← Book details Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 129 OF 152

Sashe 129

Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Two weeks after the incident,duk inda suke tunanin samun mafita sun buga sai dai rashin nasara,and at this time duka abunda yayi saura hannunsu ko half na fili bazai siya musu ba bare gida,tun lokacin yau idan suka samu labarin wani malami da aikinsa yake ci a gari kaza,a goben za su tattara su tafi,idan sun tarar da ba yadda suke buk'ata ba,goben suka samu labarin wani,without thinking of abunda zai je ya dawo za su sake d'iban jiki su tafi,cikin wannan yanayin duk abunda suke tak'amar suna da ya fara janyewa,lokaci kuma yana ci gaba da tafiya.

Two weeks later,which is two months da mutuwar aurenta,it was during this time suka samo wani bokan da aka ce idan yayi musu aikin tabbas zai yi za su yi mamaki,but cikin ayyukansa akwai sharud'a,suka ce sunji aun amince,yadda aka ba su labarinsa duk haka suka tarar,bayan zuwansu kafin suyi masa bayani ya dakatar da su,ya zayyana musu duk abunda yake tafe da su,Hajiya Karima ta amsa shi da haka ne duk abunda ya fad'a babu musu,boka ya kece da dariya,bayan ya dakata yace "Za'ayi muku aiki,sai dai akwai sharud'a" Hajiya Mariya ta cafe zance da fad'in "Ka sanar da mu kowane irin sharadi ne,za mu bi duk abunda kasa mu aikatawa,matuk'ar buk'atarmu zai biya" Boka yace "buk'atar ku zai biya sai dai sharud'a" jikinsu yana rawa suka ce ya fad'a,it was there b'ataccen ya fara shirya musu zancen "Da fari duk wani aikin da za muyi ba zai yi ba har sai Hajiya Karima kin koma gidan Alh Abubakar kin nemo kusanci da wani cikin na jikinsa like mata/y'a/mahaifi/k'ani/hadiminsa" Hajiya Mariya cikin kid'imewa tace "Aiki ga mai k'are ka,yanzun ta ina za ta samu wannan damar bayan lokacin da ya wuce munyi k'ok'ari mun raba shi da kowa,shin ta ina ne za ta samu damar shiga gidan har akai ga yin haka?" Bokan ya sake kecewa da dariya "Wannan duk ba damuwa bane,idan har tana son cikar burinta,dole sai ta shiga gidan nan,ita da kanta za tayi wannan aikin,amma akwai taimakawar shaid'anu!" Calmly Hajiya Mariya ta washe baki "Aikin sun ma ai zai fi sauk'i fiye da mu da sai mun faki idanu,me zai sa baza mu biya ba,sai su aiwatar da aikin kawai" Boka yana kallon Hajiya Mariya da wani irin muryarsa mai ban tsoro yace "Ba ita za tayi ba,su za mu sa su aiwatar!" Kan Hajiya Mariya ya kulle jin abunda ya fad'a tace "Ta yaya kenan uban shaid'anu?" Ya sake kecewa da dariya,bayan ya d'auki lokaci ya dakata yace "Wannan ba huruminki bane,kada ku shiga abunda ba ku da ruwa cikinsa!" Hajiya Mariya cikin gamsuwa tace "An gama shu'umi uban la'anannu!" Hajiya Karima was sitting on the side tana tunanin yadda aikin zai kasance,da farko bokan yace aljanu ne za su yi ba ita ba,and yace she had to look for closeness with someone cikin family'n Alh Abubakar Kumo,how can she get this chance? Duk ba ma wannan ba,ita yadda za ta shiga gidan shi ne abunda ya d'aure mata kai,a bayan auren sun ta raba shi da kowa nasa shin ta yaya ne wani d'an uwansa zai bari ta rab'e shi a yanzun? "Where's Umar Farouk?" Zuciyarta ta tambaye ta dai² lokacin da take neman mafita,wani irin cafka ta kaiwa wayarta,da sauri ta d'auka ta fara lalube,in less than three minutes ta hango lambarsa da tun wancan lokacin bayan ta samu damar had'a connection da shi zuwa ga Abbah har ya aureta take ajiye da ita,bata jira gama yanke shawaran abunda ya kamata tayi ba ta danna masa kiraa,wayar tana shiga Farouk ya d'auka had'e da fara zuba mata kirari,Hajiya Karima ta furzar da iska mai zafi maimakon abun ya burgeta kamar ko wane lokaci sai taji wani irin k'unci ya lullub'e zuciyarta,har a lokacin suna zaune gaban bokan nasu da gaggawa ta furta "Farouk kana ina ne?" Daga gefen Farouk ya amsa "Hajajju wani abu ne kike nemana da gaggawa?" Hajiya Karima tace "Idan babu damuwa ina son ganinka" Farouk yana jin ta ce haka yace "Tabbb' d'i jan! Ai wollahi Hajiya ba na kusa,maganar da muke yi da ke yanzun haka