← Book details Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 152

Sashe 40

Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Yayi murmushi kad'an yace "Taimakon farko da nake bawa majinyanta na,a duk lokacin da aka cemin Nuraz kai zaka kula da wannan patient d'in na kan yi k'ok'arin jansu a jiki mu saba da su sosai,ta yadda idan na zo aiki ba zan sha wahala ba,saboda sometimes za ki ga wasu likitocin namu saboda rashin sabo tsakaninsu da patients kana k'ok'arin bawa mutum kulawa,wannan rashin samar da alak'ar sai yasa k'arshe a samu matsala ko su rufe mutum da duka,idan aka yi rashin sa'a masu duka ne ko su kwaci makami suji maka ciwo saboda su tunaninsu ya jirkita ya zama daban da namu,so dole dai kafin ka tunkare su kai tsaye akwai buk'atar shak'uwa a tsakanin kai da su,after then zaka bada lokacin ka,da duk wata kulawar da zata taimakawa majiyancin.."

"Good Dr,kenan dai kana son cewa kafin likitoci irin ka,su tunkari majinyaci musamman b'angaren ku yana da kyau su fara samar da alak'a mai k'arfi tsakaninsu da patients d'insu ta yadda ba zasu damu ba a lokacin da ake duba su.!?"

Yace "Haka ne.",Jennet tace "Da fatan likitoci a b'angaren halayyar d'an adam suna tare da mu,kuma sun ji abunda Dr Nuraz ya fad'a,,but Dr bari mu koma baya kad'an cikin tarihin ka,a baya munji ka ce big mom d'inka ta kaika makaranta,and ka ce saboda mahaifiyarka ka zab'i wannan b'angaren,shin mahaifanka suna nan a raye ne ko kuwa mutuwa suka yi a lokacin,sannan mene dalilin duk da ka ce mahaifiyarka ce.!?"
Sai da yayi taking deep breathe kafin ya d'ago idanunsa da suka fara sauyawa ya furta "Suna nan a raye" Jennet ta kalleshi tana murmushi tace "Masu sauraro da ni za mu so jin su wane ne mahaifan DR NURAZ,and yaya ne ka yi rayuwa da family'n ka a tak'aice."

