← Book details Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 152

Sashe 61

Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Kamar yadda Maimunatu ta fad'awa Annie,ranar kwana uku da dawowarsu gida ta mata waya,tun kafin su gama shiryawa sai ga shi an turo mota da driver har gida,suka fito ita da Nusrah cikin shirin fita,lolly da Bareerah suna parlor a zaune suna hira suka yi musu sallama,su kuma suka bisu da fatan dawowa lafiya,Annie ta kalli yadda lolly ke yi da fuska but bata kula ta ba,she knew she was sad when she asked her who was sick tak'i fad'a mata,tayi murmushi dai a ranta tace "Koma waye babu lafiya idan na fad'a miki ba amfani zai yi ba,tunda ba zuwa za kiyi duba shi ba mene ne na tambaya.!?" Suka fita inda driver yake jiransu,tun da suka d'auki hanya har suka shiga arean da mansion d'in yake mamaki duk ya cika su,Annie tayi ta jinjina lamarin a ranta even though she has been hearing about Rafeek for a while but not knowing anything about his exalt,kada kuso ganin k'auyanci lokacin da suka tsaya bakin apartment d'insa,bcos duk inda tunanin su da hangensu yaje sun duba k'ofar shiga amma sama ko k'asa sun rasa,baturen dake tsaye a gurin ya tambayi sunan su,Annie ta kalli Nusrah tace "Yau na ji gulma,shi kuma wannan mai zai yi da sunan mu.!?" Nusrah ta kyalkyale da dariya tace "Shi ya sani" juyin duniya yayi da su su fad'a Annie tace da ta fad'a masa gara su shekara a nan,idan sun gaji su koma inda suka fito,bature ya koma gefe ya k'ame kamar dodon gona,suka yi tsaye they were in the house but could not figure out where the door was,sun kusa mintuna ashirin a guri d'aya kafin ta kira Maimunatu a waya ta sanar mata suna cikin gidan tun d'azun,Maimunatu tace su d'an jira ta tana fitowa yanzun,bayan kamar mintuna biyu suka ga ta fito,daga Annie har Nusrah cikin mamakin wannan lamari suka bi Maimunatu da kallo har ta k'araso inda suke,fuskarta a sake ta musu barka da zuwa,tana amsa gaisuwar Nusrah ta kalli Annie tace "Adda maryam is this our baby.!?" (Kuji dai in banda d'aukewar tunani,did Maimunatu forget since before they were left 9ja Annie's husband died) Annie ta kalli Nusrah da ta sunkuyar da kai tana murmushi tace "Ehh y'ar kuce" Nusrah tayi saurin kallon Annie kamar za tayi magana sai kuma tayi shiru,Maimunatu ta kalleta tana jinjina kai tace "Masha Allah,ai ga kama nan ta d'auko" Annie tayi saurin kallon Maimunatu tace "kamar waye ta d'auko.!?" Maimunatu tayi murmushi tace "Ta y'ar uwata Hauwa'u,but baby instead u look like i sai kika d'auko ta y'ar uwata.!?" Annie stared at Nusrah for the first time and wanted to find out what people were saying to her,ita dai tunda Allah ya had'a su da Nusrah take zaune a gurinsu abokan kasuwancin su suke yawan fad'a mata suna kama da yarinyar kasancewar da ita Annie da Lolly suna d'iban kama sosai sai dai lolly ta d'an fi Annie haske,and Bareerah has been telling her this for a long time itan ce dai bata yarda ba,a fili bayan wani lokaci ta furta "ikon Allah" duka suka kalleta Maimunatu tayi murmushi saboda bata gane abunda Annie take magana akansa ba,tana kallon Nusrah tace "what's ur name baby.!?" Nusrah tana sunkuyar da kai k'asa tace "Nusrah" ta jinjina kai tace "Masha Allah,,ya karatu fa.!? Na san dai kina yi" tace "Alhamdulillah" dai² lokacin da suka tsaya bakin entrance,Maimunatu tayi y'an danne² tana jan su da hira,they didn't take a moment tayi enrolling sunan su,kamar daga sama suka ji k'ofar tana mentioning sunayensu and welcoming nasu,suka d'aga kai a tare suka kalli juna,Maimunatu ce a kan gaba suna binta har suka shiga cikin apartment d'in daya kusa gigita tunanin su,dukiyar da aka zuba kad'ai ya zame musu abun kallo,suna ta tafiya su wuce wannan parlor su shiga wannan har suka k'arasa bedroom d'insa inda suka tarar da Hajiya,tana ganinsu ta saki fuska tayi musu maraba cikin mutunci,Annie da Nusrah suka zauna suka gaisa da Hajiyar da tambayarta mai jiki,ta amsa babu yabo saboda ta san idan tace da sauk'i kawai fad'a za tayi,kafin kace me har an fara jera musu kayan ciye-ciye,ta ko ina maidservant ne turawa sai shigowa suke suna hidima da su,tun abun yana basu mamaki har ya daina,,a tak'aice ranar har bayan maghreb suna gidan sai kusan isha sannan suka yi shirin tafiya,Hajiya ta cika su da goma ta arziki and tasa su Clark da driver su mayar da su gida,suka yi sallama,Hajiya thanked them saboda ta ji dad'i sosai tana ta basu hak'uri da sak'on su gaisar mata da Hauwa'u,ko da suka tashi dawowa motar da aka d'auko su a zuwa ba a ita aka mayar da su ba,,lolly was sitting in the parlor wondering where Annie went sai ga su sun dawo,ta bisu da kallo bayan ta yi musu sannu da dawowa,Clark ya shigo musu da kayan da Hajiya ta basu sannan yayi musu sallama,lolly ta bisu da kallon mamakin inda suka samo shi,dai² suna zama saman armchair,looking at them again tace "Adda ni kam ina kuka jene.!? Ni dai na san babu wanda kuka sani a garin nan,amma tun yamma da kuka fita sai yanzun,nayi tunanin ko mall kuka je.." Annie tace "Who knows ko we have found out a new family ne a nan k'asar" she quickly looked at her and was surprised by the expression tace "relatives? Here.!?" Ta gyad'a mata kai tana tashi tace "Ehh! Kin san komai nufin Allah ne ai" ta jinjina kai tace "Haka ne" daga haka bata sake magana ba,a ranta take ta juya maganar and ta k'udurce duk abunda Annien za tayi ba zata sake tambayarta ba,but zata sa mata ido har sai ta gano ko mene ne take hidden mata.

