← Book details Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 152

Sashe 74

Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Haka aka zauna jigum parlor'n ya sake d'aukan shiru,bayan dogon lokaci Baba y'a numfasa cike da jimami yace "Maryam kin ce kuna cikin garin nan,shin a wane garin kuke zaune.!?" Ajiyar zuciya Annie tayi ta bashi amsa da "Baba a Sardauna crescent ne" Baba ya k'ura mata ido yana maimaitawa,quickly kuma he turned to look at Rafeek's side yace "Cikin wannan gidan kuke.!?" Da mamaki a fuskar Annie tace "Baba wane gida.!?" Yana nuna Rafeek yace "Gidan da ya fad'a min ya mallakawa.." Bai k'arasa ba Annie tace "Shi ne Baba" Baba ya dafe chin d'insa da hannunsa cikin rashin yarda yace "Wannan gidan dai da muka je neman ku.!?" Not only Annie even Nusrah,Nuraz da Lolly sai da suka kalleshi,cikin alamu na mutumin da bai yarda da maganar da yaji ba Annie tace "Baba wane gida ne kuka je,gidan mu.!?" Ya girgiza kai with tears streaming down yace "Idan har gidan da Rafeek ya mallakawa y'ar uwarki kuke zaune me yasa duk zuwan da muka yi ba mu tarar da kowa a cikinsa ba.!?" Annie ta goge gumin daya tsatstsafo mata tana sauke ajiyar zuciya tace "Sure Baba a wannan gidan muke rayuwa tun tsayin lokaci... Sai dai wasu lokutan da muka kasance bama garin,but here we live",a nan ne ta sanar da Baba asalin labarin daya faru tun daga korar da yayi musu,har zuwa yanzun da suke zaune gabansa,Baba da duk wani mai raunin zuciya dake zaune a gurin banda kuka babu abunda suke yi,cikin kuka Baba yake fad'in "Ya Allah ka gafarta min laifukan dana aikata,ya Allah ka yafe min,ba don halina ba,shin da wane baki zan amsa tarin tambayoyin da zasu riske ni a lokacin da na ganni gaba gareka.!? Ya Ubangiji kaji k'aina.." Kalmomin da Baba yayi ta maimaitawa kenan Rafeek kuwa ji yayi inama k'asa ta bud'e ya shige saboda tsananin kunyar abunda ya aikata,haka Baba yayi ta bawa su Annie hak'uri yana sake neman gafarar su,after sun samu yayi shiru da kyar Annie ta kalli Baba bakinta d'auke da tarin tambayoyi tace "Baba.!" Before she could say something Baba ya tari numfashinta "I was wrong dana kasance mai son kai,na kasance wani irin uba mai biyewa zugar shaid'an da son zuciya,da ace ban aikata wannan kuskuren ba da haka bata faru ba,,why should i become such a father.!? why.?"³ ya k'arasa da wani irin voice mai ban tausayi,lokaci guda jikin kowa dake parlor'n ya sake yin sanyi,Nuraz raised his eyes da suka yi wani irin narkewa kamar zai rusa ihu ya kalli gefen da Rafeek yake,even though ya san akwai k'addara aikin abunda ya faru but laifinsa da halayyarsa ne suka janyo,bayan shi kuma babu wani mutum da ya kamata a zarga a duk cikin abubuwan da suka faru shi ne silar faruwar komai,Baba ya goge hawaye ya ci gaba da magana "Twenty-eight years ago at the time of the incident,after all of u had left home there was nothing daya dameni,haka nan political issue ban fasa ba,but the incident that happened a cikin gida na ya baza gari cikin k'ank'anin lokaci,,wannan matsala kuwa shi ne ya zame min babban k'alubalen dana fara fuskanta and which is why people start condemning nawa a harkar siyasa,but despite this incident ban canja ra'ayi ba saboda a nawa tunanin,gani nake abunda mutane suke fad'a this is how really it is,by this time everything has turned me away from politics,yayin da a gefe guda wanda yayi min jagoranci na tsaya takara aka wayi gari lokacin da za'ayi primary election ba tare da ya sanar min ba ya sauya candidate,sai a ranar da za'a gudanar da zab'e aka kira ni a waya aka sanar da ni party ta canja d'an takara,my mind was blown after i heard about the change of candidate,na kira shi domin na ji yadda batun yake,here he let me know party leaders decided to change the candidate saboda basa so sunan jam'iyyar su ya b'aci ta dalili na,saboda haka suna masu ba ni hak'uri abisa rashin sanar da ni da wuri da basu yi ba,,lokacin da kunnuwana suka jiyo min wannan sak'on kamar zautacce haka na koma tunani na da duk wani damuwa ta shi ne,the money that i save and those da na samu alkhairinsu a wajen mutane duka na k'arar da su a harkar campaign da tunanin idan na hau karagar mulki zan samu wanda suka fi su,sai ga shi al'amarin ya sauya tun kafin aje wani mataki,ina ji ina gani haka aka yi zab'e aka gama ya tabbata babu suna na a cikin candidates,a wannan lokacin na yi bak'in ciki wanda ya janyo har fita ta so gagara ta saboda yadda ake nuna ni a gari ana zund'ena da zagi na,after a while al'amura suka fara tsanani,d'an abunda na tara a gida a hankali ya fara k'arewa,dole ba don na so ba na ajiye damuwa na fara fita ina buga² though abunda za muci wani lokacin da kyar nake samowa but i kept trying to find food to eat,in four years i have no job but a haka muka ci gaba da lallab'a rayuwar cikin tsanani da wahala.
