← Book details Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 152

Sashe 47

Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Tana shigowa gida ta wuce ta nufi hanyar bedroom ko kula da su Annie bata yi ba,suna kallonta ta wuce bata yi magana ba da alamun kamar ba ta cikin hayyacinta,Lolly was strong enough to call her "Angel.!" A tsorace ta juyo tana kallonsu tana raba idanu she didn't expect to find them here,da hannu ta yafito ta cikin mutuwar gab'b'ai ta fara dawowa,Annie ta zuba mata ido tana kallonta har ta k'araso cikin parlor'n tana had'iye wasu irin terrified saliva's saboda bata san amsar da zata basu ba idan suka sako ta a gaba da tambaya,lolly ta kama hannunta ta zaunar da ita kusa da ita,kallo d'aya Annie tayi mata tace "Daughter what's going on.!?" Taji tambayar har tsakiyar kanta,a firgice tayi k'asa da kanta tana kame²,muryarta a raunane tace "Nothing Annie" sun zuba mata ido as each of them wanted to find out where the problem was,Lolly ta shafa kanta cikin salon bata kariya tace "Ko duk gajiyar skul ne baby.!?" Da sauri ta girgiza kai bakinta cike da in'ina tace "Hhhh.. Ha..ka ne Aunty",murmushi kad'an tayi mata tace "sannu baby,karatu akwai wahala,sai dai ki sake dagewa,in sha Allah nasara tana tare da ke" Bareerah dake neman gurin zama tace "In sha Allah",Annie kam ta kasa magana sai kallonta take,cos ta gama fahimtar tana cikin damuwa mai tsanani,har ta mik'e ta fara tafiya da lolly tace taje ta huta duk dan kada su takura mata,Annie tace "Daughter.!" Ta k'ame a inda take ta kasa yin gaba,Annie tace "No matter the stress is,misery or anxieties that u are going to,never forget Allah,and take ur cry to him,he will always listening and wait for ur du'a to wipe out ur tears,all the pain is with ease (Fa'innama'al usru yusra) In sha Allah he will protect us,,but one thing i want to remind u is,that anxiety and many thoughts are nothing but trouble and self-destruction.."
Jikinta ya sake yin sanyi taji wasu irin hawaye sun fara gangaro mata a hankali,tuna yadda suka yi da Aatif yanzun babu jimawa yasa bata san lokacin da kuka ya kwace mata ba,ta zubar da komai dake hanunta ta durk'ushe a gurin,hankalin Annie da lolly a tashe suka nufo ta kowanne burinsa yaji matsalarta,ta kwanta a jikin Annie tana kuka,rarrashinta ta ci gaba da yi until her mind came back to her,babu wanda ya takura mata lallai sai ta fad'a musu damuwar,but nasihar da Annie ta ci gaba da yi ta sake sanyaya mata jiki,a hankali kamar wacce aka matsa bakinta tana sakin ajiyar zuciya tace "Annie.!" Suka yi shiru duka suna kallonta,ta dago a hankali tace "For example it is said that a man says he loves a girl,and his mother does not approve the girl.. How should she do.!?" Suka kalli juna kafin Annie tayi magana Bareerah ta tari numfashin Nusrah "Tabbb'! Wannan ai babu amfanin b'atawa kai lokaci ma,idan har na tabbatar mahaifiyarsa bata k'aunata ni kuwa wane tsautsayi zaisa na kai kaina gidan d'anta.!?"
Nusrah tana kallonta with her pale eyes tace "But u know he loves u,and u just make sure u love him,kawai saboda mahaifiyarsa sai kice kin hak'ura.!?"
Bareerah tace "Of course i will,no matter how long we have spent together,duk son da muke yiwa juna tabbas zan ce masa na hak'ura,Allah ya had'a kowa da rabonsa na alkhairi"
Nusrah tayi kasak'e tana kallon yadda Bareerah ke rairayo bayani tayi tagumi har ta dasa aya,tayi ajiyar zuciya a hankali tace "So what is ur fact da kika ce u can bear.??" Bareerah ta gyara zama tace "Na farko dai shi kansa auren dan me ake yinsa.!? In order to get calmness,to have peace of mind and happiness ko.!?" Nusrah ta gyad'a kai tace "Haka ne" Bareerah tace "Toh ni da mother in-law d'ina bata k'aunata how can i get all this.!? A tunani na da kuma nawa ra'ayin tunda har ta furta bata so na kinga duk wad'ancan abubuwan dana lissafa bazan tab'a samun su ba,to kinga kenan babu amfanin nayi auren ko ba haka ba.!?" Nusrah ta gyad'a kai,Bareerah tace "and if my mother-in-law didn't love me abunda zai faru shi ne duka y'an uwansa would not like me,kinga kenan a gurinsa kad'ai nake da mutunci,and it shows that zuga da k'iyayyarsu zai yi tasiri har ya zama mun rabu,one day he will despite the love we have built since the beginning of our relationship" tayi shiru tana tunani kafin ta sake furta "To kuma bayan kin san mahaifiyarsa bata sonki,da kansa ya tabbatar miki ta k'i amincewa kuyi aure,sai ya zo miki da maganar kuyi secret marriage yaya za kiyi.!?" A tare su duka ukun suka furta "What.!?" She stared at them as they were doing,Bareerah tayi k'arfin hali tace "This is a great mistake which if i finally trust zan zo ina dana sani" ta sake yin shiru tana tunanin maganar Bareerah "To amma ai kuna son juna fa" Bareerah tayi tsaki tace "Son banza son wofi,da yawan lokaci wannan kalmar so d'in ita ce take rud'a mu mata,but u're still a girl but surely next time u will understand what i mean to u,idan lokaci yayi ko shawara ba sai kin tsaya tambaya ba za ki yanke hukunci a take" ta gyad'a kai a hankali bata sake yin magana ba tun daga nan,Annie ta zuba mata ido na wani lokaci kafin tayi magana "Daughter who's the boy!?" Tayi saurin kallonta,lolly ta shafa kanta tace "fad'a mana wane ne.!?" Kamar wacce kwai ya fashewa a ciki ta furta "Aatif sunan sa" Annie tace "Yaya kuka yi da shi.!?" Kaf duk yadda suka yi sai data fad'a musu,Annie tayi ajiyar numfashi tace "Daughter tun farko kika yi KUSKURE da kika nuna masa so irin haka,baki san d'a nimiji ba and u don't know their side effects,but ban ce miki duka suka zama d'aya ba,kamar yadda muma a cikin mu ba'a rasa b'ata gari,amma had'arin su abun gudu ne,duk yadda kike da shi and all ur love for him at the same time it can change especially bcos his mother data nuna bata gamsu da auren ku ba,a matsayin y'a muka d'auke ki mu duka shi yasa nake fad'a miki,if u are unhappy with ur marriage,muma duk baza muyi farin ciki ba,duk d'a namijin da zai zo miki da maganar aure matuk'ar ya sanar dake mahaifiyarsa bata sonki ki hak'ura da shi ki ci gaba da addu'ah in sha Allah canjin alkhairi yana nan zuwa" tayi shiru tana sauraren nasihar Annie,bayan tsayin lokaci ta numfasa tace "In sha Allah Annie i will do as u say" tace "O daughter God bless u,and may he changed it with good one" ta amsa a sanyaye,umarni lolly ta bata to go to rest saboda yadda tayi shiru tana tunane²,and she should not think of anything to worry about,ita taga sharrin tunani,dan haka her story is a great example for her,tace "in sha Allah Aunty this would never happened again.!"
Chapter 47 · 0% Book details