← Book details Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 122 OF 152

Sashe 122

Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun da suka bar gidan Annie take zaune a gurin tak'i yarda ta tashi,Abbah dake shigowa lokacin ya yi musu rakiya bayan ya yi addu'o'in neman tsari da kariya ya kulle k'ofofin gidan duka,ya dawo inda take fuskarsa d'auke da murmushi mai tattare da nutsuwa,yana fara tahowa inda Annien take ta sake sunkuyar da kanta k'asa tana yin duk addu'ar da yazo bakinta saboda yadda take ganin abubuwan suna faruwa kamar ba gaske ba,Abbah ya k'araso cikin rantsatstsen parlor'nsu da yaji wasu irin royals na musamman masu kama da anyi musu feshin gold,ya zauna yana fad'in "Rabbigfirliiy watuub alayya innaka antat'tawwabul gafuur",sun zauna shiru na wani lokaci kafin Abbah yayi gyaran murya,a hankali yana kallonta yayi ajiyar zuciya ya fara magana
"Arhm! Ina son cewa wani abu,but i just don't know idan nace zan fad'i abunda yake raina yanzun maybe ko zan takura ki?" Annie dake tunanin yadda rayuwar ta nan gaba zai kasance tayi ajiyar zuciya a hankali ta d'ago tace "Babu komai" yayi murmushi yace "Na gode" shiru parlor'n yayi na wani lokaci kafin Abbah ya numfasa,a hankali ya fara da fad'in "Alal hak'ik'a even though na san dukan mu babu yaro,and then yanayin mu'amalar ki ya tabbatar kina da sani,ina da tabbacin ba za ki tab'a yin abunda yake ba dai² ba in Allah ya amince" sai da yayi shiru kafin ya d'ora da fad'in "A gaskiya na yi matuk'ar farin ciki,kuma ina yiwa Allah godiya da wannan baiwar da yayi min,though a bayan na yi aure sau biyu,na san kina da labari wani kuma kin san abunda ya faru,but duk dai ina son sake sanar da ke ne ba don komai ba sai domin ina tsammanin samun zaman lafiya,nutsuwa da kwanciyar hankali daga gare ki,a zamanin aure na farko bayan shekarun da muka d'auka tare da ita KHADIJAH,duk da Allah yayi mata rasuwa,alhamdulillah tun da muke zaune da KHADIJAH ban fuskanci wani matsala gareta ba har Allah ya karb'i rayuwarta,sai dai wacce na aura a karo na biyun a zaman da muka yi duk da shekarun ba su da yawa na fuskanci matsaloli masu tarin yawa,wanda har kullum na tuna ina jin bak'in cikin kasancewa da irin wannan matar,sai dai ita rayuwa duka kana yin naka tsarin ubangiji yana nasa,sannan rayuwar kanta tana tafiya ne bisa doro na k'addara,abunda Allah ya nufa shi yake kasancewa,wanda bai so ba kuma ba ya kasancewa,sai dai ina fatan zaman da zamu yi yanzun zai kasance zama na amana,duk abunda kika gani zan yi ba dai² ba za ki tallafeni ki yimin jagoranci zuwa kyakykyawan hanya,kamar yadda idan na ga za kiyi zan nuna miki hanyar da ya dace" Annie dake sauraron jawabin Abbah ta kad'a kai a hankali tace "In sha Allah ina fatan hakan,ina rok'on Allah ya ba ni ikon yi maka biyayya tare da sauke hak'k'ok'in da suka rataya a wuyana" Abbah yayi murmushin jin dad'i ya amsa da "Ameen",daga nan yayi mata jagoranci zuwa bedroom d'insu,here na basu guri kun san soyayyar manya yafi k'arfin idanuwan mu.

