← Book details Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 152

Sashe 32

Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A zafafe tace "Ka saita kanka kada ka sake ka yi min rashin kunya" yayi murmushi mai sauti yace "Ba haka bane Hajiya,,rashin kunya sam ba tarbiyya ta bace" tayi tsaki tace "shi yasa naga ai ka iya gaida na gaba da kai.!"

Ya sake yin murmushi kafin yace "Ohh.! Sorry² na zo gidanki twice ban gaishe ki ba ko.!? I'm really² sorry,but na manta ne ban fad'a miki ba,ba wannan ya kawo ni ba."

Ta kalle shi tayi k'wafa,yaci gaba da magana "Hajiya yau ba wajenki muka zo ba" da sauri tace "Wajen waye kuka zo.!?" ya kalli Nusrah sannan yace "Wajen mai gidan muka zo,Allah yasa za ki bari mu ganshi kafin mu wuce",ta kalleshi ta kalli Nusrah kafin tayi magana suka jiyo murya daga side d'in staircase ana cewa "Ga ni ai,mene ne ake nema na nayi.!?" Duka suka juya suka kalli wajen da mutumin yake tahowa,Nusrah ta k'ura masa ido tana kallonsa hawaye suna ci gaba da bin fuskarta har ya k'araso inda suke,ta sake sunkuyar da kai k'asa tana jin k'irjinta na tsananta bugawa.....

#Share pls.
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©®2020.*      

                   *'DAN MACE..*
              (Tʜᴇ ᴘꜱʏᴄʜɪᴀᴛʀɪꜱᴛ)..💥

*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*    
https://my.w.tt/29u2S26SG2

Pᴀɢᴇ 16.
#Exᴘᴇʟ

      Muryar Nuraz ta jiyo yana gaida Abba'nta,ya amsa kadaran kadaham,not minded da yadda ya amsa masa Nuraz yace
    "Alhaji ina fata an sanar da kai zuwanmu na farko.!?"

   Abba'n Nusrah ya tab'e baki yace "An fad'a min something happened,but am i going to do something for u!!?"

     Nuraz yana jinjina al'amarin a ransa ya daure yace "No.! But Alh.. How do u take the matter.!?"

    Abba'n Nusrah yana kallonsa da wani irin yanayi yace "I don't understand how i have taken the matter.!?"

      Nuraz yace "I mean bayan ka samu labari ur daughter was found.. Ain't u happy.!?"

    Ya juya ya kalli hamshak'iyar Hajiyar tasa dake gefe ya kalli Nusrah,before ya maida hankalinsa kan Nuraz yace "What joy would a father have after his daughter had humiliated him.!? Yarinyar da ta sa k'afa ta fice tsayin wattani biyar ba ta gida,uban daya haifeta bai san ina ta shiga ba,bata tab'a waiwayar gida ba sai yau.. In ur own speculation nake so ka fad'a min,every woman who has been leave their home for a period of time,and u know she's not married,ba kuma ziyara taje gidan yan uwa ba,she has escaped from her home and her destination is unknown,,Then one day sai aka ce maka ta dawo,tsakanin ka da Allah what kind of name community will they call.!?"
   Nuraz yayi shiru bai amsa ba yana ta kallon mutumin da tsantsar mamaki,Abba'nta ya ci gaba "so i've already decided idan har ni na haifi Nusrah,daga yau na hak'ura da ita a matsayin y'a,thank God i was not alone,da tuni ciwon zuciya ya kama ni"
    Nusrah tayi saurin kallon Abba'nta tana hawaye but she could not have any confidence of saying a single word,slowly tayi descending daga saman armchair tayi collapsed on to the ground,Nuraz yana kallonta sympathetically ya juya ya kalli mahaifinta yace "But Alh i think u know the best of ur daughter's character,,u should not make decisions without investigation,don't ever use what people say's.. Sure sharri suka yi mata,u have to study it carefully,,but now tunda ka yi furucin ka hak'ura da ita i'll go back with her,whenever wants ur daughter come back to u,u can contact us.."

    Ya girgiza kai "I will never be able to track what already happened."

     Nuraz ya kalleshi yace "Of course if u investigate definitely u will find the truth,and u will make sure ur daughter doesn't do what u are talking about,,u know her best,if she does and if she doesn't,u all know by ur self.."

