← Book details Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 131 OF 152

Sashe 131

Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

     Sun yi tafiya mai mugun tsayi,Hajiya Mariya was in a napep suna binta duk inda tayi da son dakatar da ita,duk magiya da yaudarar da tayi mata da taga yak'i aiki a kanta sai ta hak'ure tace mai napep d'in yayi ta binta har suje inda za ta gaji ta tsaya,mai napep yace "Hajiya kud'in ki fa k'aruwa yake yi" tace "Muje kai dai ba ka da matsala" haka mai napep yayi ta binta duk inda tabi,wajen maghreb har an fara kiran sallah sannan ta dakata bakin get d'in gidan Abbah had'e da fashewa da dariya tana kwala masa kira,mai gadi ya lek'o da ya gansu sai ya bud'e musu saboda wancan ranar sun yi masa barazana za su had'a shi da Abban,kafin Hajiya Mariya ta sakko a napep ta tuni Karima ta shige gidan tana zabgawa Abbah kira,Binitta dake can kitchen ta window d'in da yake a bud'e ta jiyo ana kiran ubangidansu da sauri ta lek'o wajen,tana tsayen taji Hajiya Karima ta kece da wani irin k'ak'k'arfan dariyar da ko namiji ba lallai yayi irinta ba,and then she began to reveal everything da suka aikata,cikin hauka ta bada labarinsa,jikin Binitta yayi mugun sanyi,tsoron Hajiya Karima ya sake shiga jikinta,leaning her back on the cabinet ta fashe da kuka,ta jima sosai a kitchen d'in,da ta daina jiyo surutun Hajiya Karima ta mik'e ta fito jikinta har lokacin bai daina rawa ba ta wuce d'akinta ta fara had'a kayanta,tana kuka tana fad'in tafiya za tayi,yau kam a gurin mamanta za ta kwana,baza ta sake zaunawa ba,but kafin ta tafi she decided to call Nusrah saboda kada ta tafi kai tsayen gara ta fara sanar da su za ta ajiye aikin.

*****

      A mugun firgice Annie dake bacci ta farka bakinta yana jeranta fad'in "A'uzhubillahi minashshaid'anir rajiiym.. Laa ilaaha illa anta subhanaka inniiy kuntu minaz'zalumiiyn!" Yanayin da ta farka da shi jikinta ya had'a gumi duk uban sanyin dake cikin k'ayataccen bedroom d'in,su suka ja hankalin Abbah dake aiki kan computer,da sauri ya nufo inda take fuskarsa cike da damuwa yana tambayarta "my dear are u alright?" Ta kad'a masa kai idanuwanta a rufe,a hankali ya zauna next to her sosai kamar za su shige cikin jikin juna saboda son sanin abunda ya tayar mata hankali,ta had'iye saliva's da kyar tana kallonsa sai ta k'irk'ira murmushi tayi saboda ta ta yadda hankalinsa ya tashi,a hankali Abbah yayi ajiyar zuciya yana kallonta hannunsa rik'e da nata yace "What happened?" Tayi jim tana tunanin abunda za ta fad'a,a hankali ta lumshe idanunta tace "mafarki nayi" ya sake yin ajiyar zuciya yace "Ok! Ai kinyi addu'ah,in sha Allah nothing will happen" Annie tace "in sha Allah" daga hakan ta fara sauke k'afafunta,Abbah ya kalleta kad'an yace "Where are u going?" Ta d'aga kai tana kallonsa tace "lokaci ya k'ure ne,and ya kamata ace na fara preparing mana dinner" ya kad'a mata kai a hankali yana dawo da ita kusa da shi yace "kamar ba kya jin dad'in cikin kwanakin nan,ya kamata ki huta yanzun zan fita idan ina dawowa sai na siya mana abunda ya dace" tayi murmushi idanunta akansa but sai bata ce komai ba ta hak'ura bata sake yin maganar girkin ba,Abbah yana gama abunda zai yi ya fara shirin fita kamar yadda yace Annie ta taimaka masa,har bakin mota ta rakasa na nan cikin apartment d'in ya wuce tana d'aga masa hannu har ta daina ganinsa sosai sannan ta koma,tana shigowa direct kitchen ta wuce ta fara preparing musu healthy food as their dinner,ta gama shirya komai kafin lokacin maghreb yayi,brown rice da cabbage stew sai butter lettuce and fresh herbs,sai fruits da ta yanka different styles,duka a gaggauce tayi aikin ta kammala ta fito da komai ta jera a dining,lipton data bari kan gas d'in ta shiga saukewa saboda ya tafasa k'amshin herbs da ta sa duk ya cika parlor'n,da sauri taje ta juye a flask ta ajiye saman cabinet ta kashe gas,ta juya da niyyar d'aukan flask d'in ta fita k'aurin gas da ta shak'a,in time taji zuciyarta ta fara tashi a gurguje ta isa inda flask d'in yake tana rik'e da numfashinta,tana d'aukar flask d'in ta fita a kitchen d'in har tana had'awa da gudu,tana fitowa ta rufe kitchen d'in,sai ta lumshe idanunta a hankali tana sakin ajiyar zuciya,ta bud'e ido da nufin k'arasawa inda dining yake ta fara ganin komai yana juya mata,da sauri ta dakata tana ware idanunta sosai,a jima kad'an ta daina ganin komai duka.