*Asubah ta gari (A²)...*

*****

Rayuwar gidan Annie ya kasance wani irin rayuwa ne mai cike da tsafta da girmama juna,kasancewar su duka ba yara bane,but tsarin zaman sun abun burgewa ne ga kowa,tun daga kan yanayin soyayya,kulawar da suke gwadawa juna idan ka shiga gidan za su sa kayi tunanin auren sun tun na saurayi da budurwa ne,yayin da a b'angaren Abbah ya kasance tun da ya samu Annie matsayin matar aure yake jin wani irin nutsuwar da bai tab'a samun irin ta ba a duka rayuwarsa ta baya,haka itama Annie a nata gefen sai take jin kamar da can ba aure tayi ba yanzun ne tayi shi a inda ya dace,even though mijin tan na baya da ya rasu yana sonta sosai but soyayyar Abbah gareta ya zame mata tamkar wani babban *KUNDIN* da bata tab'a bud'e shafin sa ba bare tayi karatu a cikinsa.

Cikin sati biyu da su Lolly suka sake yi a Nigeria tare da su bayan sun huta gajiyar biki,a nan Nusrah ta yi tunanin yiwa Abbah maganar zuwa dangin Mamma'nta,saboda rabonta da su baza ta iya tunawa ba,lokacin da ta yiwa Abbah maganar yayi shiru bai ce komai ba,da ta takura masa yace ta bari idan sun samu lokaci zai kaita,tayi shiru tana tunani because an d'auki tsayin lokaci take cewa tana so ya kaita ko ya barta taje yana hanawa,a gefen Abbah kuwa duk wannan hanya² da yake mata ba don komai bane sai don tsoron abunda zai iya faruwa,kasancewar bai manta irin rabuwar da suka yi da dangin Khadijah ba a lokacin da ta rasu,k'aramin yak'in da aka yi akan sun nuna suna so ya basu Nusrah su tafi da ita duk da ba yarinya bace k'arama da za ace idan tayi wayo za'a dawo masa da ita,Abbah yace ba zai iya ba ita kad'ai yake da,suyi hak'uri su bar masa y'arsa,an kai ruwa rana sosai lokacin har daga baya dai aka rabu dutse a hannun riga,daga nan ne tunda suka yi fushi basu sake zuwa ba saboda mangaganu da akayi musayarsu,shima kuma Abba'n sai bai kaita ba saboda sun nuna basa buk'atarta ya rik'e y'arsa,suna cikin wannan rigimar da Abban ta dage akan lallai ita ko address d'in ya bata taje da kanta,cikin satin ayyuka suka tasowa Rafeek,dole yasa suka tattara har su Annie suka nufi UK,unlike su Hajiya da su tun a satin da aka yi biki suka koma,a cewar Rafeek ko da suka yi magana da Abbah yana tambayarsa me za suje yi Uk? Rafeek yace yana da kyau suje honeymoon ne,Abbah dai yayi dariya but a zahiri ya fahimci dalilin aminin nasa na yin hakan,kasancewar ba ya iya b'oye masa komai haka shima,ko da suka sauka a k'asar lokacin da aka zo d'aukansu a airport har suka zo gida babu wani maganar da suka ji daga garesa,sai da suka shigo cikin mansion,a nan idanunsu suka tarar da abun mamakin da basu tab'a zato ba,kasancewar sati uku kenan basa k'asar,sannan a saninsu apartment biyu ne a gidan daga nasu sai na Hajiya,yanzun kuma sai lsuka tarar da k'arin guda ma'ana apartment d'in sun koma uku,duka suka tsaya kallon Rafeek because sun san aikinsa ne,yayi murmushi yana kallonsu kamar yadda suke yi sai yak'i cewa komai,Lolly tace "Yallab'ai! Wannan ginin fa?" Ya kalli su Nuraz yana yin murmushi yace "Na yara na ne",ta kalleshi da mamaki tace "wane yaran na ka?" Murmushi ya sake yi yana wucewa cikin apartment d'in Hajiya yace "kin fi kowa sanin wane yara nake nufi" quickly ta biyo bayansa tana cewa "Please Yallab'ai ka yi min bayani!" He didn't stop yana ci gaba da tafiya yace "u will soon understand" Su kansu su Nusran da suke tsaye ganin tafiyarsu da abunda suka ji yana fad'a ya ba su mamaki,sai dai babu wanda yayi tunanin wani abu,duka suka biyo bayansu,kafin su k'arasa shigowa Hajiya ta taho tarbarsu,ganinsu duka sunaa shigowa yasa cike da farin ciki ta bud'e baki,duk sai ta rasa wanda za ta fara tarba a cikinsu saboda yanayin da suke ciki ya tabbatar mata suna cikin kwanciyar hankali. Tarba na musamman da ta shirya saboda ta san da zuwan sun ya k'ayatar da su,bayan sun anci an sha aka zauna hira a parlor'n tsohuwar,ana tsokanar juna da wasa da dariya abun gwanin burgewa,yanayin ranar ya fi komai yiwa Hajiya dad'i,cikin tsananin farin cikin yadda family'n suka had'e kai tayi murmushi tana sake yiwa Allah godiya bisa wannan ni'imar da yayi a garesu.