      Hajiya ta taso a harzuk'e "To yace baya buk'atarta shin dole ne sai ya dawo da ita gidan nan.!? Ta bayyana cewa itan fasik'a ce,and we said we removed it from our house.!? Malam ka ga tun da wuri ku tattara ku fita mana a gida,mun yafewa duniya ita,idan ka ji baka iya rik'onta kaima daka d'aukawa kanka wahala kana iya sallamarta tayi gaba,duniya da fad'i duk inda take so zata iya zuwa ta rayu.."
    The pain is in his eyes yake ci gaba da kallonta,tsabar k'uncin da yake ciki a lokacin jinsa yake kamar bai da rai,har ta dasa aya bai iya yayi magana ba,wani irin numfashi yake fitarwa wanda shi kansa ya san tabbas da ace matar nan ba matar aure bace yau da babu abunda zaisa bai koya mata hankali ba,yana can duniyar tunanin abunda zai mata ya huce haushi yaji tana gunguni da fad'in "Wa ya sani ma ko garin yawon ta kwaso wani mugun ciwon shi yasa ta lallab'a ta dawo gida,shi kenan bamu sani ba tazo d'aya bayan d'aya ta goga mana.! Na tabbatar ruwa baya tsami banza,dole akwai sharrin data k'ullo shi yasa ta dawo.. An yi gadon bak'in hali.."
       Yana kallonta with his colored eyes yace "Hajiya kiji tsoron Allah,,sannan ki tuna akwai ranar lahira..  What will u gain idan kin raba y'a da mahaifi.!? Is it not fun to be born.!? Ko kuma dai ba'a haihuwar d'a a nuna masa so mahaifanki suka haifeki suka so ki.!? What will u gain idan kin mata sharri gurin mahaifinta ya raba ta da gidansa.!? Kina zaton ubangiji zai kyaleki bisa hak'k'in wad'annan bayin nasa.!? What good is it to a person who says polytheism (SHIRKA) is his job.!? Don't ever think of all what u have done will be saved from his judgment,today or tomorrow,now or in the future duka sai mun je gare shi,bcos we are always like those who go to summer,we all have one God who is there waiting for our arriving,duka za mu mutu,we all find our works,and we all reap what we sow with our own hands,,but ina sake tabbatar miki idan baki ji tsoron Allah kin daina abunda kike yi ba ki tabbata ubangiji ma ba zai kyale ki ba.."
     Kallonsa tayi tana girgiza kai cike da hayaniya tace "Kaiii! K'aramin mara kunya,kada ka fad'amin maganar banza,waye ya fad'a maka ni na raba su.!? Thought shi ya fad'a da bakinsa cewar ya zare ta a gidansa.!? ga shi nan tsaye a gaban ku u can ask him who suggested him to get rid of her.!?"

      Bai jira jin wani cikinsu ya sake magana ba Alh yace "Ni naga damar cire ta daga jikina babu ruwan Hajiya,saboda haka idan iya wannan maganar ta kawo ku,heard my words,,,wish u could go and leave my house.."

    Nuraz ya kalleshi takaici fal ransa yace "Alh ya kamata kayi tunani dai gudun wata rana kada ka zo kana nadamar abunda ka aikata.!"

    Abba'n Nusrah yayi saurin katse shi "There is no thought to waste my time on it,it is a final decision banga dalilin da zaisa nayi nadama ba kuma."
    Nuraz ya gyad'a kai cike da damuwa yace "Shi kenan Allah ya ba mu tsayin rai,,in sha Allah one day u most have to regret what u've done,i assure u.!"

     Hajiya ta sake hayayyak'o masa "Wannan ranar ba zai tab'a zuwa ba"

     Ya banka mata harara yace "Idan ke kike juya duniyar ko ikon a hannunki yake sai ki hanasa faruwa"

    Ta juya ta kalli mijinta cikin b'acin rai "Wai Alh haka zaka tsaya kana kallonsa yana fad'awa mutane magana.!?"

     Ya girgiza kai yace "Rabu da ni da shi,ya gama rashin kunyar ina saurarensa" tace "wane irin kana saurarensa,baza ka sa ayi maganin sa ba,sai kace a rabu da shi.!? Idan kai ba zaka iya ba to ni zan yi da kaina.."
    Tana fad'a ta fizgo telephone dake gefe kamar shi yayi mata laifin za ta fara kiran security,,Nuraz cikin b'acin rai ya kama wayar ya tsinke,ta d'ago a fusace zata mareshi ya rik'e hannun idanunsa da b'acin rai yace "don't ever think u beach will slap my face,and kiyi tunanin zan kyaleki.. Ba aure kike tak'ama da shi ba ko tattabara kike,wollahi sai na sa kun gane cewa a tea is just a water sinadaran da aka sa masa su suka canza masa colour.. Ki yi tunanin me zai faru first kafin kiyi k'ok'arin aikatawa.." Yana fad'a ya watsar da hannayenta gefe

     Alh yace "Kai d'an marasa tarbiyya..!"

    Bai k'arasa ba yace "Stop.! Alh ina ganin girmanka bcos of ur daughter,ba don haka ba..!"
      Ya girgiza kai ba tare da ya k'arasa ba,ya juya yana kallon Nusrah dake ta risgar kuka duk badak'alar da ake yi ta kasa cewa komai a tsawace yace "get up",sai kuma ya juya yana kallon Alh yace "Ohh.! Alh i've one wish ko za ka yi mana abunda zan fad'a.!?"

    Alh ya kalle shi a wani iri yace "What.!!?"

    Bai damu ba yace "Just.! I want ur permission to pick up her school documents.."

       Ya tab'e baki yace ku jira a waje zan aiko muku."
    Nuraz yayi tak'aitaccen murmushi yace "Good" sannan ya sake juyawa inda take ya mik'a mata hannu "Get up,,let's wait outside.."
       Ta d'ago kumburarrun idanunta ta kalle shi,shi kansa fuskarsa tayi wani iri,ko ita data kalle shi sai da idanunsa suka so bata tsoro,ta daure ta mik'a masa hannu ya taimaka ya mik'ar da ita tsaye,yana rik'e da ita ya kalli Hajiya yace "Za mu tafi,but in sha Allah kamar yadda na fad'a zaki ga sakamakon abunda kika aikata.."

      Tace "Idan na gani ina fata ba tare da kai za mu gani ba.!?"

       Yace "Sure" tayi tsaki zata sake magana Alh ya sakko da takardu a hannunsa,ganinsu suna ci gaba da musayar zance yayi tsaki ya mik'a masa takardun yace "Allah ya bamu alkhairi." Yana nuna masa k'ofar fita
Chapter 32 · 0% Book details