← Book details Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 152

Sashe 56

Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

    Once again yayi wani irin mugun had'e rai ya juya yana tafiya hanyar bedroom d'insa ya d'an dakata a fili ya furta "nasa ciwon ai da sauk'i,those he humiliated shekaru 28 suka shafe without knowing the word of happiness,they only hear about it amma a kansu basu san shi ba,yaya yake yana da nau'ika ko babu.?? But Alhamdulillah they always grateful.." Annie reached where he was standing dai² door d'in shi,hannunsa ta rik'o bata yi magana ba except to aim to get him to where Rafeek was lying and there was no sign of breathing sai dai ya kafe a gurin ko kad'an yak'i yin gaba bare ta iya motsa shi,ta d'aga idonta da suka fara sauyawa tace "Kaje ka d'aga sa idan har na isa na fad'a kaji." Ya girgiza mata kai yace "Ki kyaleshi kawai Annie" ta girgiza masa kai tace "He's ur dad,would u like to miss him.!? No matter how bad he is kai ba za ka tab'a iya sawa ya zama na gari ba,and he never did anything except what Allah (S.W.T) has written mahaifi ko yaya yake y'ay'ansa basa kyamar sa,abun daya faru a baya k'addarar mu ce mu bamu isa mu kauce mata ba,mu godewa Allah duk abunda ya same mu Allah has given us the solution,,mun samu ci gaban da ba kowa ya same sa ba,ur father is ur father,u or him are not enough to change Allah's destiny,shin ka manta duk wannan ci gaban waye ne yayi nufin ku same shi!?" Yace "Allah (S.W.T) yayi nufin mu da shi" ta girgiza kai tace "haka ne but ko wane ci gaba ko alkhairi da yake samun bawa akwai silah,shin za ka iya fad'a min waye silar samuwar ci gaban mu.!? Ko kuma are we the ones who fight to have it.!?" Yayi shiru yana kallonta,tayi ajiyar zuciya tace "Ur father is the master and he is ur genius,idan ace ubangiji bai yi nufin mu da samun ci gaba ba,how do u think ur father will be to u,why did he not forsaken u.? Don't forget habibiiy at this time he has the right yasa a wulak'anta mu but he finally gives u home and a capital so that one day do not both of u to beg for a food or shelter" jikinsa ne ya d'an fara sanyi amma kuma duk da haka yak'i matsawa daga gurin,duk wasu kalamai da Annie ta san za su taimaka ya sakko ta fad'e su amma juyin duniya suka yi da shi ko tari yak'i ya sake yi sai dai yanayinsa kana kallo zaka san kalamanta sun shigesa,Annie ta gaji da zuba masa ido tace "Shi kenan habibiiy tunda kun d'auke ni marar amfani,surely i need to get back to where i came from" hankalinsa a tashe yayi saurin rungumeta yana bata hak'uri jikinsa har rawa yake yace "please Annie don't say that.. If there are any people in the world who are desperate to be with u Annie kin san sai dai su biyo baya,Annie please i beg u with the greatness of God I'm so sorry and don't say u will leave us please.." tace "u don't care about me habibiiy ni ce dai na damu da damuwarku" yayi saurin girgiza kai idanunsa sun sauya launi yace "Wollahi Annie mun damu dake" she smiles and began to wiped the tears that cames down tace "Because of ur love i have chosen to leave home,saboda soyayyar ku i choose both of u to rejoice over me,saboda wannan soyayar nake tare da ku for 28 years without marriage and not because if i find a husband i will not stay with him,amma saboda kada ku wulak'anta na hak'ura da komai na zauna,i will have no regrets today when something has happened to me,everything i have na sadaukar da shi saboda farin cikin ku,,but today what are u trying to do for.!?" Ya