← Book details Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 152

Sashe 16

Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Misalin karfe 3 da y'an mintuna na dare Hajiya tana tsaye saman abun sallah tana kai kukanta ga Ubangiji akan al'amuransu ta farka,idanunta suka fara motsawa a hankali kafin ta fara k'ok'arin bud'e su da kyar,yadda jikinta yake a d'aure bata fasa juya kanta tana kalle² ba,kud da babu yalwataccen haske yanayin k'amshin da d'akin ke fitarwa ya bata tabbacin ba a gida suke ba,tunanin abunda ya kawo su nan d'in ta fara,bayan ta gama y'an tunanukanta bata gano komai ba ta tab'e baki a hankali tana k'ok'arin tashi ta zauna,zafin da taji a gefen cikinta yasa ta sakin marayan ihu da ya kaiwa Hajiya sak'on ta farka,,muryarta dishi² take magana tana kira taji ko akwai mutum kusa da ita ya taimaka mata,Hajiya dake zaman tahiya da sauri ta k'arasa ta sallame sallah,ko addu'ah bata jira tayi ba ta taso da sauri tayi gurinta tana fad'in
"Alhamdulillah.! Hauwa'u kin farka.!? Sannu kinji Allah yayi miki albarka,ya kara muku lafiya.!" Juya kanta tayi tana kallon shade d'in Hajiya dake tsaye kusa da ita tace
"Hajiya zanje toilet.."
Da sauri Hajiya ta amsa mata,ta taimaka mata suka je tayi fitsari ta wanke bakinta suka dawo,saman gadon ta sake zama bayanta jingine jikin pillow Hajiya ta fita ta dawo da nurse ta dubata ta fita,sannan ta had'a mata tea ta bata,tana gama sha muryarta har lokacin bata fita sosai tace
"Hajiya me muke yi a hospital.!? Mene ne ya same ni a ciki na naga anyi min d'inki.!?"
Hajiya tace "haihuwa kika yi,amma aiki suka yi miki." Idonta ta d'an bud'e sosai ba kamar da farko ba data tashi da suke a shanye tana kalle² a d'akin,ganin babu jaririnta da aka ce an ciro mata a hankali ta sauke idanunta hawaye suna gangarowa cikin muryar kuka tace
"Hajiya ya mutu ko.!?" Ido Hajiya ta zaro tana kallonta tace "waye ya fad'a miki haka.!?" Tace "Hajiya ai to ban ganshi ba.!"
D'an murmushi Hajiya tayi tana dafa hannunta tace "kada ki damu daughter yaron ki yana nan a raye,an sashi dai a na'ura ne saboda yazo da rashin kuzari,an jima kad'an idan Allah ya kaimu zaki je kiga abunki kinji.!? Ki kwantar da hankali."
Sai lokacin taji wani irin nutsuwa ya saukar mata duk da nauyin da har lokacin take ji a k'irjinta a hankali ta zame jikinta ta amsa ta koma ta kwanta,bayan an fito a masjeed Hajiya ta kira wata nurse d'in ta sake zuwa ta duba jikin nata kafin Dr yazo,da safe Dr Fahad ya shigo duba jikin cos tun tun kafin ya k'araso hospital aka sanar da shi ta farka,yana zuwa ko zama baiyi ba a office ya shiga duba jikin,komai nata yana lafiya sai ciwon da ba'a rasa ba,hajiya ta tambaye shi ko za'a iya bata abinci kuma cos tunda ta farka tea kad'ai ne a cikinta,Dr Fahad yace "Ehh!" Za'a iya bata but ya zama mai ruwa²,sai kuma fruits da za'a k'ara mata da su,saboda wajen yin bayan gida kada ta wahala su samu matsala a aikin nata,godiya Hajiya tayi masa sosai,Dr Fahad ya fita ya barsu tana lallab'a ta,,y'an gidanmu duk da bama zaman dad'i sun je duba Hauwa da yake tana cikin halin jinya sai bata sani ba,ni kuwa tunda aka yi mata aikin naso na zauna nayi jinyarta saboda duk duniya nice tata da ya kamata na zauna da ita bayan mahaifiyar mu,itan bata raye sai ni,ni d'in kuma dana nuna zan zauna da ita Hajiya tace kada na damu naje na kula da gida na ita zata zauna da Hauwa har zuwa lokacin da za'a basu sallama,a zahirin gaskiya mahaifan Rafeek mutanen kirki ne,sun yiwa Hauwa rik'on amana,ko dai ace su suka kawota duniya iya gatan da zasu bata kenan,bare ba su suka haifeta ba matsayin suruka kawai take a gurinsu,ranar da Hauwa ta farka ranar ne farkon da kaji d'umin mahaifiyar da tayi silar zuwanka duniya,lokacin shayar sa kai yayi ta tafi ganinka,yanayin d'akin da kake ciki da yadda yake fitar da hucin zafi saboda yawan na'urori yasa Hauwa ta shiga damuwa,bayan duk damuwar da ta shigo da shi the resemblance of Rafeek in ur face as if it were being torn apart ya sake jefa zuciyarta a damuwa a lokacin da aka ciroka daga incubator aka mik'a mata kai,zuciyarta a raunane take ta kallonka,tunda ta farka take tunanin dalilin da yasa take jin ciwuka sa yawa a ranan but bata iya gano dalilin zamanta a hospital ba,amma lokacin data d'auke ka a karo na farko da niyyar ta shayar da kai yadda al'amarin ya faru ya dawo mata kamar a lokacin ne komai yake occurring,ta daure ta shayar da kai tana kallonka cike da soyayya mai tattare da tausayi take zubar da hawaye,har ta gama shayar da kai bata iya tashi ta fita ba,kana jikinta kana bacci yayin da ita kuma tana ci gaba da kuka tuna yadda komai ya faru,kula da nurse d'in dake d'akin tayi da halin da take ciki yana neman sawa ka fad'o daga jikinta tayi saurin karb'e ka daga hannunta ta mayar cikin na'ura,bin nurse d'in tayi da ido,idanunta suka sauka kan takardar dake jikin na'urar mai d'auke da sunan *RAFEEK Son* a hankali ta kai hannu ta ciro hawaye na ci gaba da zuba a idonta,nurse d'in ta bita da kallon tausayi tana tambayarta ko lafiya,da kyar Hauwa tayi shiru tana kallon rutun har lokacin tace
"Dan Allah y'ar uwa zaki iya min wani taimako.!?"
Tace "fad'i kada ki damu in sha Allah idan ina da yadda zanyi na taimaka miki zanyi"
Godiya Hauwa tayi mata tace "sunan nan nake so ki canja min"
Nurse d'in tace "Ohh! An sawa baby'n suna.!?"
Hauwa tace "Ehh! Ansa masa" murmushi nurse d'in tayi tace "Masha Allah,mene ne sunan.!?" Ba tare da Hauwa tayi shawara da kowa ba tace *"NURAAZ.!"*

