← Book details Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 152

Sashe 7

Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

     Lokacin da baba ya fara harkar bin y'an siyasa,sai ya zama babu ruwansa da wani binciken muna zuwa ko bama zuwa duk da a bayama ba damuwarsa kenan ba,shi dai yasan duk k'arshen term zai biya school fees na gaba d'ayan mu,wad'anda suke zuwa da wad'anda basa zuwa,damuwarsa shi ne a tattara masa shaidar biya na gaba d'ayan mu a bashi,shin mutumin da aka bawa shaida kamar haka ta yaya ne ma zai san wanda bai je ba.?
   Life goes on,,bayan tsayin shekaru da muka shafe still rayuwar gidanmu yana a yadda yake babu wani sauyi,kullum abu biyu ke yawo a tsakani dad'i/kishiyarsa da rashin watar zaman lafiya,,cikin hukuncin ubangiji a dai² lokacin dana kammala secondary school Allah ya kawo min mijin aure daga cikin y'ay'an abokan Baba,,tunda aka tsayar da ranar aurena nake cikin damuwar barin gida,a zahiri kuma ba wai ina damuwa bane saboda zan tafi,sai dan a wannan lokacin duka damuwata ita ce Hauwa,tunani na a kullum yadda zan tafi na barta,saboda ban san yaya rayuwarta zata kasance ba bayan bana gida,na san matar babanmu bata kula da kowa a baya ba da yake cikin gidan bare yanzun nayi tunanin za'a fara,tak'amarta kuma shi ne bata haifa ba,babu wanda zata raina sannan baba ya nuna fifikon soyayyar mu akanta,shi yasa tunda ta shigo gidan bata tab'a cewa muyi wannan mai kyau ne,ko mu bar wannan bashi da kyau,tunda aka tsaida ranar aurena hankalina ya kasa kwanciya,,but a wannan lokacin Hauwa tayi abunda ni ya kamata ace nayi,kasancewarta mai k'ananun shekaru a kaina,kamata yayi ace ni zan kwantar mata da hankali,amma abun mamakin shi ne ita da ake ganin bata da cikakken hankali ita take kwantarmin da hankalina,a duk lokacin da zata ganni cikin damuwa takanyi k'ok'arin taga ta sanya murmushi akan fuskata,har Allah ya kawo lokacin aurena,aka yi biki lafiya aka kai ni d'akina,a daren daya zama daren farko na rabuwarmu da Hauwa,ya kasance ni ina kukan rabuwa da ita a karon farko tun bayan tasowar mu,itama tana kukan shiga sabuwar rayuwar da babu ni a cikinta,a hakan ina kallo y'an gidanmu suka wuce suka barni,naji babu dad'i sosai duk da ba zaman lafiya muke yi ba,amma ganinsu kad'ai a tare da ni nasan zai bani kwanciyar hankali,,tsakanin gidan mu da gidan da nake aure babu nisa,but mu a gare mu a wannan lokaci gani muke kamar an gama nisanta mu da juna,bayan y'an rakiyar amarya sun watse ango ya shigo d'akin amarya.."
   Shiru Annie tayi tana sauke numfashi da kallon Nuraz sannan taci gaba
    "A bisa tsarin addini komai angona yayi min,na tabbata mijina na sona haka nima ina sonsa,kasancewar mutum ne shi daya dace da burin kowace y'a mace,,bayan komai ya lafa,duk wata hidima an k'are,aurenmu ya samu wasu kwanaki haka nan sai nayi nufin tuntub'ar babanmu akan maganar ko zai bari Hauwa ta dawo gurina dan a yadda na kula da ita cikin lokacin tana cikin damuwa da takurawar y'an gidanmu,amma kuma idan na tambaye ta duk lokacin da ta zo gurina bata iya sanar dani sai dai tace min komai lafiya,ni dai haka nan duk lokacin da zata fad'amin haka nakan ji ban gamsu ba,shi yasa lokaci guda nayi nufin samun babanmu da batun,mijina ya bani goyon bayan na karb'o ta ta dawo hannuna,cike da wannan k'arfin guiwa da sa hannunsa muka je tare har gaban Baba da maganar,duk da a d'ar² muke bcos bamu sani ba zai amince ya bamu ita ko bazai amince mana ba mu dai gamu nan a probability....

#Share.
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©®2020.*

*'DAN MACE..*
(Tʜᴇ ᴘꜱʏᴄʜɪᴀᴛʀɪꜱᴛ)..💥

*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
https://my.w.tt/29u2S26SG2

Pᴀɢᴇ 4.
#Sᴏᴜʀᴄᴇ
Chapter 7 · 0% Book details