Sashe 6
Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read
*"RAFEEK ZAKAR LABBO* shi ne cikakke kuma asalin sunan mahaifinka,wato *CHIEF ECONOMIST* kamar yadda kaji na ambata a farko ne,sai dai kamar yadda na sani ne kuma kaima ka sani a yanzun al'ummah gaba d'aya tafi kiransa da *SUPERIOR* kuma shima wannan sunan yake amsawa,wannan suna ne da zan iya ce maka ya samo shi ne tun bayan da d'aukakar sa ta bayyanar da shi a duniyar shahararru,,asalin iyayen Rafeek ba y'an garin Kano bane,zama da yanayin canjin gurin aiki irin na ma'aikatan force ya kawo iyayensa garin Kano,Allah ya had'a mu mak'otaka da su,tun kafin su haifeshi har zuwa bayan haihuwarsa muke zaune tare da su cikin unguwa d'aya,asalisu sun kasance Fulani ne su da suka fito daga jihar *YOLA*,,Mahaifin Rafeek Alhaji Zakar Allah yayi masa rufin asiri da dukiya dai² shi wanda duk wani bawa da yake neman rufin asiri a gurin ubangiji ya samu kamar wannan a iya cewa ya more,kasancewar iyayen Rafeek tun a wancan lokacin suna da arzik'in su dai² su,mahaifinsa Alhaji Zakar ya kasance mutumin k'warai daya rik'e muk'amai da dama a cikin hukumar su ta *CUSTOMS* kafin Allah ya kaishi matsayin *ASSISTANT COMPTROLLER* a b'angaren d'amarar tasu,daga nan ne kuma bai sake yin gaba ba saboda ajiye aiki da yayi (ma'ana yayi retire).
Duk wanda ya san su yasan mutane ne su na gari masu mutunci da ake zaune da su lafiya,tun farkon zuwansu kafin a samu mahaifinka,babu wanda zai zo yau yace sun tab'a yin ko da musayar yawu,haka ko bayan haihuwar Rafeek zuwa tasowarsa babu abunda ya canja,,a d'abi'u irin na yarinta ko wane yaro zaka ga da irin abunda tunaninsa da ra'ayinsa yafi karkata akai,ko nace muradinsa da idan ya girma zai so ya zama,,a wancan zamanin lokacin da shekarun Rafeek suka yi dai² da wannan stage bayan tasowarsa cikin hukuncin ubangiji,ya kasance gwani wanda yake da burin ganin ya nemi na kansa a k'ok'arinsa na ya wadata kansa ta inda ko ya girma ba zaiyi kukan rashi ba,,sab'anin sauran yara sa'anninsa da zaka tarar dole sai sunje gida suna y'ar murya suke samun biyan buk'atunsu,,sau da yawa a wannan lokacin tun bashi da shi,da y'an kud'in makarantarsa da yake ragewa yake siyo y'an k'ananun kaya da basu fi karfin aljihunsa ba a shaguna yana siyarwa a k'ofar gidansu,yau da gobe aka ce a gurin ubangiji tafi k'arfin wasa,akan wannan hali da mahaifinka ya d'auka mutane suka fara yi masa kallon shirmen yarinta yasa shi yin hakan,yayin da shi a gare shi bil'hak'k'i ya d'auki al'amarinsa,lokaci² idan ya samu yan kud'ad'ensa ba tare da yayi shawara da kowa ba zai je ya siya yan abubuwan da suke da rangwamen kud'i,kama daga kan sweet,chewing gum,biscuit da sauransu,ba don komai ba sai dan ya tallafi kansa ta hanyar neman halal d'insa and ba tare kuma da ya jira anyi masa a gida ba,and ba dan ya rasa gata ko idan yace ayi masa a gida za'a gagara yi masa ba,sai dan yana so ne ace wata rana shima ya dogara da kansa,,,tun a farkon lokacin daya fara wannan sana'a a lokacin da jama'a suke kan yi masa dariya,sam bai d'auki hakan wani abu ba,ya maida hankali sosai wajen ci gaba da siya yana siyarwa,had'e da nunawa mutanen dake masa dariya,dariyarsu bai dame shi ba,duk da wasu a ciki sukan yi masa izgili ta hanyar tsallake shagunan unguwa zuwa gurinsa,to idan sun zo d'in ma dai mai makon su jira ya basu,su da kansu suke d'auka suna masa wasa da kayan sana'a,idan yayi magana suci gaba da dariya suna tsokanarsa da fad'in maganganu