← Book details Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 152

Sashe 77

Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Since suka bar gidan their conversation were all about what happened yesterday at k'ofar Na'isa,yanayin yadda al'amarin ya kasance har lokacin gani suke kamar almara,Nusrah kam tunda suka d'auki hanyar gidansu tayi shiru,banda addu'ah babu abunda take yi har sanda suka shiga cikin unguwar,yanayin yadda take bin ko ina da kallo kamar bak'uwa shi ne ya bawa Nuraz mamaki ya kalleta kad'an ta mirror,yadda fuskarta tayi kalar damuwa duk sai ta ba shi tausayi,suna tsayawa a bakin get d'in gidan duka suka fito,Nusrah ta yi mamaki da taga ya gane gidan ba tare daya tambayeta ba,bayan sun sallami mai taxi d'in daya kawo su,kai tsaye suka tasarma get d'in gidan,su Annie a gaba sai ita da shi da suke bin bayansu yana mata magana k'asa²,sun shigo cikin gidan kasancewar k'ofar a bud'e yake,mai gadi dake cikin d'akinsa jin an bud'e k'ofa ya lek'o da niyyar yin magana yana ganin manyan mutane ne bai tsaya tambayar gurin waye suka zo ba,sun dai gaisa da su ya koma ba tare daya damu ya san gurin waye suka zo ba ko waye suke nema ba,since they came in not only Nusrah even Annie was surprised by the changes,the whole house was renovated and remodeled,though babu abunda gidan yayi but duk an fashe shi an sabunta gininsa,suna k'arasowa entrance d'in parlor suka tsaya suka yi knocking,ak'alla sun d'auki mintuna sama da biyar kafin aka bud'e musu k'ofar,zuwa lokacin Yallab'ai tuni ya fara haurawa sama,bcos he hates jira,Binitta tana ganin fuskokinsu ta tsaya tunanin inda ta sansu,Annie tayi siririn ajiyar zuciya tana kallonta ta furta "hope they're here.!" Binitta ta gyad'a mata kai and then ta basu hanya suka wuce zuwa ciki,kasancewar bata ga Nusrah ba har lokacin and ko yanzun ma itace k'arshen shigowa tana zuwa za ta wuce Binitta ta ware ido tana kallonta,bakinta har kyarma yake wajen furta sunanta,kamar wata mara gaskiya da sauri ta kamo hannunta suka yi waje jikinta sai rawa yake,Nusrah couldn't speak until they stood in the garden tana kallon Binitta da wani irin damuwa ta furta "what happen Binitta.!?" Idanun Binitta suna tara kwalla ta kalleta cikin rawar murya tace "why did u go all for a while.!? Do u know how ur father situation is.!?" Gaban Nusrah yana fad'uwa ta rik'o hannun Binitta tana fad'in "What happened to my father.!? Tell me Binitta" hawaye suna zubowa daga idanun Binitta tace cikin hausarta da bata fita sosai "The story was long but give me ur number and address na gidan da kike zan zo wani ranar,and ka fad'awa Hajiya da kuka zo da shi,kuyi tafiya.. ku tafi kafin Aunty ya sani kun zo" Nusrah tana kallonta tace "saboda me za mu tafi.!? Gurin Abbanah ai muka zo ba gurinta ba" Binitta ta runtse idanunta tace "Idan har kin yarda da ni,ya kamata kuyi tafiya daga gidan nan,idan Aunty ya sani anything can happen" jikin Nusrah har tsuma yake tace "We won't go until we have done what brought us here,duk abunda za tayi sai dai tayi but we will never leave this house" Binitta tace "Ni ba ina cewa kuyi tafiya bane i'm just afraid of what will happen" A tsawace Nusrah tace "Ke da Allah ki bari mu ganta duk abunda za tayi kada ta fasa tayi mana,waye yake jin tsoronta?" tana fad'a bata jira Binitta ta sake magana ba ta wuce a fusace ta barta a nan,jikin Binitta yana kyarma ta biyo ta tana kiranta,but Nusrah bata jira ba ta wuce da sauri,tana shiga cikin parlor'n lokacin ya yi dai² da sanda Abba'nta yake saukowa from the staircase side bayansa hamshak'iyar ce tana tafiya cikin isa da izza,kasa zaunawa Nusrah tayi ta kafesu da kallo,yadda Abba'nta ya rame abun tausayi duk ya tsotse kamar kud'in guzuri,mutum mai ji da dukiya,kyau da matsayi amma kallo d'aya za kayi masa ka tabbatar a firgice yake,kamar ance ya d'aga idanunsa jin magana k'asa² a cikin parlor