← Book details Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 118 OF 152

Sashe 118

Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Throughout the journey Nuraz was unable to speak,but lokaci zuwa lokaci yana juyawa ya kalli iyayen nasa da suma maganarsu bata wuce kalmomi,after 6 hours 45 minutes their flight landed in Kano,followed by suka yi waya da Annie da yake ta san da maganar zuwansu k'asar,and lokacin already 11:45pm ta yi,saboda haka daga nan suka wuce k'ofar Na'isa,while tafiyarsu suka barshi zuwa wayewar gari,da safe misalin k'arfe 10am bayan sun shirya jirgin Aazman airline suka bi zuwa Gombe,within 30 minutes flight d'in da suka hau yayi arriving sani abacha international airport,bayan saukarsu sun yi waya da Abbah a lokacin sha d'aya saura mintuna,he sent a car da za ta d'auko su zuwa hospital d'in,suna shigowa cikin hospital d'in Abbah himself ya fito ya tare su,suka shiga ward d'in da Nusran take a lokacin tana bacci,kasancewar Abbah ne kawai a tare da ita Deeje ta je gida ta dawo,as she was spending the night here da safen yace taje gida ta samu bacci,Malam kuma sai after asar prayer yace zai zo saboda bak'in da yayi but sun yi waya da Abbah ya tambayi jikin nata,suna shigowa babu kunya Nuraz ya wuce wajen da take kwance yana kallon yanayin jikin nata,Annie ta bishi da kallo tana mamakin halayensa,bayan sun gaisa da Abbah sun tambayi mai jiki,a nan ya sake yi musu bayanin yadda al'amarin ya faru,sympathetically duka suke kallonta,basu jima ba sosai mazan suka fita aka bar su Annie,bayan kusan awanni biyu lokacin Nuraz ya kasa hak'uri ya dawo cikin hospital,wanda har lokacin tun bayan gaisawa da suka yi da Abbah he did not say anything to anyone until suka je suka samawa kansu masauki,yana zaune gefen bed d'in da take ta fara motsawa,ya zuba mata ido burin sa duka a time d'in bai wuce ta farka yaga yanayin jikin ba idan babu ci gaba sai su canja hospital,akansa idanunta suka fara sauka,cikin mamakin ganinsa tayi blinking idanunta a tunaninta ko gizo yake mata,yayi ajiyar zuciya yana sauke numfashi a hankali,slowly ya kama hannunta ya rik'e yana muryarsa a low tone yace "Hello Roohii!" Ta sake kyafta ido bata ce komai ba,yace "how are u feeling?" Hannunta ta fara k'ok'arin cirewa daga nasa tana son tashi,yace "Na taimaka miki?" Ta girgiza kai alamun a'a,ahankali ta sauke k'afafunta ta tashi,duka suna kallonta suna jera mata sannu,ta k'irk'ira murmushi but she couldn't speak saboda bakinta was full of saliva's,ta wuce toilet a hankali bayan ta shiga ta wanke bakinta ta d'aura alwala ta dawo,jikin Annie taje ta shige,Annie tayi murmushi tace "Hello baby!" Tayi murmushi and suddenly asked "Annie when did u come?" Tace "Not too long ago" tace "But u didn't wake me up?" Tayi mata murmushi tana shafa kanta tace "ba ki da lafiya daughter,ba zan so wani abu ya same ki ba" a hankali ta lumshe ido ta bud'e tace "ban san za ku zo ba,da ba zan yi bacci ba" as she spoke slowly words d'in suna fita one after the other ya isa tabbatarwa ta sha wahala,Lolly tace "Baby tashi maza ki ci abinci" ta kad'a kai tace "I'm not hungry Aunty" tace "A'a fa daughter na san ki bakya son cin abinci" tayi murmushi tana lumshe idanunta kamar za ta sake komawa baccin,hankalin Nuraz duka yana kanta yana kula da yadda take yi,yaji bai amince suyi ta zama a nan ba,gara kawai su koma Kano ko su wuce UK mai gaba d'aya,as he wakes up zai fita yace "Annie zan je na dawo yanzu" ta kalleshi tace "what happened?" Ya kad'a kai yace "ina tunanin za mu karb'i sallama zuwa gobe mu koma Kano" Annie ta girgiza kai tace "Ok" yana fitowa ya tarar da su Abbah suna hira,ya k'arasa inda suke cikin girmamawa yace "Abbah! I would like to see the doctor" Rafeek yayi murmushi because ya fahimci abunda yake nufi,Abbah yace "Hope ba wata matsala kake son ganinsa?" Ya lumshe idonsa a hankali yace "No! I just think ya kamata mu canja hospital ne,gara mu koma Kano ko mu tafi UK" Abbah ya jinjina kai yace "No problem",tare suka je office d'in Dr Adam suka yi masa bayanin abunda suke buk'ata,yace babu matsala zuwa goben idan Allah ya amince zai discharging nasu,they thanked him and came out daga office d'in,sai ga driver ya kawo Malam,respectfully suka gaisa da Nuraz da mahaifinsa,here Abbah ya yiwa Malam bayanin da ya san zai gane game da Rafeek da Nuraz as his friend and his son-in-law kuma d'an amininsa,Malam greatly appreciated them,a nan yayi musu nasiha sosai,bayan ya duba jikin Nusrah bai zauna ba ganin da mutane ya koma gida because ya bar wasu bak'in a lokacin suna jiransa.