marasa dad'i,abun ya fara damunsa a rai ya fara tunanin daina sana'ar tunda ita take kawo masa wulak'anci,sai kuma yayi tunanin shin idan ya bari d'in gurin waye zai dunga samun kud'in b'atarwa da biyawa kansa k'ananun buk'atu na yau da kullum.?? Wannan tunani yayi masa jagoranci wajen yin watsi da al'amuran mutane yaci gaba da bin shawarar zuciyarsa,and ya d'ora daga inda ya tsaya,,a lokaci guda yana sana'arsa kuma yana ci gaba da karatunsa,kullum cikin ranakun markaranta da safe zaije makaranta,da yamma kuma zai zauna gurin sana'ar sa,duk da tun farkon fara wannan d'abi'a tasa mahaifansa sunyi iya yinsu akan ya bari tunda komai na rayuwa akwai a gida amma sai yace shifa sam su kyale shi yayi,to ganin ba dainawar zai yi ba yasa suma kansu suka hak'ura suka zuba masa idanu tare da binsa da fatan alkhairi,,,bayan wani lokaci da fara sana'ar tasa Allah ya sake bud'a masa,lokacin da Alhaji zakar ya fahimci da gaske yake son yin sana'ar ya bud'e masa shop a nan jikin gidan,raba d'aya nasara ta kwankwaso masa k'ofa daga zube kaya saman tabarma ya koma babban container,yayi farin ciki sosai lokacin da yayi gamo da canjin da ya samu daga ubangiji,,akan haka rayuwarsa ta fara kullum cikin samun bud'i daga ubangiji akan harkar kasuwancin sa."
Dan kallon Nuraz Annie tayi da yake ta kallonta tace "wannan duka ina tsakuro maka labarin abunda ya riga ya faru ne a tak'aice,kafin mu gangara kan asalin alak'ar data had'a mahaifanka. "
A hankali gyad'a mata kai alamun ya gane,Annie taci gaba
"Asalin alak'ar mu da juna,,,mun kasance tsakaninmu da mahaifinka neighbours ne mu kamar yadda na fad'a tun farko,mun taso cikin unguwa d'aya a cikin line guda,gidajen mu basu da wani nisa tsakani,hasalima sun kasance suna kallon juna,but mun samu bambancin tsagi,ina nufin mu muna wannan gefen suma gidan su mahaifinka suna d'ayan hannun,kasancewar mu a haka na tsayin shekaru yasa babu yadda za'ayi ace bamu san juna ba,duk wanda yake cikin line mu ko da jiya ya zo mun san juna mu da shi,mun kasance mu da kowane gida kamar y'an uwan juna.
Gidan mu a gaba d'aya line ya kasance shi ne gidana farko da yafi kowanne tara mutane,bisa wannan dalilin yasa a kullum ba'a rabo da yin fad'a da y'an gidanmu,saboda yawanmu da jaye²n fad'a irin namu yasa muka yi fice a unguwar,dalili yawanmu kuwa shi ne babanmu yayi aure²,wannan yasa adadin y'ay'ansa muka kai ashirin maza da mata,to kuma dai da yake ba'a samu macen data zauna ba a cikin matan daya aura sai mahaifiyarmu,wacce ta zauna tare da shi tsayin lokacin har Allah ya karb'i rayuwar ta tana gidan,bayan mutuwarta sai wata bazawara daya sake aura,idan aka cire wad'annan matan biyu a tarihin gidan mu da aure²n babanmu sune kad'ai matan da suka zauna sama da shekara guda,duk wacce ta zo bata wuce haka,,sannan a yadda muke rayuwa gidan mu ya kasance yana da matsaloli,amma abu na farko daya nakasa gidanmu shi ne rashin had'in kai sai rashin wadataccen muhalli,wannan sune suka bawa gidan tallafin da kullum a kowace safiya yake kamar gidan haya,da zaran gari ya waye za'a fara hayaniya da fad'ace-fad'ace wannan ya tsokani wancan,kullum haka ake yini abu guda,idan har kaji baki ya huta tofa sai dai idan dare ne ya zagayo kowa ya kwanta hak'ark'arinsa,a nan d'inma gurin kwanciyar bawai ina nufin za'a yi shi lafiya bane,dole sai an yada hali kafin baccin,wani lokaci idan ta d'auro cikin baccin ma sai an daki juna,,rayuwar gidanmu ta kasance rayuwa ce ake yinta kowa yana