Sashe 73
Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Annie ta daure tana b'oye kukanta tace "Muna nan cikin k'asar nan Baba,babu inda muka je" Baba yana maimaita abunda ta fad'a da mamaki yace "Amma kuna cikin k'asar baku tab'a neman gida ba tsayin wad'annan shekarun.!? Me zai sa ku k'i zuwa gida ku duba lafiyar mu.!?" Annie ta lumshe ido ta bud'e hawayen dake cikin idonta suka gangaro,silently ta furta "Baba." Then kuma tayi shiru because she felt the pain of repeating the past,Baba ya sauke kansa k'asa a hankali bcos ya fahimci damuwarta silently ya furta "Na tabbata duk abunda ya faru babu laifin kowa a cikin ku face nawa,da ban kasance irin wannan uban da duk abunda aka fad'a masa yake yarda ba tare da ya yi bincike ba,da ban kasance mara adalci ga iyalina ba,,da ban zama mai d'aukar maganar mutane ba,surely da hakan bai zame min makamin da nayi amfani da shi wajen tarwatsa ahalina tun daga tushe ba,sai dai duk da hakan ko kad'an bai kamata ace wannan dalilin ya zama sanadin da zai hana ku dawowa gida ba,why should we all be angry.!? Duka mun yi fushi bayan shugaba (S.A.W) ya hane mu saurin fushi da yanke hukunci cikin sa,dukan mu mun kasance masu laifi ta hanyar sab'awa maganarsa da bin khud'ubar zuk'atanmu,and this reason alone ya isa hujja da Ubangiji (S.W.T) zai hukunta mu gaba d'aya" Annie wiped the tears that poured out tace "Baba.! At that moment ka yi fushi sosai da mu how can we think if we come back u will forgive us and forget the fast.!?" Baba ya girgiza kai cike da jimami yace "Of course i made a mistake which i myself sure that it will be hard to correct,babbar damuwar kuma duk ba wannan ba,i contradicted the words of our holy Prophet (SAW) na raba ku da jiki na,na kore ku daga gida na,na raba ku da duk wani source da zai ba ku farin ciki,how can i ask forgiveness for what i have done to u.!? Na yi nadama a lokacin dana san gaskiyar al'amarin daya faru,na yi Allah wadai da halayyata ta saurin d'aukan magana,na yi dana sanin kasancewa ta irin wannan mahaifin mai korar y'ay'an cikinsa,what evidence do i have har ya janyo na aikata d'anyen hukunci irin wannan.!? Even before hadisin Annabi (S.W.A) ya kwad'aitar da mu hanyar samun aljannah ga duk mahaifin daya tarbiyyantar da y'ay'ansa mata,ya tsare mutuncinsu har zuwa lokacin da ya kaisu d'akin miji,,shin me yasa na manta da wannan hadisi a lokacin da ya kamata ace na yi amfani da shi.!? Ya Allah ka gafarta min sannan kasa yarana suji k'aina,ku yi hak'uri ku yafewa wannan mahaifin na ku.. Ba don halinsa ba,though ban cancanci hakan daga gare ku ba.. But.." Ba su jira ya kai k'arshe ba Lolly dake share hawaye tayi saurin katse shi da fad'in "We forgiven u Father",duka mutanen dake cikin parlor'n sai da suka dago suka kalleta lokacin da suka ji ta furta hakan,yadda take hawaye tana k'arawa kai ba za ka yi tunanin wannan kalmar za tayi saurin fitowa daga bakinta ba,slowly without ta bari wani cikinsu yayi magana ta ci gaba da fad'in "Idan muka kasa yafe maka Baba shin duk duniyar nan waye muke da shi da ya kaika.!? Kai ne fa mahaifin mu,wanda ya tsaya akan tarbiyyarmu tun daga yarinta har zuwa girmanmu,ka bamu ilimi dai² gwargwado,duk abunda ya faru a bayan mun riga mun sani kaima ba laifinka bane,Ubangiji (S.W.T) ya k'addara faruwar komai since before we were created,tun ran gini tun ran zane,therefore whether we like it or not,we must be patient and accept duk abunda ya same mu as our destiny.." Mamakin maganganun da suke fitowa daga bakinta ne suka d'aure Baba a gurin da yake zaune,banda gyad'a kai da tsantsar mamaki da tarin kunya gami da nadamar abunda ya aikata babu abunda yake cikin zuciyarsa,hawayen da suka taru gefen idanunsa ya share,yayin da zuciya da kwakwalwarsa jin su yake a cunkushe da tunanin abunda yayi musu a bayan,wanda ko kad'an bai tab'a zaton za su yafe masa ba,sai ga shi a dai² lokacin da bai yi tsammani ba suna furta sun jima da yafe masa and ko ganinsa da laifin ba suyi ba,slowly ya sauke wani munafukin ajiyar zuciya,inwardly ya furta "Lallai Ubangiji ya cika alhakimu kuma albasiru,idan banda ubangiji how can we think of reunion.!? Har yaran nan su yafe min,duk girman laifin da nayi musu.!?" Baba sai sak'e² yake a zuci.