Sashe 64
Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Quickly Nuraz turned his face to look where she was watching,akan Aatif idanunsa suka sauka wani mahaukacin gimtse fuskar daya sake yi babu shiri as if he had never known how to laugh,ta kalli yadda yayi kicin² duk ya tsare ta da idanunsa da sauri kafin yayi magana ta riga shi "What is he doing here.!?" Harara ya zabga mata ya d'age shoulders yace "how do i know.!?" Nusrah envisioning the bitterness of jealousy lying in his beautiful eyes ta sake marairaicewa gudun kada yanzun a dalilin Aatif ta sake fad'awa ha'ula'i tace "But this is ur house.!" Siririn tsaki ya saki yace "when did it become our home.!?" Kamar za tayi kuka tace "Please tell me what brought him here.!?" Ya tab'e baki yace "Let's just go ba sai mun k'arasa bama" tayi saurin girgiza masa kai tana lumshe idanunta da take jin suna mata wani irin yaji da zafi² tace "A'ah! We won't do that" ya kalleta zai yi magana Hajiya ta d'ago za tayi magana da Maimunatu ta hango inuwarsu ta bayan pillar,ta zubawa gurin ido kafin tace "who's there.!?" Gaban Nusrah ya fad'i ta marairaice fuska tace "Ka gani ko.!?" Ya sake tab'e baki ya fito yana harhad'e fuska yayi sallama,Hajiya ta saki fuska tana masa maraba saboda ba kad'an ba tayi farin ciki da zuwansa,har ya yi gaba ya waiwaya yaga bata fito daga inda take ba,ya dawo da baya yana kallonta yace "will u come out or not.!?" Ta kalleshi tana marairaicewa tace "Be quiet please" yace "Ank'i ayi shirun" tace "Please.!" Yadda tawani runtse ido abun ya so bashi dariya,ya fuske yace "Will u pass ko sai kinsa na d'auke ki a gabansu.!?" Tayi saurin bud'e idonta tace "Kai yanzu sai ka dauke ni.!?" He began to unbuttoning his shirts hand,quickly ta kalleshi tace "What are u planning to do.!?" Ya kalleta yana had'e rai yace "Wai da d'aukar kin zanyi kinga na rage miki tafiyan tunda yana yi miki wahala" ta zaro ido tace "I didn't tell u so" yace "ai ba sai kin fad'a ba,ni na san haka ne" ta tsaya kallonsa kamar yadda yake yi,Hajiya taga bai k'araso ba ta sake kallonsa,ganin kamar magana yake yi tace "Noor kai da waye ne.!?" Yayi saurin kallonta a hankali yayi murmushi ya rik'o hannunta ya janyota waje,Hajiya tana ganinta ta sake sakin fuska tace "Baby! What a surprise.!" Ta harare shi ta gefen ido a hankali ta fara d'aga k'afarta tana tafiya,yayi k'wafa yace "Za mu koma gida ai" har suka k'araso bata yarda ta sake kallonsa ba suka gaisa da Hajiya,suna gama gaisawa da Hajiya kawai sai yaja baki yayi shiru,yak'i ya tambayi ya mai jiki sai da Nusrah ta nuna masa sannan yace "Arhm.! Ya mai jiki.!?" Hajiya ta amsa calmly bcos ta ga abunda ya faru,Aatif dake zaune yana watching nasu since their arrival ya rasa me zaiyi,yana tunanin will he speak to them since they have ignored him or will he leave.? Daya rasa abun yi and ya gaji da kallon su ya mik'e a salub'e yace "Hajiya zan koma" Hajiya data shiga hidima da jikokinta tace "Well,Aatif har tafiya za kayi.?" Yace "Ehh Hajiya" Hajiya tace "thank u very much" yace "Babu komai Hajiya Allah k'ara lafiya" tace "Ameen,mun gode sosai ka gaida Daddyn ka,ka yiwa Mommyn naka godiya" ya amsa yayi musu sallama,ko