girgiza kai muryarsa na rawa yace "Annie please.!" Yana magana yana goge mata hawaye "Do i deserve this from u.!?" Ya ci gaba da girgiza kai "Annie please.! Please don't say that,whatever u said we would do just bcos of u,ko da hakan yana nufin yankewa." ta sake yin murmushi mai ciwo "I wish ina da wannan alfarmar da na fi kowa farin ciki" ya katse ta da sauri yace "U have it Annie" tana kallonsa tana girgiza kai tace "Ba ni da shi habibiiy" yace "Kina da sama da shi Annie" ta had'iye saliva's tace "Idan har ina da shi,and na kai matsayin da zan iya samunsa a gurinka ina son kaje ka kama mahaifinka" ya kalleta a tsorace yace "Annie is this really what u want.!?" Ta gyad'a masa kai tana lumshe ido tace "Idan har ina da alfarmar da kace habibiiy,wannan shi kad'ai nake buk'ata a gurinka" yayi ajiyar zuciya mai nauyi a hankali ya girgiza kai yace "An gama Annie" yana fad'a ya nufi inda Rafeek ke kwance,su hajiya suka bisu da kallon mamaki,shi kad'ai ba tare da taimakon kowa ba ya d'auke shi yayi hanyar fita,a gurguje Maimunatu ta dakatar da shi tace "Da ka dawo da shi his doctor is on the way",ya tsaya sororo rik'e da shi,ta girgiza masa kai a hankali,he slowly turned towards his bedroom with Annie standing by the side of the room yana zuwa ta bud'e masa door d'in ya shige,Hajiya tana ganin haka ta koma saman armchair ta zauna ragwaf cikin damuwa tana godiya ga Allah da sauke ajiyar zuciya,,ya kwantar da shi ya juyo yana kallon Annie dake tsaye fuskarta da damuwa yayi kamar zai fita daga d'akin Annie tace "Where are u going.!? Dont leave him alone habibiiy ko ka manta wannan shi ne muradinka.!?" Yayi shiru ya fasa fita but jikinsa duk yayi sanyi saboda maganganun Annie sun ruguza masa shiri,Dr Stevens ya k'araso Maimunatu ta fita ta shigo da shi,since he came in ya kalle shi ya girgiza kai saboda yadda ya gansa ya san dole da matsala ya dudduba sa a gaggauce,ya d'ago yana goge gumi yace "We need to go to the hospital." hankalin Hajiya ya sake tashi saboda tsayin lokaci da yake tare da ciwon he just checked him at home and provided him whatever he needed amma batun zuwa hospital kam ya manta when last hakan ya faru.
     Nuraz ya kalli Dr Stevens zai yi magana ya dakatar da shi da fad'in "due to his condition we need to rush to the hospital because he is at the final stage." Jin abunda ya fad'a yasa bai iya tsayawa yin magana ba ya juya da sauri ya d'auke shi a gaggauce suka fita daga gidan,Clark da driver'nsa suna ganin fitowarsu suka fito a gaggauce daga mota,but bai tsaya jiran su taimaka masa ba ya wuce yana niyyar sa shi a mota ambulance ta k'araso,kafin su Hajiya su fito har an sashi a mota sun wuce hospital,St Barnabas Clinic dake nan arean Albert street suka nufa a gaggauce suna zuwa aka shiga shi Nuraz da su Clark suka tsaya nan reception,lokacin da Hajiya suka k'araso idanunta sun kumbura sunyi ja,danma Annie tayi ta basu hak'uri ita da Maimunatu,Hajiya cikin jimami tace "Ni kam ban san wane irin k'addara ne wannan ba,ace daga wannan sai wannan,tunda yaron nan ya bijirewa maganar nan shi kenan rayuwarsa take cikin wani hali,in har dan saboda abunda ya aikata ne a baya ya ubangiji ka kawo masa sauk'i cikin lamuransa,na yafe masa wollahi har abada.." Annie tace "In sha Allah Hajiya komai zai zo da sauki ki daina fad'an haka,ki ci gaba da yi masa addu'ah." Hajiya ta girgiza kai tace "Kullum cikin yi masa addu'ah nake,in sha Allah ubangiji ba zai tab'ar da shi ba.." Annie tace "In sha Allah.."
Chapter 56 · 0% Book details