In the fifth year of leaving u home Allah cikin ikonsa ya aiko mana yaron nan takanas ya zo k'asar domin neman yafiyar kuskuren daya aikata,cike da sa rai za muji k'ansa tunda yake ya gane kuskuren daya aikata yana fad'a min ba laifinsa bane rashin sani ne da jahiltar lamarin Ubangiji yasa shi aikata hakan but i hadn't listened to him,tsayin lokaci haka muka kasance he was always bound to come to my house akan magana d'aya,even if i was at home or out he was following me yana ba ni hak'uri akan laifin daya aikata,but duk da haka ban tsaya munyi wata magana ba,all of a sudden while we were sitting a bakin masallaci sai ga Alhaji Zakar da iyalinsa sun dawo k'asar,it was during this visit that Alhaji Zakar himself came to my house muka zauna da shi,a nan yayi min bayanin duk abunda ya faru ya k'ara da ba ni hak'uri,maganar gaskiya a lokacin da na san gaskiyar al'amarin na ji b'acin rai kuma na ji tsananin fushi,but da nayi tunani duk cikin abunda ya faru ni ne mai babban laifi sannan halaccin da mahaifinsa yayi muku a rayuwa na yarda nayi hak'uri,ni kaina na sani da ace tun farkon na karb'i al'amarin a matsayin k'addara da ubangiji ya sauk'ak'a min,at that moment i understood the meaning of my failure on the other side,na yi kuka na rok'i ubangiji gafarar laifin dana aikata,bayan na d'an yi fushi na sakko kamar yadda shi Rafeek ya sanar da ni ya mallakawa Hauwa'u gida,da ni da shi har ma da Alhaji Zakar da yayan ku Abdullahi haka muka yi ta yawon zuwa unguwar but we did not find u there,a wannan lokacin babu inda ba mu neme ku ba,hatta radio station,television da newspapers sai da aka buga labarin but har tsayin wani lokaci shiru babu feedback,ko da muka ga haka dole muka yi hak'uri sai dai ba mu cire tsammani da ganinku ba,and ba mu fasa sawa a taya mu rok'on Allah akan ya bayyana mana inda kuke idan har kuna raye.. But a wannan lokacin da muke ta k'ok'arin neman ku labari ya sake baza gari ganin da jama'a suke yiwa Rafeek yana zuwa gurina da yanayin mu'amalar mu has attracted the attention of those who cannot keep their mouths shut suka fara yad'a jita-jita da wasu irin maganganu marasa tushe,wanda a lokaci guda har an fara jifanmu with such a bad words wasu suna fad'an mun had'a baki mun siyar da ku to a secret organization,without asking anyone for advice ya warwarewa y'an jarida yadda al'amarin ya faru,lokacin da ya sanar da ni abunda yake faruwa though na san wasu matsalolin da muke kan fuskanta akan case d'in,hakan yasa na sake gasgata nadamar da yayi akan lallai ne wancan lokacin ko da al'amarin ya faru ba shi da ilimi akan hakan,after a long time of trying to find u out Alhaji Zakar had to send him back to his job,tun daga wannan lokacin duk wata nasara da na samu long ago wannan yaro shi ne sila,takarar da aka hana ni a baya the one i was blamed at the same time was looking for me using his wealth,his health and his time ya tsaya min na cimma muradi na,harkar campaign da every change da kuka tarar a rayuwar mu yanzun da y'an uwanku da suka rasa aikin yi a baya a dalilin abunda ya faru yayi silar da a yanzun ko wannensu yake cikin rufin asirin ubangiji.." Dakatawa Baba yayi,bayan ya ja fasali ya ci gaba,nasiha mai shiga jiki yayi musu bayan ya tabbatar jikinsu duk ya yi sanyi slowly ya furta "if we haven't forgiven him what do u think we should do.!? Ko ubangiji idan muka yi masa laifi muna da damar rok'on sa yafiya kuma ya gafarta mana,if what happened years ago a cikin zuri'ata ne zai sa ayi ta kallonsa da laifi i surely forgave him,wannan shi ne k'addarar mu,dan haka wani ko mu bamu isa canjawa ko hanawa ba,abunda duk ubangiji yaso shi yake faruwa,wannan kuma shi ne abunda ya hukunta akan mu.!"
Chapter 74 · 0% Book details