yana kallon cikin parlor'n idanunsa suka sauka akan Nusrah dake tsaye ta kafe shi da wani irin kallon tausayi idanunta suna tara hawaye,her heart were all weakened in some kind of expression ta furta "Abbah!" Not only him even Hajiya was scared of seeing her,jikinsa yana rawa da wani irin expression a fuskarsa ya juya ya kalli Hajiyar ya sake juyawa yana kallonta,bakinsa har b'ari yake lokacin daya tabbatar ita ce a tsorace ya furta "Nusrah.!" Yana fad'a ya fara sakkowa da sauri,da sauri itama Nusrah ta nufi gurinsa kamar yadda yake yi,daf da za su rik'e juna Hajiyar ta kira sunan Abba'n da wata irin murya *"ABUBAKAR.!"*,cak ya tsaya a inda yake ya juya yana kallonta jikinsa na kyarma ya furta "Na'am Hajiya ta" fuskarta a mugun had'e tace "Zo nan" babu musu kamar wani gaula yace "To" tiryan-tiryan ya koma kusa da ita har yana yi kamar zai tsuguna a gabanta,yadda lamarin ya faru akan idanunsu ba k'aramin tsoratar da su yayi ba,Nusrah kuwa k'amewa tayi a gurin da Abba'nta ya barta tamkar gini,Hajiya tana kallonsu tana yatsina fuska cikin fad'a ta furta "Da ka tafi gurinsu ka san su ne.!?" Saurin girgiza mata kai yayi muryarsa tana rawa yace "A'a" ta harare shi tace "Ka san bana son munafurci ko.!? Za ka fad'a min ko a'a.!?" Ya sake girgiza mata kai yana fad'in "Wollahi Hajiya ban san su ba" tsaki tayi ta fara sakkowa tana tafiya,ya biyo bayanta kamar wani bodyguard d'inta har suka ratso cikin parlor'n,zaunawa tayi saman armchair tayi shirim,Abba'n Nusrah kuwa ya takure a gefe kamar ba gidansa ba,yana goye da hannayensa a baya,yana shirin yiwa su Annie magana ta banka masa hararar da dole yayi shiru ya sake komawa baya,Annie da Lolly banda kallon mamaki babu abunda suke jifansu da shi,shi kuma Abba'n abun tausayi tunda ya koma gefe yayi tsuru bai sake attempting yin magana ba sai binsu da kallo kawai yake yi,saurin mik'ewa Annie tayi tana kallonsu tace "Kunga ku tashi mu tafi,ina ganin babu buk'atar mu ci gaba da zama" duka kamar jira suke ta basu umarnin suka mik'e,wani mugun kallon da Nuraz ya aika mata yana girgiza kai sai da yasa ta taji tsoron sake kallon cikin idanunsa,inda Nusrah take Lolly ta matsa ta kamo hannunta,cikin sanyin murya ta furta "Yi hak'uri daughter muje kinji akwai Allah" sai lokacin wani irin kuka ya kwace mata tana toshe bakinta da duka hannayenta,da sauri Annie ta matso kusa da su tana fad'in "Haba daughter kada kiyi kuka mana,duk abunda yake faruwa kin manta Ubangiji yana kallo,duk abunda mutum zai yi kansa ya yiwa,ke dai ki tsarkake zuciyarki sannan kada ki zalunci kowa,duk abunda za ki aikata ki dunga tunawa cewa ubangiji yana kallon ki",ai kamar Annie ta watsa mata narkakken dalma haka taji saukar kalamanta,though ba ita take kallo ba lokacin da tayi maganar but ta fahimci magana ta fad'a mai harshen damo,girgiza kai kad'ai tayi ba tare da ta tanka musu ba har suka yi nasarar janye Nusran suka bar parlor'n,Abba'n Nusrah dake tsaye yana kallon sun fita ya faki idon Hajiyar zai bi bayansu,har ya je bakin k'ofa ta kalle shi tana fad'in "Kai kuma munafuki da kake k'ok'arin fita ina za kaje.!?" Da sauri ya juyo yana kallonta jikinsa na rawa yake fad'in "Am.. Umm! Dama ai kin san zan fita ana jira na a office" harararsa tayi tace "Da wane munafuki ne yace ka tsaya baka tafi ba.!?" Hak'uri ya fara bata tayi tsaki tace "Will u come back or not.!?" Ya tsaya a gurin jikinsa sai kyarma yake saboda baya so ta gane nufinsa cikin dad'in baki yace "Haba Hajajju ina na isa nace bazan zo ba,but da kin yi hak'uri na je mun gama meeting,na fad'a miki harkar kasuwanci ne and za'a samu alkhairi sosai,kiyi hak'uri mana nasarar duk da za'a samu taki ce fa" tab'e baki tayi sai kuma ta furta "Shi kenan sai ka dawo" tana fad'in haka yayi mata murmushin yak'e and ya juya a hankali yana tafiya gudun kada yayi sauri tayi zargin wani abu daban.
Chapter 77 · 0% Book details