kallo bai ishi Nuraz ba har ya fice,Maimunatu ta shigo ta zauna tana kallon Nuraz da yak'i sakin jiki tace "Hajiya sun shiga gurinsa ne.!?" Hajiya tayi murmushi tace "A'ah ki bari su huta mana ko.!?" Maimunatu tayi murmushi itama bata sake cewa komai ba,basu dad'e da zuwa ba y'ay'an Maimunatu suka shigo su uku namiji d'aya da mata biyu,in honor of seeing them suka gaida su,Nuraz ya kallesu kad'an though the children were impressed saboda tarbiyyar da suka samu amma ya fuske ya mik'awa *ARYAN* hannu,shima yayi masa murmushi ya mik'a masa hannu kamar yadda yayi though Nuraz ya girme masa,ya zauna a kusa da shi yana kallonsa da tunanin inda ya san fuskarsa,y'an matan suka zauna kusa da Nusrah suna mata hira babbar duka da ba zata wuce 18yrs ba ta fad'a mata sunanta *KALTHOM*,kasancewar they had no friends apart of mutanen k'asar mu,nan da nan suka saki jiki da Nusrah sai janta Kalthom take da hira,cikin k'ank'anin lokaci suka saba,the young lady who never passed 13yrs asked Nusrah's name Nusrah tayi mata murmushi tace "Nusrah" suka yi murmushi a tare da y'ar uwarta suka ce "Kina da suna mai kyau kamar ke" tayi murmushi tace "U too",karamar da har lokacin bata fad'a mata sunan ta ba,tace "Ni ai baki san suna na ba" Nusrah ta sake yin murmushi tace "Ehh duk da haka na san mai kyau ne kamar ke" kalthom tayi dariya tace "kaii! Sunan tsofaffi aka saka mata fa" Nusrah tace "Ai yafi dad'i sunan tsofaffin" Kalthom ta kyalkyale da dariya saboda tsokana take ji tace "Do u know what her name is.!?" Nusrah ta girgiza kai tace "A'ah" tayi caraf tace "sunan Hajiya ne aka samin fa" Nusrah ta girgiza kai tana murmushi,Kalthom tana sake yin dariya tace "Sunan ta.. Na fad'a.!?" Kafin ta fad'a Hajiya tayi magana "Kinga Kalthom ki fita idona,ke saboda rashin girma kullum ki tsokaneta kuyi ta rigima kamar wasu k'ananun yara shi ne burinki ko.!?" Tana dariya tace "Hajiya to ai sunan tsoffin ne gareta" Hajiya tace "Sannu mai sunan y'an gayu,aka fad'a miki ita nata sunan bai da dad'i ne.!?" Tace "A'ah ni dai ban fad'a ba" Hajiya tace "Kima fad'a ki ga yadda zanyi dake" ta sauke kai k'asa tana yiwa k'anwartan gwalo,ta shagwab'e fuska tace "Hajiya kinga tana min gwalo ko" throw pillow Hajiya ta jefowa Kalthom tace "Ja'ira za ta aikata",Maimunatu dake gefe tana duba ayatur-ruk'yah cikin littafin Addu'a'u min kitabi was-sunnah tace "Hajiya wollahi da kin fita sabgar *JIAN* tafi kowa tsokana kuma tafi kowa saurin kuka,ga kai k'ara kamar me,kuma wani abun ita take janyowa ayi rikicin,ga ta da d'an banzan ragwanci,ko yaya ka tab'a ta yanzun ta b'are maka baki" Hajiya tace "Ku kuka sani,ni dai ba zan saki takwara na rik'e iska ba,ko me za tayi ina bayanta" Jian tasa dariya ganin an goyi bayanta tana tsokanar kalthom,,haka sukai ta zama shiru sai dai ko yayi mata magana da ido,basu wani jima sosai ba Nuraz ya mik'e yana kallon Nusrah,he wants her to leave but the way they look at him makes him feel ashamed,Hajiya da taga haka bata ce da shi komai ba sai murmushin data k'irk'iro tace "Ba dai tafiya za kuyi ba.!?" Yayi ajiyar zuciya sama² yace "A'a Hajiya komawa za muyi" ta daure tace "Kuma baku shiga kunga jikin nasa