9:00pm His car stopped at the apartment,ya fito ya rufe a hankali ya nufo entrance,duka suna zaune a parlor har lokacin suna hira doorbell tayi k'ara Annie tace "Daughter je ki bud'ewa.." Tun bata k'arasa ba tayi zumbur ta mik'e tana fad'in "Kai Annie,ni dai ba sai kin fad'a komai ba" Ita Annie dariya ma Nusran ta bata,tace "Ku ji min ja'ira,do u know what am i going to say kika tari numfashi na.!?" Tace "No Annie! But if u say so Allah na san sai kin sani jin kunya" suka sa dariya har Bareerah dake fitowa daga kitchen,dai² tana bud'e masa k'ofa Bareerah tace "Ni dai Annie ban san me yake faruwa ba,duk naga kwana biyu baby kunyar ki take ji." Annie tana dariya tace "To waye ya sani ne,ga ta nan dai tambayeta muji whether she'll say anything to u",suna had'a ido da shi yayi mata murmushi k'asa² yadda za ta ji shi yace "Hi.!" Ta bishi da kallo tace "Hello" He rolled his eyes and stood still where he was yace "how are u.!?" Tace "Uhm! Alhamdulillah" ya jinjina kai yana sakin ajiyar zuciya sannan ya fara takowa ciki,ta koma baya kad'an ta bashi hanya ya wuce ta mayar da k'ofar ta rufe sannan ta dawo tana cewa "Bareerah Aunty what are u asking.!?" Bareerah tace "Kunyar Annie naga kina ji,wai mene ne yake faruwa ne.!?" Tayi murmushi tace "Kema dai Auntyn nan ki ji ki da wani magana,kuma shi kenan ba zan ji kunyarta ba.!?" Bareerah tace "Amma da ai banga hakan ba,when did u start.!?" After she sat back tace "Yesterday" suka sake yin dariya.
Chapter 61 · 0% Book details