← Book details Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 152

Sashe 17

Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Kallonta nurse d'in ta dunga yi kamar taga bak'uwar halitta,can da taga ba zata iya shiru ba ta janyo kujera ta zauna tana kallon Hauwa tace
"Dan Allah kiyi hak'uri y'ar uwa idan har maganata zata sa kiji babu dad'i" da kai Hauwa ta amsa mata saboda kukan da take har a lokacin yak'i bari tayi magana,nurse d'in tace "Idan babu damuwa can we be a sister's so that sai muyi maganar a matsayin y'an uwa ba mai kula da yaro ba.!?"
Hauwa ta sake kad'a mata kai,godiya tayi mata sannan tace "dan Allah mene ne dalilin da yasa kika ce asa masa sunanki al'halin na san yana da mahaifi.!?"
Sai da tayi k'ok'arin tsayar da sababbin hawayen dake sake taho mata sannan tayiwa nurse d'in tak'aitaccen bayani akan matsalolin da suka samu wanda sune silar da suka janyo musu fad'awa mawuyacin halin da suka tsinci kansu a ciki,da ta samu ta d'an fad'awa nurse d'in,wacce lokaci d'aya taji har zuciyarta ta aminta da ita,wani irin kuka take tunda ta samu ta fitar da maganar daga ranta,burinta kenan a lokacin yadda take ciki damuwa ta samu wanda zata fitarwa da maganar ko zata huta da rad'ad'in dake addabarta,tausayin Hauwa da baby yasa nurse bata gama jin labarinsu ba sai da tayi musu hawaye,tana kallon Hauwa bayan sun gama maganar tace "kada ki damu yar uwata,in sha Allah komai mai wucewa ne,,da yardar Allah lokaci zai zo da Rafeek zai neme ku duka,a lokacin zaiji kunyar wulak'anta kyautar da Allah yayi masa,in Allah ya yarda sai Yaron da nuna baya k'auna ya zame masa jigon da bazai tab'a samun kamarsa ba a rayuwa,,fatan da zan masa shi ne Allah ya nuna masa hanyar gaskiya komai tsayin lokaci..",sun jima sosai nurse d'in tana mata hira saboda tana son rage mata damuwa,da Hauwa zata tafi nurse d'in ta fad'a mata sunanta *AAEDAA* Hauwa ta mata sallama ta koma room d'in da take,da yake duka a ward d'aya suke,tana shiga d'akin su Hajiya suna zaune tun fitarta suna hira da Maimunatu,tayi sallama suka amsa ta wuce saman gado ta kwanta tayi shiru bata sake magana da kowa ba,,bayan wani lokaci Hajiya taje ganin Yaro ta tarar da abunda Hauwa tayi,tazo tana mata fad'an me yasa zata yi haka,al'halin kowa yasan Yaro nasu ne ita da Rafeek.? Babu kunya Hauwa ta fashe da kuka but ta kasa magana,Hajiya jikinta yayi sanyi ta matso ta rarrasheta,Hauwa tayi shiru cikin sanyi da lallami Hajiya ta tambayeta ko me yasa tayi hakan.? Bata b'oye ba ta sanar da Hajiya kaf abunda ya faru a ranar da incidence d'in ya faru,Hajiya taji bak'in cikin abunda ya faru musamman sakin da Rafeek yayi,amma da yake babu yadda za tayi tunda ya riga ya yanke hukunci tace "ai shi kenan,kansa ya cuta ba ni ba,Allah ya baki lafiya daughter,kiyi hak'uri da duk abunda zai faru,in sha Allah tunda yace baya son yaron nan sai ya zama mafi k'ololuwar alkhairi a rayuwarsa,da yardar Allah zai yi nadamar abunda ya aikata a nan gaba" a zuci hauwa tace "Allah yasa"
Hajiya dake rike da ita tace "maza kwanta ki huta kinji,Allah ya k'ara muku lafiya",da Alhaji yazo duba su shima lokacin da Hajiya ta fad'a masa ya ji bak'in ciki sosai,har yaji ina ma ace yana da wani d'an namiji,da a yau ya d'aura musu aure da Hauwa ko dan ya huce takaici da kunyar da Rafeek yasa shi ji,sai dai da yake y'ay'an duka guda biyu ne Allah ya azurta su da su bayan wanda suka binne guda uku,biyu b'ari d'ayan kuma an haifeshi rayuwar ce da Allah bai nufa zaiyi mai tsayi ba shi yasa tun yana jariri ya karb'i kayansa,Alhaji ya yiwa baby khud'ba da suna *NURAZ* kamar yadda Hauwa ta zab'a,,a kullum duk wanda zai d'auke ka tunda aka yi haihuwar duk da babu wanda ya san abunda yake faruwa har lokacin,addu'ah yake Allah yasa ka kasance haske ga mahaifiyarka kamar yadda ta ambaceka,,bayan shafe kwanaki da aka rik'e ku a hospital aka sallamo ku muka dawo gida,Hajiya taci gaba da kula da ku,kullum rana tunda kuka fito daga hospital na kasance ina tafe akan hanyar gidana da gidan kakanninka ba dan komai ba sai dan na duba yaya kuke,har Allah yasa duka kuka samu lafiya,kamar yadda kullum ake sake samun ci gaba,kana girmanka da wayo,Hauwa kuma ta koma shiru ta daina hira da kowa kullum cikin keb'e kanta take daga idanun mutane.