"Wow.! But dan Allah zan iya tambayar ki.!?" Nurse d'in ta fad'a tana kallon Hauwa da kanta ke k'asa tace "fad'i tambayarki",tace" Ma'anar sunan nan da kika fad'a dan Allah zaki fad'a min,na ji sunan yamin dad'i sosai",bata d'ago ba tace "Treasure of noor",tace "gaskiya na gode,but nace ba.. Za ki iya min kyautar baby'n ina sonsa sosai",murmushin k'arfin hali tayi ta d'ago kanta dake k'asa tace
"Wannan shi ne farin cikina,amma tunda kina sonsa na baki"
Murmushi nurse d'in tayi cikin jin dad'i tace "Kai amma gaskiya na gode sosai,kyautar baby sukutum,Allah dai ya k'ara muku lafiya Maman baby"
Hauwa tace "amin'',tana zaune nurse d'in tana mata hira tunda ta kula tana cikin damuwa,har ta rubuta sunan tace mata "kinga sunan yayi.!?"
Da kyar Hauwa ta sake d'aga kai ta kalli takardar,ganin *NURAZ RAFEEK* a jiki bar'o² wasu hawayen suka sake taho mata,da sauri ta girgiza kai tace "A'a" kasa fahimtar abunda take nufi nurse d'in tayi har ta matso kusa da ita tace "bai yiba kenan sunan.!?" Ta gyad'a mata kai "me za'a rubuta to.!?" Sai data share hawayenta tana sake kallon yaronta dake kwance cikin incubator jikinsa duk anyi connecting na'urori yana bacci tace
*"NURAZ BIN HAUWA."*

*#Posting abun so ga reader's,#Comments abincin writer's,mu daku kamar k'waryar sama dana k'asa ne,idan akwai d'aya babu d'aya al'amarin baya tafiya dai²,it's better ace mun faranta ran wad'anda suke k'aunar mu fisabilillah.!*

#Share.
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©®2020.*

*'DAN MACE..*
(Tʜᴇ ᴘꜱʏᴄʜɪᴀᴛʀɪꜱᴛ)..💥

*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
https://my.w.tt/29u2S26SG2

Pᴀɢᴇ 8.
#Hᴜᴍɪʟɪᴀᴛɪɴɢ
Chapter 16 · 0% Book details