ma ina shirin barin k'asar ne" Hankalin Hajiya Karima a tashe ta tari numfashinsa "Zuwa ina?" Farouk yace "Wollahi daga gida aka yi min waya mahaifiyata ba ta da lafiya jikinta yayi tsanani" Hajiya Karima cikin tsananin tashin hankali tace "Idan ka tafi sai yaushe za ka dawo kenan?" Farouk yace "Gaskiya babu lokaci,dawowa na sai lokacin da Allah yayi kawai" Hajiya Mariya ta tab'a Hajiya Karima tana tambaya "Me yake faruwa ne?" Hajiya Karima ta kalleta idanunta sun k'ank'ance tace "Shi kenan Farouk,sai ka dawo d'in za muyi magana",har suka gama maganar suna shirin ajiye waya Farouk yaji bata tambayi mai jiki ba,har zuciyarsa sai yaji babu dad'i,za ta kashe wayar kenan Farouk yace "Hajiya wai kuwa kina da labarin Yallab'ai ya yi aure?" Hajiya Karima tana yamutse fuska tace "Wane ne yayi aure?" Farouk yana sakin murmushin mugunta a ransa yace "Bari nayi miki abunda ba za ki ji dad'i ba tunda tsayin rayuwarki baki san mai miki mutunci ba" a fili yace "I'm talking to ur ex-husband Alh Abubakar Kumoo!" Wani irin zabura tayi tana zunduma ashar,Hajiya Mariya tayi saurin rik'o ta,a fusace ta fizge hannunta tana fad'in "Kan uba! When did he get married?" Farouk yace "Ina tunanin wata d'aya kenan yanzun" hankalinta a mugun tashe take girgiza kai jikinta duk sai rawa yake,kallo d'aya za kayi mata ka tabbatar da tsananin tashin hankalin da take ciki,ko gama sauraren Farouk bata yi ba,da taji ya ce bari ya turo mata I.V d'in dan ta tabbatar ta yanke kiran sai huci take idanunta sun sake k'ank'ancewa,duk abunda yake faruwa a gaban Bokan sun aka yi aka gama,lokaci d'aya fuskarta ta yi jaa because she never thought Abbah would get married this soon shi yasa ta sakankance,bata kai ga ajiye wayar ba sak'on Farouk ya shigo,tana bud'ewa idanunta suka sauka kan sunan Abbah,hankalinta ya sake tashi fiye da farko,ta d'ago idanunta da suka k'ank'ance sunyi wani irin jaa mai ban tsoro tana kallon witch d'in ta furta "Duk abunda zai faru sai dai ya faru amma ko zan yi yawo tsirara sai na raba auren nan,Abubakar baka isa ka rabu da ni sannan kayi tunanin zan bari ka zauna da wata mace daban ba!" Boka yana jin furucin da tayi ya kece da dariya,ta zuba masa ido tana kallonsa zuciyarta tana sake tunzurota da mugayen k'uduri,cike da fusatuwa tace "ina so a raba auren sun nan!" Boka yana ci gaba da dariya yake nunata da hannu,sai da yayi mai isarsa sannan ya tsagaita da watso mata tambaya "Me kike so ayi musu?" Tace "Ni dai komai ma ayi,amma kada su zauna k'ark'ashin inuwa d'aya!" Wasu irin d'alasiman tsafi ya fara furtawa idanunsa a rufe,bayan wani lokaci yayi saurin bud'e idanunsa,yana kallonta da wasu irin jajayen idanunsa yace "Canza wani buk'atar wannan bazai yi ba" a razane ta kalleshi tace "Kamar ya bazai yi ba?" Yace "Abunda na gani kenan,su duka suna tare da tsari daga ubangijinsu,raba su abu ne mai matuk'ar wahala" Hajiya Karima ta runtse idanunta felt like a chilli powder was poured on tace "Ni dai kawai ayi duk yadda za ayi a raba su" sake rufe idanu yayi yana ci gaba da sambatu,ba'a d'auki lokaci ba ya bud'e idanunsa ya sauke kan Hajiya Karima da fad'in "Akwai hanya d'aya idan kin amince,sai dai akwai had'ari!" Bai k'arasa fad'a ba ta amsa da fad'in "Whatever a danger na amince!" Bokan ya jinjina kai ya juya gefensa dama da hagu sannan ya kalleta yace.....

#Ku k'ara hak'uri da ni please,all these days wayana take ba ni matsala.

#Share pls.
#Asli Smasher.
💠💠💠💠💠
*©®2020.*        

                   *'DAN MACE..*
              (Tʜᴇ ᴘꜱʏᴄʜɪᴀᴛʀɪꜱᴛ)..💥

*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*    
https://my.w.tt/29u2S26SG2

🎉 *U stood with me every time i snapped,u made my every childhood experience a memorable one,u are my best friends since all these years,and u are the reason i believe in myself. Thank u for all the awesome times we shared 😍,wish u a very happy birthday habibtiiys.♥*
      *NI'IMATULLAH (Aunty Hassy) & RAHMATULLAH (Aunty Hussy).🎂*

Pᴀɢᴇ 50.
#A ɴᴇᴡ ʙɪʀᴛʜ
Chapter 129 · 0% Book details