*Ina labarin RAFEEK..!??*

B'angaren Rafeek (mahaifinka) kam tun daga wannan tafiyar da ya bar gida cikin fushi,sai ya kasance bai sake waiwayen gida ba,a waya idan an kira babu wanda yake samunsa,shima kuma baya kiran kowa,,tun ranar da Hauwa ta haihu da Hajiya ta buga waya ta fad'a masa,ya daure yace "Allah ya raya" daga haka har ta gama maganar da zata yi bai sake cewa komai ba,lokacin da suka samu labarin abunda ya faru tsakaninsu a bakin Hauwa Alhaji zakar ya kirashi yayi masa tas,shi ne ya sake jin haushin Hauwa akan ta had'a shi fad'a da mahaifansa suna ganin laifinsa,suna gama waya a lokacin gaba d'aya ya cire sim cards d'in ya canja wasu,a cewarsa tunda sun zab'i zama da ita suje suyi ta sonta,shi ya hak'ura zai zauna a nan har zuwa sanda zasu gane gaskiyar abunda yake son su fahimta.
Zamansa a k'asar bayan y'an wattani ya kama aiki da yake lokacin ya kammala karatunsa,cikin hukuncin ubangiji tunda ya fara aiki da skul d'in da yaje karatun a matsayin lecturer a b'angaren Economics,ko shekara bai kai da farawa ba world bank suka yi sanarwar neman kwararru a b'angaren Economics,da yake harka ce ta kwakwalwa kuma Alhamdulillah Rafeek yana da k'ok'ari sosai tun kafin yaji labarin wasu abokansa da suke tare a k'asar suka shawarce ko zai gwada sa'ar sa,ya tura details d'insa through mail da suka bada,bayan turawa Rafeek ya duk'ufa addu'ah ba da wasa ba,tunda ya tura yake jiran amsar su still yana ci gaba da aikinsa,a weeks later da tura details suka masa replying idan ya shiryawa special exam d'insu ya tuntub'e su duk lokacin daya samu damar shigowa k'asar,cike da farin ciki lokacin da yaga sak'on ya tattara komansa a satin ya bar k'asar bcos dama zaman k'asar ya isheshi taurin kai ne yasa shi zama,ya tura takardar ban hak'uri ga hukumar collage d'in da yake aiki ya ajiye musu aikinsu,lokacin da jirginsu yayi arriving a babban birnin *WASHINGTON* charter taxi ya samu da zai kaishi masauki,ya samu hotel mafi kusa da 1818 street ya sauka,,kwana biyu da zuwansa k'asar bayan ya huta sannan yayi shirin tunkarar world bank headquarter,daga hotel d'in daya sauka zuwa headquarter babu wani nisa sosai,duka baifi mutum ya taka da k'afa ba,,a cikin sama da mutum d'ari daga k'asashen duniya mabambanta Rafeek becomes *CONQUEROR* bayan special exam da suka yi,ya samu damar zamowa d'aya daga cikin ma'aikatan su,,yanayin gogewarsa a b'angarensa cikin tak'aitaccen lokaci da kama aiki ya zamo wani jigo a gurinsu,tunda ya fara aiki ya rik'e aikinsa da gaskiya babu wasa,ci gaban rayuwa ya kasance yana zuwa masa a kowane yini like brightening burning light,a gefe guda tunanin gida da mahaifansa kullum yana mak'ale da zuciyarsa,but a ganinsa har lokacin tunaninsa shi ne ya basu lokaci da yake ganin idan har basu nemesa ba shi zai koma musu a lokacin da zai gama duk wasu shirye² na korar Hauwa daga gidan.
Chapter 17 · 0% Book details