Ya lumshe ido ya bud'e yayi ajiyar zuciya mai nauyi yace "Mahaifana ba wasu bane,sannan na kasance ni kad'ai ne a gurin mahaifana,na taso a rayuwata ba ni da elder brother ko wasu little siblings,na rayu a wajen Big mom d'ina,duk da a cikin gidan mu bamu kasance da wani relatives namu ba,mun rayu mu kad'ai big mom d'ina da maidservant,sai Mommy na though she was unconscious bayan ta haife ni,sai kuma ni kai na kenan,dalilin da yasa na zab'i zama psychiatrist kamar yadda na fad'a a bayan saboda Mommy na ne,,sanadinta na zab'i wannan field d'in.."
A hankali cikin sanyayyar muryarsa ya fara finding out irin rayuwar da suka yi tun kafin a haifeshi,irin wahalhalun da suka sha kafin ya zo wannan matakin har ya dire a k'arshen,but abu guda ne bai yarda ya fad'a ba,sunan mahaifinsa though Jennet ta so ya fad'a,ya tsaya a nan yace "Idan har lokacin sanin ko wane ne mahaifinsa yayi zai bayyanawa duniya,though ya san ba b'oyayye bane,sunan sa kad'ai idan ya fad'a gaba d'aya duniya zata girgiza,but shi har yanzun yana doubting ne akansa,anya ya cancanta ya zama uba.!? Mahaifiyarsa ita ce komai nasa a rayuwa,,dan haka yana so al'ummar duniya su shaida hakan,kamar yadda mutumin da yayi ik'irarin shi ba mahaifinsa bane,shima ba yau zai fad'awa duniya shi d'ansa bane,saboda haka zai ci gaba da amsa sunansa na *'DAN MACE..* Kamar yadda society da k'abilar malam bahaushe take kiransa da shi.."
Yadda tattaunawar ta kasance zuwa bayyanar tarihin sa yasa al'ummah da dama kuka,Rafeek na zaune ya k'afe screen na cinema da ido yana hawaye da wani irin nadamar abunda ya aikata a zuciyarsa,he feels that time where running back,surely da there is nothing will stop him from turning it first,a hankali yayi descending daga saman chair yayi collapsed on to the ground,bakinsa na wani irin karkarwa yake fad'in "Astagfirullah wa'atubu ilaik.. Allah na tuba,na san ni bawanka ne mai tsananin taurin kai,na wulak'anta kyautar da kayi min a lokacin da ya kamata ace na nuna godiya ta gare ka,na tozartar da su,ya Allah ka dubi halin da nake ciki ba don hali na ba ka dawo min da su cikin rayuwata.."
A cikin wannan mawuyacin halin da yake ciki Clark ya shigo masa da report d'in binciken daya sa shi yayi masa ya riskeshi hankalinsa a tashe,ganin uban gidansa na kuka babu ji ya kira Hajiya ya sanar da ita,ita kanta hankalinta a tashe ta zo apartment d'in ta tarar da shi durk'ushe a k'asa hawaye wasu suna bin wasu a fuskarsa,idanunta sun yi wani iri saboda tausayinsa ta rik'o shi tana tambayarsa "RAFEEK kanka d'aya ka ke neman mayarwa da kanka bara ta za dawo bana.!?"
Jin muryar mahaifiyarsa yasa ya d'ago jajayen idanunsa da sauri ya kalleta yana girgiza kai,muryarsa sai rawa take da kyar yace "Hajiya ina jin tsoron abunda zai faru da ni gaba,tun a baya kunyi k'ok'arin fahimtar da ni abunda zai iya faruwa amma a lokacin sai nak'i saurarenku,na watsa muku k'asa a ido,bayan na butulcewa mahalicci na ta hanyar nuna masa kyautar da ya bani ba komai bace face k'azantacciya,al'halin ni nayi silar samar da ita ta tsarkakakkiyar hanya,,Hajiya da wane idon zan kalli d'an dana wulak'anta.!? Da wane idon zan kalli mahaifiyarsa.!? Na wulak'anta su,na tozarta su,duk da haka ban tsaya a nan ba,sai dana tozarta su a idon duniya,na yi sanadin da mahaifinta ya koreta,Hajiya me zance da ubangiji a lokacin da na ganni a gabansa.?? Me zan fad'a na wanke kaina saboda hak'k'in dana d'aukarwa kaina.!? Ina dana sani a rayuwata,ba zan tab'a daina yin nadamar abunda na aikata ba har zuwa numfashi na na k'arshe.." Hawaye ne ya gangaro mata tana rik'e dashi a jikinta,ta rungume shi tana fad'in
"Yi shiru haka nan,in sha Allah za su yafe maka,kai dai kayi k'ok'arin neman yafiyarsu,ta wannan hanyar ne kad'ai zaka samu sassauci.."

"Ba zasu yafe min ba Hajiya,na cutar da rayuwarsu da yawa,ba zasu yafe min ba.. Na sani hakan ba zai tab'a kasancewa ba"
Girgiza kai tayi ta d'ago fuskarsa ta masa whipping tears tace "in sha Allah za suyi hak'uri su yafe maka" ya girgiza kai da sauri wasu hawayen suna sauko masa zai yi magana Hajiya tayi saurin taron numfashinsa "Kada kace komai,kaci gaba da addu'ah in sha Allah babu abunda yafi k'arfin ubangiji.."
Ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi,ya sake kwanciya a jikinta yana maimaita "Astagfirullah..! Astagfirullah wa'atubu ilaiik.!"
A hankali ya lumshe idanunsa yana jin wani irin yanayi a jikinsa,Hajiya tana shafa kansa sai data tabbatar ya fara samun nutsuwa sannan ta barshi ta wuce nata apartment d'in.
Chapter 40 · 0% Book details