake ba ni damar amincewa da Clark,a dalilinsa yau gashi ina rayuwa cikin farin ciki da nutsuwar da ciwon da nake tare da shi,ake tunanin nan da wani lokaci zan iya rasa rayuta yayi sauk'i sosai,even the doctors themselves wondered what was the cause
Chapter 150 · 0% Book details