Ranar gaba d'aya they stayed here at the hospital until 9:00pm sannan suka tafi,while Annie stayed by her side because she refused to let anyone stay with her and tak'i bari su tafi duka,yadda Abbah ya ga suna tafiyar da al'amuransu cikin wuni d'aya har mamakin shak'uwa da soyayyar dake tsakanin su yake yi,,,they were discharged from the hospital at about 8:00am,kai tsaye sai da suka fara zuwa gida,bayan Nusrah ta sake hutawa da yamma da suka ga jikin nata Alhamdulillah yayi sauk'i sosai unlike yesterday suka yi sallama suka bi flight zuwa Kano tare da Abba'nta,da yake motar da suka zo da ita dama ya siyeta ne saboda Malam (ya kai chin hanci😉) so a nan suka barta,lokacin da suka sauka a Kano K'ofar Na'isa suka wuce,a tak'aice basu bar kano ba a ranar,cikin kwanaki biyu da dawowarsu kusan kullum Rafeek suna tare da Abbah har dare,here in Kano aka sake kaita AKTH suka ga wani consultant Dr,da ya tabbatar komai lafiya ya basu shawarwari on how to keep it in the future if such problem arises.

Kwanan su uku a kano,ranar ana gobe za su bar k'asar Abbah suna hira da Rafeek a parlor'n gidansu da ya mayar na saukar sa duk lokacin da ya zo,kasancewar su a can suka sauka,Nusrah kuma still tana wajen Annie ko da suka zo Kano,Rafeek ya damu da shirun Abbah akan maganarsu ya kalleshi sosai ya kad'a kai ba tare da ya ce komai ba,Abbah dake kula da abunda Rafeek yake yi yace "Friend ya aka yi ne na ga kana min wani kallo?" Rafeek sighed before he finally adjusted yace "No kada ka damu,but gaskiya ina da wata y'ar tantama" Abbah ya k'ura masa ido yace "Akan me?" Rafeek yace "on u!" dariya Abbah yayi yace "Uhn! Well i'm listening to u" Rafeek ya yi ajiyar zuciya kafin ya watsowa Abbah tambayar "Anya friend kana da lafiya?" Cikin rashin fahimtar inda kalamansa suka nufa yace "Ban fahimta ba" Rafeek yace "Za ka fahimta,but ina so ka fad'amin,kana da lafiya ko mu fara nemar maka magani?" Dariya Abba yayi yace "ka ganni a kwance ina jinya?" Rafeek yace "ina tunanin wannan rashin lafiyar ya wuce haka" Abbah yace "really?" Rafeek ya kad'a masa kai yace "Fisabilillahi za kace min baka gano hakan ba?" Abbah yayi murmushi yana kallon Rafeek da yayi kichin² yace "Idan har maganar da kake min ne,ina farin cikin sanar da kai na amince da duk wacce ka ga ta dace da ni,but a nawa ra'ayin ina son macen da za ta so yarinyata,bayan wannan ba ni da wani sharad'i,to know that amincewar da nayi da kai shi ne yasa na bar zab'i na a hannunka" cikin tsananin murna Rafeek yace "Do u really agreed friend?" Abbah yace "absolutely sure" Rafeek ya rik'e hannunsa sosai zuciyarsa taf farin ciki yace "Toh batun Malam fa? Kun yi magana?" jim Abbah yayi kamar mai tunanin wani abu,a hankali ya sauke numfashi yana kallon Rafeek yace "na so na yi masa maganar,sai wannan incidence d'in ya faru,but zan yi masa waya in Allah ya amince na sanar da shi,ya taya mu addu'ah Allah ya zab'a mana mafi alkhairi" Rafeek ya amsa yana jin wani irin nutsuwa yana saukar masa,they chatted for a long time and then Abbah yayi masa sallama,Rafeek yayi masa rakiya har bakin mota,bayan ya shiga mota ya zauna kafin driver ya ja motar Rafeek yace "Friend,u allow me to choose a partner for u,but har yanzu ban ji ka tambayi wace ce ba?" Abbah yayi dariya yana kallon Rafeek yace "ko wace ce a yanzun ba shi ne abunda yake damu na ba,what i need most is to know her character,yanayin mu'amalarta da mutane,tana da addini ko babu?" Rafeek yace "Duka wad'annan ta had'a su,including the one u didn't mention,but in Allah ya amince goben i'll let u know who she is!" Abbah yayi murmushi yace "Allah ya kaimu" suka yi sallama driver yaja mota suka tafi.

Lokacin da Rafeek ya dawo daga raka shi ya tarar da Lolly ita da Bareerah suna fira,yana shigowa Bareerah ta tashi ta yiwa Lolly sallama ta tafi gida,bayan fitarta Lolly ta wuce bedroom here ta same shi yana magana a waya,but kafin ta k'arasa zama sai ya katse kiran yana cewa za suyi magana later,fuskarta a sake tace "Yallab'ai ka korar min mai taya ni hira" yana yi mata murmushi yace "A'a ba ni na koreta ba,ta dai ganni ta tafi" tace "shigowarka ai shi ne dalilin tafiyar ta" yace "Na amince da abunda kika fad'a" he kept quiet and looked back yace "Ina Noor ya shiga? Yau gaba d'aya ba na tunanin na ganshi tun safe" tashi tayi tace "Uhn! Maybe ka fini sanin inda ya shiga,ni da nake nan cikin gida ina zan san inda ya shiga?" Yayi jim a hankali kuma ya sake cewa "ya kamata gobe ku shirya da wuri ba na son tafiyar tsakiyar dare" ta amsa tana cewa "in Allah ya amince ba za mu yi latti ba" yace "Allah yasa".
Chapter 118 · 0% Book details