Da dare a time d'in kowa yayi shirin bacci bayan sun gama hira,Nusrah ta shigo bedroom bata yi sallama ba sai b'ata rai take,ya d'ago kansa daga aikin da yake yi a computer ya kalleta bai ce komai ba,tana zuwa za ta wuce ta gabansa yayi saurin rik'o ta ya dawo da ita,ta kalleshi bata ce komai ba,yayi ajiyar zuciya yana k'ureta da kallo yace "what happen?" Ta girgiza kai bata ce komai ba sai k'ifta ido da take yi,a hankali ya janyota ya zaunar a jikinsa ya rik'o fuskarta,muryarsa k'asa² yace "Ba za ki fad'a min ba?" Kuka ta fashe masa da shi,ya lumshe idonsa yayi shiru sai da yaga ba ta da niyyar dainawa ya bud'e idonsa yana kallonta da kyar yayi ta maza yace "Shhhh! Be quite please" ya rungumeta yana shafa bayanta,da kyar ya samu tayi shiru tana yin ajiyar zuciya yace "Mene ne aka yi miki?" Sheshshek'ar kuka ta fara,za ta ci gaba yayi saurin cewa "u know ba na son kuka,yana tayarmin da hankali duk lokacin da naji ana yinsa kusa da ni,sau nawa kike so na fad'a miki ba na son kina yin kuka?" Tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya,a hankali ya sauketa daga jikinsa ya fita,ta bishi da kallo har ya dawo tana inda ya barta,yana zuwa ya mik'a ruwa,ta karb'a ta sha ya sake zaunawa a gefenta,sai da ya bari ta samu nutsuwa then yace "Za ki iya fad'a min abunda aka yi miki?" Ta lumshe ido fuskarta tana bayyana damuwarta cikin shagwab'a tace "ba Abbah ne saboda nace ya kaini family'n Mamana.." Bata k'arasa ba yace "Me za kiyi musu ne kike son zuwa?" Tayi saurin kallonsa,ya kalleta yace "Uhn! Tell me" ta had'iye saliva's da kyar saboda yadda fuskarsa ta koma tace "Dama fa ban sansu ba sosai,kuma tunda ta rasu bamu sake zuwa ba" ya gyad'a kai yana rufe computer da ya bari yace "Yanzun kuma kina son zuwa?" Ta gyad'a kai tace "Ehh!" Ya kad'a kai yace "Ok! Bari mu gani k'arshen session d'in ku yayi" tayi saurin kallonsa tace "will u..?" Bata k'arasa ba ya girgiza kai yace "Ban yi alk'awari ba" tayi murmushi mai burgewa saboda da farko da ya girgiza kai bata yi tunanin abunda zai fad'a ba kenan,da sauri ta haye jikinsa cikin murna duk da bai amsa zai kaita ba,but ta sani tunda yace idan sun yi hutu tana da tabbas zai kaita.
Chapter 122 · 0% Book details