Some hours left ...

     Annie who was lying bayan farkawarta,ba tare da ta bud'e ido ba ta kai hannu ta dafa kanta da take jin yayi mata nauyi tana yamutse fuska,haka ma duk tana jin jikinta yayi mata babu dad'i,a hankali ta furta "Alhamdulillah alaa kulli shaii'iy" rik'e hannunta da taji anyi sai ta fara bud'e ido,Nusrah ta gani zaune kusa da ita quickly tayi yunk'urin tashi ta zauna Nusrah ta dafeta tana mata murmushi,a hankali ta waiwaya tana kalle²n wajen da suke,ganinsu a hospital ta zaro ido tana fad'in "me muke yi a hospital daughter?" Nusrah tayi mata murmushi tace "Muma fa Annie we just come and found u lying on the floor,but not knowing what was happening" Annie tayi shiru kamar tana tunani can ta d'ago ta kalleta tace "me yake damuna to muka zo hospital? Ni lafiya ta k'alau daughter" ta fad'a tana k'ok'arin sauka daga saman gadon,da sauri Nusrah ta rik'e mata hannun da ake mata k'arin ruwa saura kad'an ta cire cannular d'in,cike da mamaki Annie tabi hannun ta da kallo ta d'ago ta kalli Nusrah kafin tayi mata wani tambayar aka turo k'ofar aka shigo,Abbah ne tare da Nuraz kallo d'aya za kayi musu kasan suna cikin farin ciki,Annie ta bisu da kallo but ta kasa fahimtar yanayin su duka,suka kalleta suna yin murmushi,itama ta daure ta mayar musu,Nuraz ya zauna d'aya side d'in nata yana rik'e hannunta ya kwantar da kanta jikin shoulder d'insa,cikin sanyin murya ya furta "Annie ya jikin?" Ta tab'e baki tana kallon hannunta mai k'arin ruwa a jiki tace "Who told u i was sick?" A tare suka kalli juna,Nusrah za tayi magana Nuraz yayi gyaran murya yana nuna mata da ido,sai ta wayance ta d'auke kai kawai,Annie ta bisu da kallo su ukun but sai bata sake tambayar kowa ba cikinsu,har ruwan ya k'are tana zaune tana kallonsu,nurse tazo ta cire mata daga nan Dr Paredes ya shigo,bayan ya sale duba yanayin jikin nata yayi mata y'an tambayoyi sai yayi discharging nasu daga hospital d'in,su Abbah suka yi masa godiya then suka fara shirin barin hospital d'in,lokacin da Dr Paredes yazo fita ya mik'awa Nuraz hannu da fad'in "Allah ya inganta!" Wannan kalmar da Annie taji sai ya tsaya mata a rai but kuma sai ta kasa fahimtar abunda suke nufi,a hakan har suka fito daga Nuffield health suka nufo gida.

      After they came in decideddare ya fara yi sai basu zauna ba suka yi sallama da su Annien suka tafi,ita dai Annie tun da suka baro hospital ganin duk sunk'i fad'a mata abunda yake damunta sai ta koma kamar wata dumb,maganar ta ya koma kad'an² shima sai ya zama dole,tun da su Nusrah suka bar gidan kuma sai duk ta sake yin shiru,idan Abbah yayi magana sai dai ta bashi amsa da "Uhm" ko "um'um" da yaga ba ta son magana sai ya kyale ta a tunaninsa duk jikin ne yasa ba ta son magana sosai,sai bai takurata ba har lokacin bacci yayi,a nan ta fara ganin wani sabon salon kulawa na musamman,motsi idan tayi sosai idanun Abbah suna kanta har ta fara zargin wani abu but she decided not to ask him again.
Chapter 131 · 0% Book details