ba" kamar zaice "Ba sai ya jeba" ya daure dai bai ce komai ba,Hajiya tace "Aryaan maza raka su suga jikin kawun ku" ya mik'e cikin ladabi ya wuce gaba,suka bisa a baya not because Nuraz wanted to go after him,tun kafin su k'arasa bedroom d'in san wanda tsakaninsa da su glass curtain wall ne da babu k'ofa suka hango shi,kwance yake saman wani irin lafiyayyen royal,duk inda tunanin mutum yake lamarin dole ya burge shi,k'asa² yadda ita da yayi maganar dominta ita kad'ai za taji yace "Kin sa mun wani zauna ko mene ne hakan oho.!" Ita dai bata kula shiba sai murmushin da tayi,suna shiga bedroom d'in Aryaan yaje dai² kansa da niyyar dubawa yaga ko ya tashi,da yaga idanunsa a kulle sai ya d'ago ya kallesu yana musu murmushi "Ina ganin kamar yana bacci" Nuraz ya lumshe ido ya bud'e yace "Don't worry,ba jimawa dama za muyi ba bcos we are on our way" Rafeek who had only been awake for a long time idanunsan ne kawai bai bud'e ba a firgice ya bud'e idanunsa sakamakon muryar data daki kunnensa,shi dai ya tabbatar a duniyarsa mutum d'aya ya sani da irinta,even in the world of death yaji ta after then aka dawo da shi back to his life aka sake tambayar shi waye zai bada gamsashiyar amsar da dole a yadda da shi,a kan Nuraz ya sauke idanunsa masu cike da hawaye,Aryan ya kallesu yayi murmushi yace "He's awaken" Nuraz ya tab'e baki yana d'auke kansa gefe,Aryan ya matsa kusa da Rafeek yace "Uncle anzo duba ka" ya girgiza masa kai slowly ya bud'e bakinsa yace "Thank u Aryan" ya gyad'a kai and then walked out ya ba su guri,Nusrah ta gaishe shi tayi masa ya jiki,ya amsa da kyar yana mata godiya,she turned to allow them to speak because of his attitude towards Nuraz but what? Tana zuwa za ta wuce ya rigata yin gaba,she quickly stopped and lost everything to do,taga dai da gaske niyyar fita yake hurrily tace "stop please" he turned angrily at her yana kallonta bcos ya san me za tace,ta matso inda yake k'asa² tace "Ka tsaya kuyi magana please,ko baka kula yana son maka magana ba.!?" Yayi kicin² da ransa yace "Ni wai.!?" Ta ga tambayar da yayi mata ya so raina mata hankali da sauri ta wuce shi,muryarsa ta jiyo yana fad'in "What if i stopped,what would he say to me.!?" Tayi saurin juyowa ta kalleshi with her soft-spoken voice tace "Well, it's good to listen to him,yana da kyau ka bashi dama,sannan ka bashi hak'k'insa na kasancewarsa mahaifi.." Tana fad'a ta wuce ranta duk a jagule tana hasko yadda zasu k'are ta da shi idan suka tafi,bayan ta bar gurin kasa juyawa yayi,Rafeek ya zubawa bayansa ido yana kallonsa with tears streaming down,yaji shirun yayi yawa ya juya a hankali yana tura hannayensa a cikin aljihun trouser d'insa ya tsare uban da kallo,da kyar Rafeek ya d'ago hannunsa ya d'auki handkey ya goge hawayen da suke ziraro masa ta gefe,Nuraz ya tab'e baki yace "Ya jiki.!?" Murmushin dole Rafeek yayi ya lumshe ido ya bud'e da kyar ya amsa "Alhamdulillah" daga haka Nuraz bai sake ko yin tari ba,sai daya gaji da jiran Rafeek yayi magana ya juya slowly ya fara tafiya,Rafeek ya bishi da kallo har ya fice yana jin zuciyarsa tana masa wani irin zafi,yana fitowa bai yarda ya zauna ba suka yiwa su Hajiya sallama suka tafi.