ganin hanjin kowa,zaman lafiya yayi mana k'aranci,kowa tak'amarsa shi kad'ai Babarsa ta haifa,kasancewar duk matan da suka shigo daga haihuwa d'aya ne zaman yake k'in dad'i wata ma bata haihuwar sai kaga an tafi,tafiyar da babu biko bare kome,,kowa shi kad'ai ne bashi da d'an uwa duka a cikin gidan,idan aka cire mu ni da mahaifiyarka da muka kasance ciki d'aya kuma baba d'aya,komai namu mun kasance tare muke yinsa tun tasowar mu duk da tsakani na da ita akwai nisan shekaru biyar (5),bata tab'a raina ni ba,tana bani girma na a matsayin yayarta,yadda ta d'auke ni take girmama ni a matsayina na y'ar uwarta da muka fito ciki d'aya,yana b'atawa sauran y'an uwanmu rai,a ganinsu ta yaya zamu kasance masu had'in kai al'halin duka gidan kawuna suna a rarrabe.? And duk wanda zai neme mu da fad'a bama kulawa daga ni har Hauwa,wannan hali ne wanda mahaifiyarmu ta d'ora mu akai,duk abunda zasu ce idan zasu kwana suna magana bama tanka musu,,kafin Allah ya yiwa mahaifiyarmu rasuwa tayi iya kokarin da zata iya na ganin ta had'a kawunanmu gaba d'aya,ganin lamarin ya gagareta ta hak'ura ta zubawa sarautar Allah ido,Innar mu mace ce mai hak'uri da kauda kai,ta rasu lokacin Hauwa tana da shekaru uku a duniya,,to da yake a gidanmu bamu samu wadataccen muhalli ba,kasancewar duka d'akuna guda hud'u ne,babanmu d'akinsa daban,matar babanmu ma haka,sai ya zama mu mata gaba d'aya muna d'aki guda,sauran d'akin kuma na y'an uwanmu ne maza,,a duka tashinmu halin babanmu guda biyu yake burgeni kuma nake matuk'ar so,duk da nasan da yawa mutane sukan yi mamaki da wannan halin nasa,amma agare mu ba abun mamaki bane,duk da kasancewar muna da yawa a gidanmu hakan ko kad'an baisa ya gagara ciyar damu ba,a kullum rana yadda ake d'ora tukunya a sauke sau uku a ko wane gida da suke jin suna da rufin asiri,muma haka nan ake yinsa a gidanmu,safe,rana da dare duk lokacin da mutum ya b'ukaci abinci zai same shi,,amma batun girmamawa ga juna ko soyayya irin ta y'an uwantaka wannan ne babu shi,haka ko a b'angaren karatu ma dai² gwargwado baba yana iyakar k'ok'arin sa wajen ganin mun wadata da ilimi,sai dai mu d'in a wannan fannin ba kowa ne hankalinsa ke kan karatun ba,duk wanda aka ce yau mahaifiyarsa bata cikin gidan mahaifinsa dole ne rayuwarsa ta samu nakasa dole ne kuma kaga bambanci da ratuwar wanda yake tare da tasa mahaifiyar,mahaifiya ita ce tushen tarbiyya ga ko wane d'a,shin mu da bamu da iyaye wane ne zai ce muyi ko mu bari.? Duk wacce baba zai auro wani lokaci sharrin yau da gobe ke sawa ya rabu da ita,dan har ga Allah babanmu mutum ne da yake da saurin yarda da magana,sannan duk duniya idan har kana son ganin b'acin ransa ka tab'a masa y'ay'a,a wannan lokacin na tabbatar duk yadda kuke da shi lallai za kuyi hannun riga,,ganin abunda muke so shi muke yi yasa itama matar gidan da aka auro take zaune da mu bata tab'a hana mu,idan ana hayaniya bata tab'a cewa mu bari,hasalima sai dai ta kad'e zaninta tayi wucewarta d'aki ta barmu nan,idan muna iyawa mu kashe juna ko mu hak'ura wannan duka ruwanmu ne,wad'annan dalilan yasa gaba d'aya kowa abunda ransa ya so yake yi,makaranta zuwanta sai wanda yaga dama ko yasa kansa,duk safiya baba zai sa mu shirya mu fita saboda yana ganin hakan shine babban gatan da zai mana a rayuwa,zuwa kuma ya rage na mai niyya,iidan ka ji baka iyawa kana fita daga gida zaka iya wucewa gararinka,idan ka daidaici lokacin tashi ka biyo ayari a dawo tare,,ruwanka ne kuma rayuwarka ce.